An Biya wa Mahaifin Yaran da Aka Yi wa Kisan Gilla Kujerar Makkah, Ya Samu Kyauta

An Biya wa Mahaifin Yaran da Aka Yi wa Kisan Gilla Kujerar Makkah, Ya Samu Kyauta

  • Ana ci gaba da taya Malam Haruna Bashir jimami bayan iftila’in hallaka iyalinsa a Kano, lamarin da ya jawo tallafi daga jama’a
  • Fitaccen lauya Abba Hikima ya tabbatar wata Hajiya ta biya masa kujerar Hajji tare da N200,000 domin biza
  • Abba Hikima ya ce ana ci gaba da karɓar gudunmawa, inda aka riga aka tara makudan kudi domin nuna masa kauna

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Malam Haruna Bashir na ci gaba da jimami bayan iftila'in da ya faru na hallaka iyalinsa da aka yi a jihar Kano.

Mutane da dama sun tausaya wa bawan Allah saboda irin bala'in da ke cikin rasa iyali baki daya wanda ya sa aka fara taimaka masa.

An biya wa Bashir Haruna kujerar Makkah
Malam Haruna Bashir da iyalansa kafin hallaka su a Kano. Hoto: Abba Hikima.
Source: Facebook

Fitaccen lauya a Kano, Abba Hikima ya tabbatar a shafinsa na Facebook cewa wata Hajiya ta biya wa Malam Bashir Kujerar Makkah.

Kara karanta wannan

'Wanda aka kashe matarsa da 'ya'yansa 6 a Kano na bukatar taimako'

Kisan gillar: Al'umma sun fara tara kudi

Hakan ya biyo bayan kira da al’umma suka fara yi da a hada kai domin taimakawa Malam Haruna Bashir da aka kashe 'ya'yansa shida da matarsa a Kano.

Barista Abba Hikima ya bayyana jerin abubuwan da ya ce ya kamata a masa da nufin saukaka radadin da mutumin ke ciki tare da farfado da rayuwarsa.

Masu ruwa da tsaki sun bukaci gwamnati, attajirai da ’yan jarida su nuna tausayi a mu’amalarsu da wanda abin ya shafa lura da halin da yake ciki.

Malam Haruna Bashir da iyalinsa kafin hallaka su
Iyali da aka yi wa kisan gilla a Kano. Hoto: Kwankwasiyya Trustworthy NG.
Source: Facebook

Kyautar da aka ba mijin Fatima a Kano

Abba Hikima ya bayyana matar mai suna Hajiya Bilkisu Suleiman Fema da aka fi sani da Zinariyar Arewa da wannan abin alheri.

Ya bayyana cewa Hajiyar ta yi masa alkawarin guzuri bayan ba ta gudunmawar N200,000 domin a yi masa biza zuwa Saudiyya.

A rubutunsa ya ce:

"Hajiya Bilkisu Suleiman Fema wadda aka fi sani da Zinariyar Arewa, ta biya wa Malam Haruna Bashir kujerar aikin Hajji.

Kara karanta wannan

Abba, Barau da hukumomi 2 da suka yi alkawarin nema wa Fatima da yaranta 6 adalci

"Ta aika min da N200,000 ayi masa rakardu domin samun damar fita kuma ta yi alkawarin bashi guzuri.
"Allah ya saka mata da mafificin alheri, Ameen, wannan abu yayi matukar maranta min wlh."

Bayan haka, Abba Hikima ya jaddada cewa har yanzu ana ci gaba da karabr gudunmawar da ake yi masa.

Ana tara kudi ne domin nuna masa ana tare da shi wanda lauyan ya ce tuni aka samu makudan kudi da jama'a ke tallafawa.

Ya ce:

"Har yanzu dai muna ci gaba da tattara masa gudunmowar ku domin nuna masa al’ummar Annabi SAW na tare da shi a wannan yanayi."

Gwamnati ta shiga shari'ar kisan iyali a Kano

Mun ba ku labarin cewa Gwamnatin Kano ta tabbatar da cewa za ta jagoranci shigar da ƙara kan kisan matar aure da ƴaƴanta shida a Dorayi Chiranchi.

Hakan ya biyo bayan kisan Fatima Abubakar, aka kashe ta da yaranta gudan shida a ranar 17 ga watan Janairu, 2026 da bata gari suka yi.

Kafin wannan lokaci, gwamnatin Kano ta bayyana cewa za ta yi tsayin daka har an tabbatar da adalci a kan kisan Fatima da yaranta bakwai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.