Pantami Ya Yi Mamakin Kisan Gilla da Tsakar Rana a Kano, Ya Yi Masu Mummunar Addu'a
- Tsohon minista Farfesa Isa Pantami ya nuna alhini kan kisan gillar yan gida daya mutum bakwai da aka yi da tsakar rana a Kano
- Pantami ya ce kisan ya nuna ƙarshen rashin imani, yana addu'ar ga Allah ya hukunta maharan idan ba masu shiryuwa ba ne
- Malamin ya yi addu’a ga yaran da mahaifiyarsu, yana roƙon Allah ya saka musu Aljanna tare da bai wa iyalansu haƙuri
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Tsohon minista a Najeriya, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami ya yi magana game da kisan gillar da aka yi wa iyali a Kano.
Sheikh Pantami ya nuna damuwa matuka tare da alhinin abin da ya faru bayan wasu miyagu sun shiga gida da tsakar rana suka hallaka mutane bakwai.

Source: Facebook
Legit Hausa ta samu wannan bayani ne daga shafin malamin wanda ya wallafa a Facebook da safiyar yau Lahadi 18 ga watan Janairun 2026.

Kara karanta wannan
Tashin hankali: An yi wa wata matar aure da 'ya'yanta 3 kisan rashin Imani a Kano
Yadda aka hallaka iyali gaba daya a Kano
Idan ba ku manta ba, mun kawo musu labarin yadda wasu da ba a san ko su waye ba, sun shiga gidan da rana suka yi musu kisan gilla.
Tsageru da har yanzu ba a gano ko su waye ba sun shiga har gida, sun kashe matar aure da 'ya'yanta shida a cikin birnin Kano.
Wannan mummunan al'amari ya auku ne a unguwar Dorayi Chiranci, kuma an ce maharan sun jefa karamin jaririn matar a cikin rijiya.
Duk da babu wata sanarwa a hukumance daga rundunar yan sanda, amma mazauna Dorayi sun ce lamarin ya tada masu hankali matuka.

Source: Original
Martanin Pantami kan kisan gilla a Kano
Sheikh Pantami ya bayyana kaduwarsa game da kisan gillar inda ya ce wannan lamari ya nuna karshen rashin imani kenan.
Ya ce akwai abin mamaki da rashin imani wanda ya kai iyaka, a ce an kashe mutane bakwai da tsakar rana a Kano kuma a Arewa.

Kara karanta wannan
Bashir Ahmad ya soki Abba Kabir kan tsawaita maganar zuwa APC, ya fadi illar dambarwar
Tsohon ministan ya yi addu'ar shiriya ga wadanda suka aikata hakan, inda ya ce idan ba ma su shiryuwa ba ne Allah ya ya yi musu mummunan sakamako.
Ya ce:
"Inna lil Laahi wa inna ilaiHi Raaji'un!
"Lallai rashin imani da lalacewa sun kai iyaka. A kashe mutum 7 ko kusan haka da rana a cikin garin Kano? Arewa? Allah Shi kyauta.
"Ya Allah, duk wadanda suka yi wannan mummunan aiki, na kashe wadandan yara tare da mahaifiyarsu, idan ba masu shiryuwa ba ne, Allah ka musu mummunan sakamako irin na wanda ya kashe muminai."
Tsohon ministan ya yi addu'a ga yaran da aka hallaka da kuma mahaifiyarsu yana fatan Ubangiji ya saka musu da gidan aljanna.
Ya bayyana bakin cikinsa kan abin da ya faru tare da zubar da hawaye inda ya ba iyalan mamatan hakuri kan wannan babban rashi da suka yi.
An tsinci gawarwakin yan gida daya a Rivers
A wani labarin, 'yan sanda sun ciro gawarwakin mutane shida 'yan gida daya da suka mutu bayan sun kwanta barci a Rivers.
Rundunar 'yan sandan jihar ta bayyana cewa binciken farko ya nuna cewa hayakin janareta ne ya yi ajalin mutanen.
Kwamishinan 'yan sandan Ribas ya ja hankalin mutane su guji kunna janareta a wuraren da suke kwanciya barci don kauce wa matsala.
Asali: Legit.ng