Yadda Yaron Shago Ya Hallaka Mai Gidansa Makonni 3 bayan Aurensa a Gombe

Yadda Yaron Shago Ya Hallaka Mai Gidansa Makonni 3 bayan Aurensa a Gombe

  • Wani rikici tsakanin mai gida da yaron shagonsa ya rikide zuwa kisa a Gombe, bayan zargin sata da ya janyo husuma
  • Shaidu sun ce yaron shagon ya caka wa mai gidansa almakashi lokacin da ya yi yunƙurin dukan ɗaya daga cikinsu
  • Marigayin ya rasu makonni kaɗan bayan daurin aurensa, yayin da ake dakon sanarwa daga hukumomin tsaro da gwamnati

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Gombe - Al'umma da dama sun shiga jimami a jihar Gombe bayan kisan wani matashi saboda samun wata yar karamar hatsaniya.

Lamarin ya faru ne yammacin Asabar 17 ga watan Janairun 2026 bayan wata hatsaniya ta ɓarke tsakanin Abdul’aziz Aliyu da yaron shagonsa.

Yaron shago ya kashe mai gidansa a Gombe
Marigayi Abdulaziz Aliyu da aka hallaka a Gombe. Hoto: Abubakar Mohammed.
Source: Facebook

Ana jimamin mutuwar matashi a Gombe

Day daga cikin abokansa, Ishaq Adam Mai Hula ya bayyana wa wakilin Legit Hausa faruwar lamarin inda ya ce yaron shagonsa ne ya caka masa almakashi.

Kara karanta wannan

Kano ta yi babban rashi, attajiri kuma tsohon shugaban kasuwar kwari ya rasu

Ishaq ya tabbatar da cewa marigayin 'da ne ga limamin masallacin Darul Hadith da ke unguwar Dubai da ake kira Malam Ali Madina.

Ya tabbatar da cewa matashin ya yi aure a watan Disambar shekarar 2025 da ta gabata wanda yanzu bai wuce makonni uku ba kenan.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa marigayin da aka fi sani da Dan Malam ya gamu da tsautsayin ne a kokarin ladabtar da yaran shagonsa.

An ce saɓanin ya samo asali ne bayan da, Abdul'aziz, ya zargi yaron da sauran yaran shagon da yi masa sata, lamarin da ya sa cikin ɓacin rai yace ya kori yaran nasa.

Ana jimamin mutuwar ango a Gombe
Taswirar jihar Gombe da ke Arewa maso Gabas. Hoto: Legit.
Source: Original

Yadda yaro ya hallaka mai gidansa a Gombe

Rahoton Progress Radio ya ce cikin fushi ya kori yaran, amma rikicin ya ƙara muni bayan sun yi masa rashin kunya, lamarin da ya kai ga amfani da makami.

A yayin rikicin, wasu shaidun gani da ido sun ce yaran sun fara masa rashin kunya, kuma a lokacin da ya yi yunƙura zai daki ɗaya daga cikinsu, sai yaron shagon ya jawo almakashi ya caka masa.

Kara karanta wannan

Ta'addanci: 'Yan bindida 80 sun mika wuya, gwamnati ta gindaya sharuda

Marigayin ya samu mummunan rauni inda aka yi ƙoƙarin kai shi asibiti domin ceto rayuwarsa, amma abin ya ci tura, kamar yadda shaidu suka bayyana.

An garzaya da Dan Malam asibiti sakamakon mummunan rauni, amma ya rasu, lamarin da ya girgiza jama’a makonni kaɗan bayan aurensa.

An ce za a gudanar da jana’izar marigayin a yau Lahadi 18 ga watan Janairun 2026 da misalin ƙarfe 11:00 na safe a Masallacin Juma’a na Bolari da ke cikin garin Gombe.

Kawo yanzu dai, rundunar yan sanda da kuma Gwamnati ba su fitar da wata sanarwa a hukumance dangane da faruwar lamarin ba.

An hallaka mata da 'ya'yanta 6 a Kano

An ji cewa wasu miyagu da ba a gano ko su waye ba sun shiga har gida, sun kashe matar aure da 'ya'yanta uku a cikin birnin Kano.

Wannan mummunan al'amari ya auku ne a unguwar Dorayi Chiranci, kuma an ce maharan sun jefa karamin jaririn matar a cikin rijiya.

Duk da babu wata sanarwa a hukumance daga rundunar yan sanda, amma mazauna Dorayi sun ce lamarin ya tada masu hankali matuka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.