Obasanjo Ya Bayyana Abin da ba Zai Daina ba a Rayuwarsa
- Tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo, ya yi magana kan muhimmancin da yara suke da shi a cikin al'umma
- Olusegun Obansajo ya bayyana cewa duk al'ummar da ke som ci gaba, dole ta kula da walwala da kare rayukan yara
- Tsohon sojan mai shekara 88 ya kuma bayyana cewa duk da da yaran da ya haifa sun manyanta, ba zai taba daina haihuwa ba
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Abeokuta, jihar Ogun - Tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo, ya yi magana kan haihuwa.
Olusegun Obansanjo wanda ya mulki Najeriya a mulkin soja da farar hula ya bayyana cewa “ba zai taɓa daina haihuwa ba.”

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta ce Olusegun Obasanjo ya faɗi hakan ne yayin da yake karɓar bakuncin shugabannin kungiyar likitocin yara ta Najeriya (Pae PAN), ƙarƙashin jagorancin shugabanta, Dakta Ekanem Ekure, a gidansa da ke Abeokuta, jihar Ogun.

Kara karanta wannan
Kisan Fatima: Sheikh Daurawa ya yi magana mai ratsa zuciya kan ta'addancin da aka yi a Kano
Olusegun Obasanjo ya yi magana kan haihuwa
Da yake bayani kan wannan furuci, tsohon shugaban ƙasar ya ce ko da yake shi da kansa ba ya kara haihuwar yara kuma ’ya’yansa sun manyanta, rayuwa na ci gaba ta hanyar jikokinsa da al’ummomi masu zuwa nan gaba.
Obasanjo ya jaddada cewa ci gaban zuri’a daga karni zuwa karni na nuna cewa kare rayuka da jin daɗin yara nauyi ne na kowa, kuma nauyi ne da ba ya karewa.
“Ni a karan kai na ba na haihuwar yara, kuma ’ya’yana sun manyanta. Amma ’ya’yana suna haihuwar yara, jikokina ma suna haihuwar yara, don haka ba zan taɓa daina haihuwa ba."
“Domin idan na daina, ’ya’yana ba za su daina ba, idan su ma suka daina, jikokina ba za su daina ba, kuma haka rayuwa ke ci gaba."
- Olusegun Obasanjo
Obasanjo ya fadi muhimmanci yara
Ya bayyana yara a matsayin ginshiƙin kowace al’umma, tare da kira da a kara himma wajen kula da su, tabbatar da sun samu ingantacciyar rayuwa.

Kara karanta wannan
Bashir Ahmad ya soki Abba Kabir kan tsawaita maganar zuwa APC, ya fadi illar dambarwar
Obasanjo ya kara da cewa makomar kowace kasa tana rataye ne da yadda ake kare yara da kula da su a yau.
Dattijon mai shekaru 88 ya na cikin mutane biyu da suka samu damar mulkar Najeriya a matsayin sojoji da kuma shugabannin farar hula a tsarin damukaradiyya.
Ya yabawa likitocin yara
Ya yaba wa likitocin yara bisa muhimmiyar rawar da suke takawa wajen kare rayukan yara, yana mai bayyana fannin likitancin yara a matsayin aiki na musamman kuma mai wahala.

Source: Facebook
“Ayyukanku aiki ne na rayuwa da mutuwa, musamman ganin cewa yara ba sa iya bayyana abin da ke damunsu kamar manya."
"Dole ne ku ji tausayinsu, ku fahimce su, kuma kura ƙoƙari fiye da yadda ake tsammani.”
- Olusegun Obasanjo
Tsohon shugaban kasar ya amince da buƙatar PAN ta naɗa shi a matsayin jakadan kula da lafiyar yara da walwalarsu, inda ya yi alkawarin ba da gudunmawa ga duk wasu shirye-shirye da za su inganta rayuwar yara a Najeriya da ma duniya baki ɗaya.
Shekarun Obasanjo a duniya
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya yi magana kan ainihin shekarunsa na haihuwa.
Obasanjo ya sake tabo batun ne yayin tattaunawa da Farfesa Toyin Falola, tare da Dr. Mathew Kukah da Farfesa Kingsley Moghalu.
Tsohon shugaban kasar ya bayyana cewa yana tantance shekarunsa ne ta hanyar duba shekarun tsofaffin abokansa na makarantar firamare da sakandare da suka yi saura a duniya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
