Biki Bidiri: Matawalle Zai Aurar da ’Ya’yansa 9 Rana Daya a Abuja
- Ministan Tsaro na Kasa, Bello Matawalle, na shirin aurar da ’ya’yansa har guda tara da za a gudanar a rana guda a Abuja
- Gayyatar bikin auren ta bazu a kafafen sada zumunta, inda aka bayyana cewa za a gudanar da shi a Masallacin Kasa da ke Abuja
- APC ta ce shirye-shiryen bikin sun yi nisa, kuma an kafa kwamitoci domin tabbatar da nasarar taron a watan Fabrairun 2026
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Ana ci gaba da shirye-shirye gadan-gadan domin bikin aurar da ’ya’ya tara na Ministan Tsaro na Kasa, Bello Matawalle.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa za a gudanar da gagarumin bikin daurin auren ne a birnin tarayya Abuja.

Source: Twitter
Za a yi bikin 'ya'yan Matawalle 9
Katin gayyatar bikin auren, wanda ke dauke da hoton ministan, ya bazu sosai a kafafen sada zumunta, inda aka gano, cewar Punch.
A cewar katin gayyatar, za a gudanar da bikin auren ne a Masallacin Kasa da ke Abuja da misalin karfe 1:30 na rana a ranar 6 ga watan Fabrairun 2026.
Sunayen ’ya’yan da za a aurar sun hada da Ibrahim, Suraj, Safiya, Maryam, Aisha, Fahad, Muhammad, Nana Firdausi da Farida.

Source: Original
APC ta fadi shirin da take yi
Da yake magana da yan jarida, kakakin jam’iyyar APC a Jihar Zamfara, Yusuf Idris, ya bayyana cewa ’ya’yan minista Matawalle da za a aurar sun kunshi maza biyar da mata hudu.
Ya ce, da yardar Allah, za a gudanar da bikin auren ne a Masallacin Kasa da ke Abuja, inda ya kara da cewa shirye-shiryen taron sun kai mataki mai kyau.
Idris ya bayyana cewa yana daga cikin kwamitin da aka kafa domin shiryawa da gudanar da bikin, yana mai tabbatar da cewa komai yana tafiya yadda ya kamata domin ganin an gudanar da biki cikin kwanciyar hankali.
A cewarsa:
“Da yardar Allah, za a gudanar da bikin a Masallacin Juma’a na Abuja a ranar 6 ga Fabrairu. Ina kuma so in bayyana cewa ‘ya’yan ministan da za su yi aure su ne maza biyar da mata huɗu.
Ni na kasance cikin ‘yan kwamitin da ke shirya wannan babban biki, kuma a halin yanzu shirye-shiryen sun kai wani mataki don tabbatar da an gudanar da bikin cikin kwanciyar hankali a Abuja a watan gobe.”
Rahoton ya nuna cewa ana sa ran bikin auren zai samu halartar manyan baki daga sassa daban-daban na kasar nan, sakamakon matsayi da Bello Matawalle ke rike da shi a gwamnatin tarayya.
APC ta wanke Matawalle kan kama matashi
Mun ba ku labarin cewa jam’iyyar APC a Zamfara ta wanke Ministan Tsaro Bello Matawalle daga zargin hannu a kama hadimin gwamna, Dauda Lawal Dare.
APC ta ce rundunar musamman ƙarƙashin ofishin Nuhu Ribadu ce ta kama shi bisa zargin alaƙa da ta’addanci da laifuffukan yanar gizo.
Jam’iyyar ta jinjina wa hukumomin tsaro, tana cewa Matawalle yana ƙasashen waje kan aikin ƙasa lokacin kama mutumin.
Asali: Legit.ng

