An Yanke wa Wani Dan Najeriya Hukuncin Kisa, Za a Rataye Shi har Lahira
- Babbar Kotun Akwa Ibom ta yanke wa Anwanga Effiong Udofia hukuncin kisa ta rataya saboda kashe Aniekan Edet
- Kotun ta tabbatar da cewa Udofia ya bi yaron da adda, ya farmake shi yayin da yake kan hanyarsa zuwa makaranta a Itoko, ranar 6 ga Disamba 2016
- Al’ummar Itoko sun ce hukuncin ya kawo ƙarshen shari’ar da ta daɗe tana addabar su, tare da nuna cewa adalci ya samu duk da jinkiri
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Uyo, Akwa Ibom - Shari’ar kisan gillar da aka yi wa Aniekan Idongesit Edet, ɗalibi mai shekara tara, ta ƙare a babbar Kotu a Akwa Ibom.
Mai shari’a Archibong Archibong ya yanke hukunci kan Anwanga Effiong Udofia, mai shekara 38, inda ya same shi da laifin kisan yaron tare da yanke masa hukuncin kisa ta rataya.

Source: UGC
Za a rataye mutum kan kisan kai
Shari’ar da ta fara tun shekarar 2016 ta ɗauki lokaci mai tsawo kafin kotu ta kammala sauraron dukkan shaidu da hujjojin da ɓangarorin biyu suka gabatar, cewar Leadership.
Bayanan shari’a sun nuna cewa lamarin ya faru ne ranar 6 ga Disamba 2016 a ƙauyen Nung Oku Akpasima da ke Ibesikpo Asutan, lokacin da yaron ke tafiya makaranta.
An bayyana cewa wanda ake tuhuma ya bi yaron dauke da adduna biyu, ɗaya a hannu ɗaya kuma ɗaya a ɓoye a cikin wandonsa.
Shaidu sun nuna cewa Udofia ya cimma yaron, ya rinjaye shi, sannan ya yi masa munanan raunuka da suka yi sanadin mutuwarsa nan take.
Wani abokin mamacin, ɗalibin aji hudu, ya shaida wa kotu yadda ya ga Udofia yana bin Aniekan kafin ya gudu saboda tsoro.
Shaidar ta ce:
“Na ga Anwanga dauke da adduna biyu, yana bin Aniekan zuwa cikin daji kusa da makaranta, ban san abin da ya faru daga baya ba.”

Source: Original
Yadda aka gano gawar dalibin firamare
Washegari, an gano gawar yaron cikin jini, sanye da kayan makaranta, bayan yara sun je neman itacen wuta a yankin.
Rahoton ya ce an yanke hannun yaron guda ɗaya, yayin da wuyansa ke dauke da babban rauni da ya yi kama da bugun adda.
Daga bisani, ‘yan sanda suka gurfanar da Udofia a gaban kotu bisa laifin kisa, sabanin sashe na 326(1) na dokar laifuka ta jihar Akwa Ibom.
A yayin shari’ar, masu gabatar da ƙara sun kira shaidu huɗu tare da gabatar da hujjoji biyar domin tabbatar da tuhumar.
Wanda ake tuhuma shima ya kare kansa a gaban kotu, amma alkali ya ce hujjojin gwamnati sun wadatar ƙwarai.
Mai shari’a Archibong ya ce an tabbatar da laifin fiye da shakku, sannan ya yanke hukuncin kisa ta rataya.
Ya ce:
“Na same ka da laifi, kuma hukuncin kotu shi ne a rataye ka har sai ka mutu. Allah ya ji ƙanka.”

Kara karanta wannan
Tirkashi: Kotu ta tura tsohon shugaban kasa gidan yari, zai yi zaman shekaru 5 a Korea
Wani jagoran al’umma, Chief Udobong Akai, ya ce hukuncin ya kawo ƙarshen baƙin cikin da ya dade yana damun al’ummar Itoko.
Ya ƙara da cewa, duk da jinkirin shari’a, hukuncin ya nuna cewa adalci zai iya zuwa koda bayan dogon lokaci, cewar Daily Post.
Kotu ta yanke wa sojoji hukuncin rataya
A wani labarin, mun ruwaito cewa, kotun sojoji a Jos ta yanke wa soja hukuncin rataya bayan kama shi da laifin kashe mai Keke Napep a jihar Bauchi.
Rahotanni sun nuna cewa sojan ya hada baki da abokinsa, suka jawo marigayin cikin gida, suka buge shi, sannan suka shake shi.
Alkalin kotun ya nuna damuwa kan yadda soja ya canza daga mai kare jama’a zuwa kisa yana mai kiran aikinsa abin kunya ga rundunar.
Asali: Legit.ng

