Gwamnatin Kano Ta Shige Gaba don Shari'a kan Kisan Matar Aure da Yaranta 6

Gwamnatin Kano Ta Shige Gaba don Shari'a kan Kisan Matar Aure da Yaranta 6

  • Gwamnatin Kano ta tabbatar da cewa za ta jagoranci shigar da ƙara kan kisan matar aure da ƴaƴanta shida a Dorayi Chiranchi
  • A ranar Asabar 17 ga watan Janairu, 2026 ne wasu bata-garin matasa uku suka shiga gidan Fatima Abubakar, aka kashe ta
  • Kafin wannan lokaci, gwamnatin Kano ta bayyana cewa za ta yi tsayin daka har an tabbatar da adalci a kan kisan Fatima da yaranta bakwai

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana aniyarta ta jagoranci shigar da ƙara kan mummunan kisan gillar da aka yi wa wata matar aure da ƴaƴanta shida a unguwar Dorayi Chiranchi da ke cikin birnin Kano.

Kara karanta wannan

Mahaifin Umar ya barranta da 'dansa da ake zargi da kashe yar uwarsa da yara 7

Lamarin ya girgiza zukatan jama’a tare da jefa daukacin jihar cikin alhini mai tsanani a yayin da har yanzu, mutane ke cikin alhinin faruwar lamarin.

Gwamnatin Kano za ta bi hakkin Fatima da yaransa
Mijin Fatima da yaransa 6 da aka kashe a Kano Hoto: Kwankwasiyya Trustworthy NG
Source: Facebook

BBC Hausa ta ruwaito cewa gwamnatin ta ce abin da ya faru ba wai kawai laifi ba ne, babban cin zarafi ne ga bil’adama da kuma take doka.

Gwamnati ta tsayawa marigayiya Fatima da yaranta

Gwmnati ta bayyana kisan a matsayin aikin rashin tausayi da rashin imani da ya girgiza tunanin al’ummar Kano, tare da haifar da fargaba da damuwa game da tsaron rayuka.

Wannan matsaya ta fito ne a cikin wata sanarwa da Babban Lauyan Jihar Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru Maude, SAN, ya fitar bisa umarnin Gwamna Abba Kabir Yusuf.

A cikin sanarwar, gwamnatin jihar ta miƙa ta’aziyya ga iyalan mamatan tare da jajantawa al’ummar Kano baki ɗaya kan wannan mummunan lamari.

Kara karanta wannan

Ma'aikatar shari'a: Abin da za mu yi game da kashe Fatima da yaranta 6 a Kano

Ta tabbatar wa iyalan da abin ya shafa cewa ba za a barsu su fuskanci wannan jarabawa su kaɗai ba, dole a tsaya masu domin tabbatar da adalci.

Gwamnatin Kano ta ce za ta tabbatar an yi adalci kan kashe matar aure da yaranta
Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Ya ce:

“Gwamnati na tare da iyalan da wannan lamari ya shafa, kuma za ta yi duk mai yiwuwa don ganin an yi adalci."

Ya kuma jaddada cewa gwamnati za ta bayar da cikakken goyon baya ga duk wani mataki da zai kai ga hukunta wadanda suka aikata wannan laifi.

Gwamnatin Kano na cikin alhini

Gwamnatin ta bayyana cewa wannan kisa ya saba wa kimar dan Adam, addini, da al’adun al’umma, tare da yin kira ga jama’a da su kwantar da hankalinsu su bar doka ta yi aikinta.

Haka kuma, gwamnatin Kano ta yaba wa rundunar ƴan sandan jihar bisa gaggawar ɗaukar matakin bincike da ya kai ga kama manyan waɗanda ake zargi da aikata laifin.

Ta ce saurin matakin da ƴan sanda suka ɗauka ya nuna jajircewar hukumomin tsaro wajen yaki da laifuffuka masu muni.

Kara karanta wannan

"Ba za mu lamunta ba:" Gwamna Abba ya yi alkawarin nema wa fatima da yaranta adalci

Sanarwar ta ce wannan nasara a bincike na taimakawa wajen dawo da amincewar jama’a ga hukumomin tsaro da tsarin shari’a.

A cewar Babban Lauyan Jihar, Ofishin Babban Lauya zai jagoranci shari’ar tare da kafa tawagar lauyoyi ta musamman.

Manufar hakan ita ce tabbatar da cewa an gudanar da shari’a cikin gaskiya, sauri, da bin ka’idojin doka, domin ganin adalci ya tabbata ga mamatan da iyalansu.

Gwamnatin Kano ta kammala da jaddada kudirinta na kare rayuka da dukiyoyin al’umma, tare da tabbatar da cewa duk wanda ya aikata laifi zai fuskanci hukunci bisa doka.

An kama matasan da suka kashe matar aure

A wani labarin, kun ji cewa rundunar ’yan sandan Kano ta tabbatar da kama wasu mutane uku da ake zargi da hannu a kisan Fatima Abubakar da yaranta a birnin Kano a ranar Asabarm 17 ga watan Janairu, 2026.

Kara karanta wannan

Yadda yaron shago ya hallaka mai gidansa makonni 3 bayan aurensa a Gombe

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, CSP Abdullahi Kiyawa, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai a ranar Lahadi 18 ga watan Janairu, 2026 inda ya ce jami'an tsaro sun yi aiki.

A cewar Kiyawa, rundunar ta dauki matakan tsaro na gaggawa bayan faruwar lamarin, domin bin sawun wadanda ake zargi da kuma tabbatar da cewa an kamo su ba tare da bata lokaci ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng