Kano Ta Yi Babban Rashi, Attajiri kuma Tsohon Shugaban Kasuwar Kwari Ya Rasu
- Sanata Barau Jibrin ya yi jimamin rasuwar fitaccen ɗan kasuwar Kano wanda ya rasu bayan fama da jinya na wani lokaci
- Barau ya ce marigayin ya kasance abin koyi wanda ya jagoranci Kasuwar Kantin Kwari da shugabanci nagari da inganta kasuwanci
- Mataimakin shugaban majalisar dattawan ya miƙa ta’aziyya ga iyalan marigayin da ’yan kasuwa, yana roƙon Allah ya gafarta masa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin ya yi jimamin rasuwar babban dan kasuwa a jihar Kano.
Barau ya nuna bakin cikinsa kan rashin attajirin wanda shi ne shugaban kasuwar Kwari, Dr. Bature Abdulaziz MON.

Source: Facebook
Barau ya kadu bayan mutuwar dan kasuwa
Sanatan ya bayyana haka ne a yammacin yau Asabar 17 ga watan Janairun shekarar 2026 da muke ciki a shafin X wanda wakilin Legit Hausa ya leko.
Barau ya nuna jimami bisa rashin dattijon da aka yi a Kano inda ya ce marigayin na daya daga cikin fitattun yan kasuwa.
Ya ce a lokacin da ya kasance shugaban kasuwar Kwari ya ba da gudunmawa sosai tare da yin shugabanci nagari da kuma inagnta kasuwanci.
Sanarwar ta ce:
"Inna Lillahi wa Inna Ilaihi Raji’un.
"Ina jimamin rasuwar Dr. Bature Abdulaziz, MON, ɗaya daga cikin fitattun ’yan kasuwa a Jihar Kano, wanda ya rasu a yau bayan fama da jinya.
"Ba kawai ɗan kasuwa mai nasara ba ne, har ila yau wata babbar cibiya ce ta kansa, a lokacin da ya kasance shugaban Kasuwar Kantin Kwari, ya nuna shugabanci nagari da ya ƙarfafa kasuwanci, ya samar da dama ga dubban ’yan kasuwa, tare da ƙara ɗaukaka matsayin Kano a matsayin cibiyar kasuwanci a Najeriya."

Source: Original
Barau ya yaba da halayen marigayi Bature
Sanata Barau ya yaba da halayen marigayin inda ya ce Dr. Bature ya kasance abin koyi ga mutanen jihar da yan kasuwar Kano.
Ya mika ta'aziyyarsa ga iyalan marigayin, shugabannin kasuwar Kwari, kungiyar yan kasuwa da sauran al'umma.

Kara karanta wannan
CAN ta yi jimamin rasuwar malamin Musulunci da ya ceci Kiristoci a Rikicin Plateau
Ya ce:
"Marigayi Dr. Bature ya kasance abin koyi kuma fitaccen jigo a al’ummar ’yan kasuwar Kano.
"Ina miƙa ta’aziyyata ga iyalansa, shugabanci da ’yan Kasuwar Kantin Kwari, Ƙungiyar ’Yan Kasuwa ta Najeriya, da dukkan al’ummar ’yan kasuwa a Kano gaba daya.
"Allah Maɗaukakin Sarki (SWT) ya gafarta masa kura-kuransa, ya karɓi kyawawan ayyukansa, ya sanya shi a Aljannatul Firdaus. Allah ya ba iyalansa, abokan kasuwancinsa da dukkan al’ummar ’yan kasuwar Kano juriyar wannan babban rashi."
An ce za a yi jana'izar marigayin a yau Lahadi 18 ga watan Janairun 2026 da misalin karfe 10:00 na safe a gidansa dake Unguwar 'Yankaba.
Sanata Barau ya yi jimamin mutuwar Sanata
Kun ji cewa mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya yi jimamin rasuwar Sanata Godiya Akwashiki.
Barau ya bayyana marigayin a matsayin jajirtacce, amintaccen ɗan majalisa da ya yi aiki tuƙuru wajen bunƙasa rayuwar al’ummar.
Sanata Akwashiki, wanda aka fara zaɓen sa a shekarar 2019, ya sake samun nasara bayan sake zaɓe a zaben 2023, ya rasu yana da shekaru 52 a duniya.
Asali: Legit.ng
