An Barke da Murna, Farashin Abinci Ya Sake Zubewa a Kasuwanni
- Rahotanni sun tabbatar da cewa farashin kayan abinci ya ci gaba da sauka a kasuwannin Abuja
- Wasu majiyoyi na ganin haka ya biyo bayan bukukuwan Kirsimeti, lamarin da ya kawo sauƙi ga mazauna birnin
- Hukumar NBS ta ce hauhawar farashin abinci ta ragu zuwa kashi -0.36% a Disamba 2025, sakamakon wadatar kayan gona
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - Farashin wasu muhimman kayan abinci ya sake sauka a kasuwannin Babban Birnin Tarayya (FCT), Abuja.
Wannan lamarin da ya janyo farin ciki a tsakanin mazauna birnin duba da wahalar da aka sha a baya.

Source: Getty Images
Farashin abinci ya sauka a Abuja
Binciken kasuwa da aka yi ya nuna cewa bayan bukukuwan Kirsimeti, farashin kayan abinci kamar tumatir, barkono, albasa, dankali da wake ya ragu a yawancin kasuwanni, cewar Premium Times.

Kara karanta wannan
"Ba za mu lamunta ba:" Gwamna Abba ya yi alkawarin nema wa fatima da yaranta adalci
Wasu mazauna yankin sun ce raguwar farashin ta kawo musu sauƙi, amma sun bukaci gwamnati ta tabbatar da dorewar lamarin, ganin yadda ƙarfin sayen jama’a ke ƙara raguwa.
Rahoton Hukumar Kididdiga ta Ƙasa (NBS) ya nuna cewa hauhawar farashin abinci ta ragu zuwa kashi -0.36 cikin ɗari a watan Disamba 2025, idan aka kwatanta da kashi 1.13 cikin ɗari da aka samu a Nuwamba.
NBS ta danganta raguwar farashin da sauƙaƙewar farashin kayan abinci kamar tumatir, garri, ƙwai, dawa, wake, albasa, barkono, alkama da kayan marmari.
A kasuwar Garki Model, an lura da raguwar farashin tumatir, barkono da albasa, inda kwandon tumatir ya ragu daga N7,000 zuwa kusan N5,000, yayin da barkono ya sauka zuwa N2,500.
Sai dai a wasu lokuta, kamar dankalin turawa, an samu hauhawar farashi, inda farashinsa ya tashi zuwa N10,000 kan kwando guda.

Source: Original
Yadda farashi yake a kasuwar Gwagwalada
A kasuwannin Nyanya, Gwagwalada, Apo da Dei-Dei, an samu sauƙin farashi a yawancin kayan abinci, yayin da farashin shinkafa ya kasance daidaitacce.
Wasu ‘yan kasuwa sun danganta saukar farashin da ƙarancin kuɗin sayayya a watan Janairu da kuma yawaitar kayan gona daga gonaki.
Masana noma da ƙungiyoyin manoma sun gargadi cewa wannan sauƙin farashi na iya zama na ɗan lokaci idan ba a ɗauki tsare-tsare na dogon lokaci ba.
Shugaban Ƙungiyar Manoman Najeriya (AFAN), Kabir Ibrahim, ya ce dole ne gwamnati ta ƙarfafa noman rani, tsaro, sufuri da samun kuɗaɗen shiga domin tabbatar da dorewar sauƙin farashin abinci.
Wasu mazauna Abuja sun ce duk da raguwar farashi, har yanzu mutane da dama ba sa iya sayen kayan abinci saboda ƙarancin albashi da rashin biyan albashi a kai a kai.
Farashin abinci: Tinubu ya yi albishir
Mun ba ku labarin cewa shugaba Bola Tinubu na Najeriya ya yi hasashe game da farashin kayan abinci yayIn da aka shiga sabuwar shekarar nan da aka shiga.
Tinubu ya yi albishir ga yan kasa cewa za a samu raguwar hauhawar farashin kaya a shekarar, yana cewa ana iya saukowa ƙasa a 2026.
Fadar Shugaban Ƙasa ta ce wannan sauyi zai inganta rayuwar jama’a tare da hanzarta bunƙasar tattalin arzikin Najeriya baki ɗaya.
Asali: Legit.ng
