Dakarun Sojojin Najeriya Sun Shirya Yin Bore? An Ji Gaskiyar Zance
- An yada wasu rahotanni masu cewa dakarun rundunar sojojin Najeriya na shirin yin bore saboda karancin albashi da alawus
- Rundunar sojojin Najeriya ba ta yi wata-wata ba, ta fito ta maida martani kan rahotannin wadanda aka yada a intanet
- Ta bayyana cewa jin dadi da walwalar jami'anta na daga cikin abubuwan da ta fi ba muhimmanci matuka gaya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Rundunar sojojin Najeriya ta yi martani kan rahotannin da ke zargin cewa sojoji na shirin tayar da bore.
Rundunar sojojin ta karyata batun boren saboda karancin albashi, alawus da matsalolin walwala, tana mai bayyana rahoton a matsayin karya kuma mai cike da ruɗani.

Source: Twitter
An bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da daraktar hulɗa da jama’a ta rundunar sojojin kasa, Kanal Appolonia Anele, ta fitar a shafin X a ranar Litinin, 19 ga watan Janairun 2026.

Kara karanta wannan
Sojojin saman Najeriya sun yi ruwan bama bamai a Borno, mutane fiye da 40 sun mutu
Rundunar ta jaddada cewa shugabancinta na nan daram wajen kula da walwalar jami’anta, ladabi da kwarewa a aiki.
Me rundunar sojoji ta ce kan batun bore?
A cewar sanarwar, rundunar ta bayyana rahoton a matsayin yunkuri na ganganci domin tayar da hankali, ɓata suna da kuma raunana amincewar jama’a da tsaron kasa.
“An ja hankalin rundunar sojojin Najeriya kan wani rubutu da ke yawo a intanet da ke zargin cewa sojoji na barazanar tayar da bore saboda albashi da alawus."
"Muna kallon rahoton a matsayin karya, mai cike ruɗani kuma cike da tayar da hankali wanda aka shirya da gangan."
- Kanal Appolonia Anele
Kanal Anele ta jaddada cewa babu wani lokaci da aka taɓa samun barazanar bore a cikin rundunar sojojin Najeriya, tana mai cewa bore babban laifi ne a karkashin dokar soja kuma ya sabawa ɗabi’a, ladabi da kwarewar sojojin Najeriya.
Sojojin Najeriya na da biyayya
Ta ƙara da cewa jami’ai da sojojin rundunar na ci gaba da nuna biyayya ga kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya da kuma babban kwamandan rundunar sojojin kasa.
Rundunar ta kuma soki rahoton bisa dogaro da bayanai marasa tushe da ba a san inda suka fito ba, da ake yadawa ta hanyoyin da ba na hukuma ba.
Ta jaddada cewa irin waɗannan labarai ba sa wakiltar ra’ayi ko halayen sojojinta, waɗanda aka horas da su, su bi hanyoyin da doka ta tanada wajen gabatar da korafe-korafe ta hanyar da ta dace.
Yadda tsarin albashin sojoji yake
Dangane da batun albashi da alawus, sanarwar ta fayyace cewa karin albashi sakamakon ƙarin mukami wani ɓangare ne kaɗai na albashin soja, kuma bai kamata a gabatar da shi a matsayin jimillar abin da soja ke samu ba.
“Albashin soja ya kunshi albashi na bai ɗaya, alawus bisa matsayi, alawus na aiki, alawus na fagen fama da na wahala, da sauran hakkoki da ke bambanta bisa inda aka tura soja, ƙwarewa da nauyin aiki."
- Kanala Appolonia Anele

Source: Facebook
Ana kula da albashin sojoji
Sabanin zargin sakaci, rundunar ta ce gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na ci gaba da nuna himma wajen kula da walwalar sojoji da ingancin ayyukansu, musamman a daidai lokacin da ƙalubalen tsaro ke karuwa.
A ƙarshe, sanarwar ta sake jaddada cewa rundunar sojojin Najeriya runduna ce mai haɗin kai, ladabi da kwarewa, wadda ta mayar da hankali kan aikinta na kare ikon kasar da tallafa wa ayyukan tsaron cikin gida.
Ta yi kira ga jama’a da su yi watsi da rahoton karya, su kuma dogara da hanyoyin sadarwa na hukuma domin samun sahihin bayani kan rundunar sojojin kasa.
Dakarun sojoji sun kashe 'yan bindiga
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar ragargazar 'yan bindiga yayin wani artabu a jihar Kaduna.
Sojojin sun samu nasarar hallaka wasu daga cikin ’yan bindiga, aka ceto wata mata da aka sace tare da kwato makamai.
Dakarun sun yi musayar wuta da ’yan ta’addan, lamarin da ya yi sanadiyyar hallaka mutane hudu daga cikinsu, yayin da sauran suka tsere.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

