Harin Amurka: An ‘Gano’ inda ’Yan Ta’adda Ke Tserewa saboda Ruwan Wuta a Sokoto

Harin Amurka: An ‘Gano’ inda ’Yan Ta’adda Ke Tserewa saboda Ruwan Wuta a Sokoto

  • Hare-haren makaman Amurka a Sokoto sun janyo cece-kuce, inda ake cewa kungiyar Lakurawa ce aka kai wa hari
  • Rahotanni sun nuna Lakurawa na kokarin guduwa daga Sokoto zuwa Nijar ko Chadi bayan an kashe sama da mutum 150
  • Masana sun gargadi cewa hare-haren kasashen waje na iya kara tsananta tsaro da haddasa ramuwar gayya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Sokoto - Hare-haren makaman linzami da Amurka ta kai a jihar Sokoto a watan Disambar 2025 sun yi tasiri a yaki da ta'addanci.

An tabbatar da cewa harin ya yi 'yan ta'adda illa sosai duk da cewa bai su kawo karshen matsalar ba.

Harin Amurka ya yi tasiri kan yan kungiyar Lakurawa a Sokoto
Taswirar jihar Sokoto da Amurka ta kai hari. Hoto: Legit.
Source: Original

Rahoton Tribune ya ce an gano wasu yan kungiyar Lakurawa na tserewa daga wasu yankunan jihar Sokoto zuwa Nijar.

Harin da Amurka ta kai a Sokoto

Kara karanta wannan

Ana fargabar harin Bello Turji, 'yan bindiga sun yi ta'asa a Sokoto

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa an kai harin ne domin murkushe kungiyar ISIS da ke zargin tana aiki a yankin, tare da kare Kiristoci marasa laifi.

Sai dai masana sun ce babu wata hujja ingantacciya da ke nuna ISIS na da sansani ko karfin aiki a Sokoto.

Rahotanni sun nuna mafi yawan wadanda rikicin tsaro ya shafa a yankin Musulmai ne daga kauyukan da ke fama da fashi, gudun hijira da rashin tsaro mai tsanani.

A Arewa maso Yamma, rikicin tsaro ya samo asali ne daga bangarori biyu: ‘yan bindiga masu neman kudi da kuma kungiyoyin tsattsauran ra’ayi.

Daga cikin wadannan kungiyoyi akwai Lakurawa, wacce ke da manufar kafa cikakkiyar shari’ar Musulunci a yankunan da take iko da su, cewar Premium Times.

Rahotanni sun nuna Lakurawa na dauke da mayaka daga kasashen Mali, Nijar, Chadi da Najeriya, kuma ta kafa sansani a dazukan Tangaza, Gudu da Kware tun 2017, inda ake kiyasin tana da mayaka kusan 800.

Kungiyar ta haramta rawa da wake-wake, ta hana sayar da giya da taba sigari, ta kuma tilasta haraji a kan jama’a ta hanyar karbar shanu da karfi.

Kara karanta wannan

An gano gargadin da aka yi wa Donald Trump har Amurka ta fasa kai hari Iran

Yadda Lakurawa ke barin yankunan Sokoto

Shaidu sun ce hare-haren sun kashe kimanin mayaka 155 na Lakurawa, ciki har da shugabanni, tare da lalata rabin shanunsu, duk da haka, kungiyar ta kai hari Birnin Yauri a Kebbi inda aka kashe fararen hula 21.

Bayan harin, Lakurawa na kokarin tserewa daga Sokoto zuwa Nijar ko Chadi, sai dai hakan na da hadari saboda tsauraran matakan tsaro. An ruwaito cewa an kashe mayaka 20 yayin yunkurin tsallaka iyaka.

Masana sun gargadi cewa hare-haren waje na iya janyo ramuwar gayya daga ‘yan bindiga da kungiyoyin tsattsauran ra’ayi.

A karshe, rahoton ya nuna cewa dogaro da kasashen waje wajen kai hare-hare ya fallasa raunin tsarin tsaron Najeriya, tare da kara tambaya kan ikon gwamnati wajen kare ‘yan kasarta.

Ta'addanci: Yan Sokoto na tserewa zuwa Nijar

Mun ba ku labarin cewa mazauna Isa a Sokoto sun bayyana yadda barazanar Bello Turji ta sa iyalai ke barin gidajensu suna tsallakawa zuwa Jamhuriyar Nijar.

Kara karanta wannan

Magana ta girma: Iran da Amurka sun nuna wa juna yatsa a taron tsaro na duniya

Rahotanni sun nuna cewa sama da kauyuka 20 sun watse bayan sababbin barazana da hare-haren ‘yan bindiga ya kara bulla a yankunansu.

Wasu mazauna sun ce duk da hadarin hanya da barazanar kama su, guduwa zuwa wasu wurare kamar Nijar ya fi masu zama a yankin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.