Azumi Saura Wata 1: Sarkin Musulmi Ya ba da Umarnin Duba Watan Sha'aban 1447
- Majalisar mai alfarma Sarkin Musulmi ta umarci Musulmi a fadin Najeriya da su fara duban jinjirin watan Sha’aban 1447AH a ranar Litinin, 19, Janairu, 2026
- Sanarwar ta fito ne daga Kwamitin Shawarwari kan Harkokin Addini na Majalisar, inda aka bayyana cewa ranar ta dace da 29 ga watan Rajab 1447AH
- An bukaci Musulmi da su ba da rahoton ganin wata ga hakiman gundumomi domin isarwa ga Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Sokoto – Majalisar Sarkin Musulmi ta umarci Musulmai su fara duban jinjirin watan Sha’aban 1447AH a ranar Litinin, 19, Janairu, 2026.
Sanarwar ta bayyana ne a wata takarda da Wazirin Sakkwato kuma Shugaban Kwamitin Shawarwari kan Harkokin Addini, Farfesa Sambo Junaidu, ya sanya wa hannu.

Source: Getty Images
Punch ta wallafa cewa sanarwar ta ce ranar Litinin ta zo daidai da 29 ga watan Rajab 1447AH, wanda a bisa koyarwar Musulunci ita ce ranar da ake duba jinjirin wata.
Umarnin fara duba watan Sha'aban
Kwamitin Shawarwari kan Harkokin Addini ya bayyana cewa ayyana ranar duban jinjirin watan Sha’aban ya dace da al’adar Musulunci wadda ke bukatar a tabbatar da ganin wata kafin shiga sabon wata.
A cikin sanarwar, kwamitin ya jaddada cewa duban jinjirin wata a ranar 29 ga Rajab 1447AH ya dace da koyarwar Musulunci, inda za a tabbatar da shigowar Sha’aban ta hanyar gani ko cikar kwanaki 30.
Haka kuma, sanarwar ta bayyana cewa wannan mataki ba sabon abu ba ne, ci gaba ne da bin tsarin da fadar mai alfarma Sarkin Musulmi ke bi a duk lokacin da ake dab da fara sabon watan Hijira.
Kiran da aka yi ga al’ummar Musulmi
Majalisar Sarkin Musulmi ta yi kira ga al’ummar Musulmi da su duba jinjirin wata da niyyar yin aikin addini.
Kwamitin ya bukaci kowa da kowa da ya ga jinjirin watan da ya gaggauta kai rahoto ga hakimin gundumarsa ko kauyensa.
An bayyana cewa wadannan rahotanni za su bi matakan tantancewa kafin a mika su ga mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, wanda shi ne Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci a Najeriya.
Tribune ta ce kwamitin ya jaddada cewa aikin duban jinjirin wata nauyi ne na addini da ke bukatar kulawa da gaskiya, tare da kauce wa yada bayanan da ba su da tushe.

Source: Facebook
Sarkin Musulmi ya yi fatan alheri
A karshen sanarwar, Kwamitin Shawarwari kan Harkokin Addini ya yi addu’a ga Allah Madaukakin Sarki da Ya ba al’ummar Musulmi ikon sauke wannan nauyi cikin nasara.
Kwamitin ya roki Allah da Ya shiryar da al’umma, Ya kuma tabbatar da ganin jinjirin cikin sauki da lumana. A cewarsu, hadin kai da bin ka’ida zai taimaka wajen fara watan Sha’aban cikin tsari da kwanciyar hankali.
Sarkin Musulmi ya yi kira ga Tinubu
A wani rahoton, kun ji cewa Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III ya yi magana game da tsaron Najeriya.
Ya yi kira ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya ziyarci jihar Neja bayan wasu 'yan bindiga sun yi wa 'yan kasuwa yankan rago.
Fadar Sarkin Musulmi ta yaba wa dakarun Najeriya kan yadda suke fafatawa da 'yan ta'adda a yankuna daban-daban domin kawo zaman lafiya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


