Yan Sanda Sun Kama Mutum 3 da ake Zargi da Kashe Matar Aure da Yaranta 6 a Kano
- Rundunar ’yan sanda ta kama manyan mutane uku da ake zargi da jagorantar kisan wata matar aure da ’ya’yanta shida a Dorayi Chiranchi, Kano
- Jagoran mutanen da suka kai mummunan hari, Umar Auwalu, ya amsa laifin tare da bayyana rawar da kungiyar ta taka a wasu hare-hare a baya
- Mutanen sun jawo tashin hankali a Arewacin Najeriya bayan sun kai wani mummunan hari da tsakar rana gidan mutanen, tare da yi masu kisan gilla
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, bisa umarnin Sufeto-Janar na ’Yan Sanda, IGP Kayode Adeolu Egbetokun, ta kama wasu mutane uku da ake zargi da kashe Fatima Abubakar da yaranta.
Kakakin rundunar na Kano, CSP Abdullahi Kiyawa ne ya tabbatar da haka a wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai a ranar Lahadi.

Kara karanta wannan
"Ba za mu lamunta ba:" Gwamna Abba ya yi alkawarin nema wa fatima da yaranta adalci

Source: UGC
A sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Kiyawa ya ce yan sandan sun yi amfani da binciken sirri da dabarun aikin wajen kama mutanen da ake zargi da kisan da ya girgiza jama'a a ranar 17 ga Janairu, 2026.
Yan sanda sun kama bata-gari a Kano
A karkashin jagorancin Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, wata tawaga ta kwararrun jami’ai ta gudanar da samame na musamman.
Sun yi aikin daga 10.00 na dare zuwa 4.00 na asubahin ranar 18 ga Janairu. A yayin wannan aiki ne aka kama wadanda ake zargi uku, bayan samun sahihan bayanan sirri.
Mutanen da aka kama sun hada da Umar Auwalu, dan shekara 23 daga unguwar Sabuwar Gandu, Isyaku Yakubu mai lakabin “Chebe”, dan shekara 40 daga Sagagi.
Sai kuma Yakubu Abdulaziz mai lakabin “Wawo”, dan shekara 21 daga Sabon Gida Sharada, dukkaninsu a cikin birnin Kano.
Rundunar ta bayyana cewa kama su ya kasance sakamakon tsauraran matakan tsaro da aka dauka bayan faruwar lamarin.
Matasa sun amsa laifin kisa a Kano
A cewar bayanin rundunar, jagoran ta'addancin, Umar Auwalu, wanda dan uwa ne ga marigayiyar, ya amsa laifin hannu a cikin kisan.

Source: Facebook
Ya kuma bayyana cewa sun taba aikata wasu munanan laifuffuka a baya, daga ciki har da kisan wasu mata biyu a Tudun Yola a cikin birnin Kano.
Rundunar ta ce an kwato kayayyaki da dama daga hannun wadanda ake zargi, da suka hada da tufafi masu tabon jini, wayoyin marigayiyar guda biyu, adda, gora, wasu kudi da ake zargin an kwace a wurin, da kuma wasu makamai masu hadari.
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta yaba da kokarin jami’an da suka gudanar da aikin, tare da gode wa al’umma bisa addu’o’i, goyon baya da hadin kai.
Ta kuma tabbatar wa jama’a cewa za ta ci gaba da jajircewa wajen ganin an gurfanar da duk masu aikata laifuka a gaban kuliya domin tabbatar da adalci da zaman lafiya a jihar.
Kian bayin Allah a Kano ya fusata Gwamna
A wani labarin, kun ji cewa Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana matuƙar baƙin ciki da alhini kan kisan gilla da aka yi wa wata mata ’yar Kano, Fatima Abubakar tare da ’ya’yanta a unguwar Dorayi Chiranchi.
Gwamnan ya bayyana lamarin a matsayin mummunan aiki na rashin imani, marar dalili, kuma babban cin mutunci ga darajar ɗan Adam tare da alkawarin gwamnati ba za ta bari hakkinsu ya tafi a banza ba.
Gwamna Abba ya yi ta'aziyyar kashe uwa da yaranta Gwamnan ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan da abin ya shafa, mazauna Dorayi Chiranchi, da kuma al’ummar Jihar Kano baki ɗaya bisa wannan rashin imani.
Asali: Legit.ng

