'Yan Bindiga Sun Kutsa Wuraren Ibada a Kaduna, an Sace Mutane Sama da 100
- An shiga jimami a jihar Kaduna bayan 'yan bindiga dauke da makamai sun kai hare-hare a wasu wuraren ibada
- Tsagerun 'yan bindigan sun tasa keyar mutanen da suka je yin ibada a ranar Lahadi, 18 ga watan Janairun 2026
- 'Yan bindigan sun kai hare-haren ta'addancin ne a karamar hukumar Kajuru lokacin da jama'a suka fita domin gudanar da ayyukan bauta
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kaduna - ’Yan bindiga sun kai hare-haren kan coci uku a kauyen Kurmin Wali da ke karamar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna.
'Yan bindigan dauke da makamai sun sace sama da masu ibada 100 a yayin ayyukan coci na Lahadi, 18 ga watan Janairun 2026.

Source: Twitter
Jaridar Vanguard ta ce mazauna yankin sun ce maharan, waɗanda suka zo da yawa, sun kai harin kusan a lokaci guda, inda suka kewaye wuraren ibada tare da kwashe masu ibada.
'Yan bindiga sun kai hari a coci
A ranar Lahadi, ’yan bindigar sun kai hari kan Cocin Evangelical Church Winning All (ECWA), cocin Katolika da kuma Cocin Seraphim and Cherubim, inda suka sace daruruwan masu ibada.
Ko da yake adadin mutanen da aka sace bai bayyana ba a hukumance, ana zargin ya haura mutum 100.
An tabbatar da kai harin 'yan bindiga
Usman Danlami Stingo, ɗan majalisar dokokin jihar Kaduna, ya tabbatar da faruwar lamarin ga jaridar TheCable ta wayar tarho.
“’Yan bindiga masu ɗauke da manyan makamai sun kewaye majami’un, inda suka sace maza, mata da yara a yayin ibadar ranar Lahadi."
"Mutane tara daga cikin waɗanda aka sace sun samu damar tserewa yayin da ake kai su cikin daji.”
“Al’umma na ci gaba da kirga mutane domin tantance adadin waɗanda har yanzu ke hannun ’yan bindiga."
- Usman Danlami Stingo
Kokarin jin ta bakin kakakin rundunar ’yan sandan jihar Kaduna, Mansir Hassan, bai yi nasara ba zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.
'Yan bindiga na yawan kai hare-hare a Kaduna
A ’yan lokutan nan, hare-haren ’yan bindiga da sace-sace sun karu a jihar Kaduna.
A watan Nuwamba na shekarar 2025, ’yan bindiga sun sace Bobbo Paschal, limamin Cocin St Stephen’s da ke Kushe Gugdu a karamar hukumar Kagarko, a yayin wani hari da suka kai wa al’ummar yankin.

Source: Original
An kuma ruwaito cewa an kashe ɗan’uwan Anthony Yero, wani limami a cocin, a harin, yayin da aka sace mazauna yankin da dama.
Wata guda kafin hakan, an ce ’yan bindiga sun sace mutane da yawa a jihar Kaduna bayan kai hare-hare kan kauyuka da dama a kananan hukumomi biyu.
An bayyana cewa maharan na ɗauke da manyan makamai masu ƙarfi.
'Yan bindiga sun sace jigo a APC
A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindiga sun sace wani jigo a jam'iyyar APC a jihar Ondo da ke Kudancin Najeriya.
Shugaban karamar hukumar Ilaje ta jihar Ondo, Mista Maurice Oripenaye ya bayyana damuwa kan sace wani jigo na jam’iyyar APC, Mista Owoloemi Emorioloye.
Shugaban karamar hukumar ya ce tun bayan faruwar lamarin, ba a san inda Emorioloye yake ba, duk da kokarin tuntubarsa.
Asali: Legit.ng

