'Sun Yi Amfani da Keken Dinki,' An Ji Yadda Aka Kashe Fatima da Yaranta 6 a Kano
- Wani Malam Bala Abubakar, ya bayyana yadda bata-gari suka kashe Fatima Abubakar da yaranta har shida a Chiranci, jihar Kano
- Mutumin, makocin gidansu Fatima, ya ce maharan sun yi amfani da kan keken dinki wajen kwankwatsa kawunan kananan yaran shida
- Malam Bala ya kuma fadi abin da Fatima ta rika fada lokacin da ta ga har da dan uwanta a cikin wadanda za su kashe ta da 'ya'yanta
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kano - Mazauna unguwar Chiranci dake karamar hukumar Gwale a Jihar Kano, suna cikin yanayi na firgici bayan kisan gilla da aka yi wa Fatima Abubakar.
An kashe Fatima mai shekaru 35, tare da yaranta guda shida, wadanda suka hada da Maimuna, Aisha, Bashir, Abubakar, Faruk, da Abdulsalam.

Source: Facebook
Amfani da kan keken dinki wajen kisa
Wani makwabcin gidan, Malam Bala Abubakar, ya bayyana cewa ya fito daga gida sanye da tawul bayan jin ihun neman taimako daga Fatima, in ji rahoton Vanguard.
Malam Bala ya bayyana cewa maharan sun yi amfani da kan keken dinki ne wajen kwankwatsa kawunan yaran kanana, inda suka kashe su nan take.
Ya bayyana cewa daukacin yaran sun mutu ne suna zubar da jini, inda maharan suka nuna tsananin rashin imani yayin da suke kaddamar da wannan danyen aiki.
Malam Bala ya ce 'yan sanda sun kama mutane uku, ciki har da Umar Auwalu mai shekaru 23, wanda dan uwan marigayiyar ne kuma shi ya jagoranci harin.
Yadda aka kama maharan a cikin gidan
Mazauna unguwar sun kewaye gidan domin hana maharan tserewa, inda aka gano daya daga cikinsu ya boye a cikin bandaki bayan sun kashe Fatima da yaranta.
Malam Bala ya bayyana cewa marigayiyar ta rika rokon dan uwan nata tana cewa, "Umar, don Allah kada ka kashe ni," kafin ya kashe ta.
Jami’an tsaro sun kwato wasu kayayyaki daga hannun wadanda ake zargin, wadanda suka hada da tufafi masu jini, wayoyin wadanda aka kashe, takobi, da kuma babban kulki.

Source: Original
Wadanda ake zargi da kisa sun halarci jana'iza
Sarkin Chiranci, Malam Ahmad Ya’u Yahaya, ya bayyana cewa wasu daga cikin maharan sun halarci jana'izar iyalin domin nuna kamar suna jimami.
Sai dai, jami’an tsaro sun rika sanya ido kan dukkan motsin mutanen da suka zo ta'aziya har sai da suka kamo dukkan wadanda ake zargin, in ji rahoton NAN.
Yahaya ya yaba wa jami'an tsaro kan kwarewar da suka nuna wajen amfani da bayanan sirri domin kamo wadanda suka aikata wannan danyen aiki.
Mazauna unguwar sun musanta rahoton cewa ba su taimaka wa iyalin ba, inda suka ce sun yi iyakacin kokarinsu amma kaddara ta riga fata.
Al'ummar yankin sun yi kira ga gwamnati da ta tabbatar da cewa an yi adalci, domin hukunta wadanda ake zargin zai kawo musu saukin radadi.
Kisan Fatima: Bola Tinubu ya bada umarni
A wani labari, mun ruwaito cewa, Shugaba Bola Tinubu ya nuna damuwarsa tare da yin Allah-wadai da kisan gilla da aka yi wa Fatima Abubakar da yaranta shida.
Shugaban kasar ya jinjina wa rundunar yan sanda bisa yadda suka yi gaggawar kamo mutane uku da ake zargi da aikata wannan danyen aiki.
Tinubu ya ba jami'an tsaro umarnin tabbatar da cewa an gurfanar da wadannan mutane gaban kotu domin su fuskanci hukuncin da ya dace da laifinsu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


