Hotuna: Yadda Miliyoyin Mutane Suka Halarci Mauludin Sheikh Ibrahim Nyass a Katsina
- Kimanin mabiya Tijjaniyya miliyan uku ne suka hallara a Katsina domin bikin Mauludin Sheikh Ibrahim Nyass na shekarar 2026
- Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na II ya bukaci Musulmi da su jajirce wajen neman ilimi da sana'o'i domin dogaro da kansu
- Gwamna Dikko Radda ya yaba wa malaman addini kan addu'o'in zaman lafiya da suke yi wa Katsina da ma Najeriya baki daya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Katsina - An kiyasta cewa mabiya ɗarikar Tijjaniyya kusan miliyan uku ne daga ciki da wajen Najeriya suka hallara a birnin Katsina ranar Asabar domin taron Mauludin Sheikh Ibrahim Nyass.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa ƙungiyar "Majma’u Ahbab Sheikh Ibrahim Nyass" ce ta shirya wannan ƙasaitaccen taro a filin wasa na Muhammad Dikko.

Source: Twitter
Karancin masauki da karamcin mutanen Katsina
Shugaban kwamitin shirya taron, Sheikh Muhammad Hadi-Balarabe, ya bayyana cewa sun yi hasashen samun baƙi miliyan huɗu daga jihohi 36 na Najeriya da kuma ƙasashen Afirka.
Bincike ya nuna cewa kusan dukkan ɗakunan otal-otal na birnin Katsina sun cika maƙil, lamarin da ya sa mazauna garin bayar da gidajensu kyauta ga baƙi.
Wasu baƙin da ba su sami masauki ba ko kuma ba su da ikon biyan otal, sun kwana ne a filin wasan duk da tsananin sanyin hunturu da ake yi.
Kafin ƙarfe tara na safe, filin wasan ya riga ya cika maƙil inda mutane suka mamaye dukkan kujeru da kuma cikin filin ƙwallon baki ɗayansa don sauraron malamai.
Babban titin da ya tashi daga zagayen WTC zuwa zagayen Barhin ya cika makil da mutane, lamarin da ya dakatar da zirga-zirgar ababen hawa a yankin gaba ɗaya.
Tasirin taron ga harkokin tattalin arziki
Wannan taro ya buɗe kofofin kasuwanci ga masu siyar da abinci, ruwa, magungunan gargajiya, tufafi da littattafai, waɗanda suka sami riba mai yawa sakamakon yawan jama'a.
Yayin jawabin sa, Sheikh Ibrahim Dahiru-Bauchi ya gode wa gwamnatin Jihar Katsina bisa karɓar baƙuncin wannan taro, tare da yin addu'ar dorewar zaman lafiya a yankin Arewa.

Kara karanta wannan
Anas Aremeyaw: An kaddamar da shirin horar da ƴan jarida kan amfani da fasahar AI
Sarkin Kano, Alhaji Muhammad Sanusi II, ya yi kira ga Musulmi da su tsayu tsayin daka wajen bin umarnin Mahalicci tare da koyi da koyarwar Annabi Muhammad, in ji rahoton Daily Trust.
Sarki Sanusi ya kuma ba su shawarar ƙarfafa neman ilimi da yin sana'o'i domin dogaro da kai maimakon jiran tallafi ko roƙon abin hannun wasu mutane daban.

Source: Twitter
Jawabin gwamna da addu'o'in neman zaman lafiya
Gwamna Dikko Radda na Jihar Katsina ya nuna godiyarsa ga masu shirya taron, inda ya bayyana cewa addu'o'in malaman na taimakawa wajen dawo da zaman lafiya a jihar.
Mataimakin Sheikh Mahi Ibrahim-Nyass, wato Sheikh Muhammad Ibrahim-Nyass, ya yi addu'ar neman rahama ga marigayi Sheikh Dahiru Usman-Bauchi wanda ya rasu wasu watanni da suka gabata.
Malamin ya buƙaci Musulmin duniya da su ci gaba da kasancewa tsintsiya ɗaya madaurinki ɗaya, tare da nuna wa juna ƙauna da riƙon addini cikin gaskiya da amana.
An kammala taron da addu'o'i na musamman ga Jihar Katsina, Najeriya baki ɗaya, da kuma shugabannin ƙasar domin samun nasara wajen tafiyar da ayyukan da suka sa a gaba.
Kalli hotunan taron a kasa:

Kara karanta wannan
Jigon ADC ya zargi Tinubu da sakaci, an tsunduma mutane miliyan 141 a bakin talauci
Radda ya gana da Sarki Sanusi II
Tun da fari, mun ruwaito cewa, Gwamna Dikko Radda ya kai ziyara ta girmamawa ga Sarki kuma Khalifan Tijjaniyya, Muhammadu Sanusi II, domin tattauna batun Mauludin Nyassa a jihar.
Gwamnan jihar na Katsina ya fara duba shirye-shirye a filin wasan Muhammadu Dikko gabanin babban taron Mauludin Tijjaniyya na kasa na shekarar 2026 kafin zuwa wajen Sarki Sanusi II.
An shirya cewa taron zai ja hankalin sama da mutane miliyan 4 daga kasashe kusan 15, lamarin da ya kara wa taron muhimmanci ga Katsina da Najeriya baki daya.
Asali: Legit.ng
