Bola Tinubu Ya Dawo Najeriya bayan Makonni 3, Ya Samo Abin da Zai Amfani 'Yan Najeriya
- Bayan makonni uku a kasashen ketare, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya dawo Najeriya yau Asabar, 17 ga watan Janairu, 2025
- Fadar shugaban kasa ta ce Tinubu ya dawo ne bayan halartar taron ADSW 2026 a birnin Abu Dhabi da ke Hadaddiyar Daular Larabawa
- Najeriya ta rattaba hannu kan Yarjejeniyar Haɗin Gwiwar Tattalin Arziƙi (CEPA) da UAE, wadda aka ce za ta ƙarfafa alaƙar kasashen biyu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya dawo gida Najeriya bayan shafe makonni uku ba ya kasar.
A wannan tafiya da Tinubu ya yi, ya samu halartar Taron Dorewar Ci Gaba a Abu Dhabi na shekarar 2026 (ADSW 2026) wanda aka gudanar a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE).

Source: Twitter
Mai magana da yawun Shugaban Ƙasa, Bayo Onanuga, ne ya tabbatar da dawowar Bola Tinubua cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar a Abuja, in ji Daily Trust.
Onanuga ya ce shugaban kasar ya halarci taron tare da wasu mambobin majalisar zartarwa ta tarayya watau FEC.
Tinubu ya sa hannu a yarjejeniya da UAE
A gefen taron, Najeriya ta rattaba hannu kan Yarjejeniyar Haɗin Gwiwar Tattalin Arziƙi (CEPA) da ƙasar UAE, wadda aka ce za ta ƙarfafa alaƙar tattalin arziƙi tsakanin ƙasashen biyu.
Yarjejeniyar na da nufin bunƙasa cinikayya da zuba jari tsakanin Najeriya da Hadaddiyar Daular Larabawa, tare da ƙarfafa fannin fasaha da ilimi.
Haka kuma, za ta faɗaɗa haɗin gwiwa a muhimman fannoni kamar makamashi, gine-gine, noma, hakar ma’adinai da harkokin fasahar zamani, cewar The Nation.
Najeriya za ta karbi bakuncin taro
A jawabinsa a wajen taron, Shugaba Tinubu ya sanar da cewa Najeriya da UAE za su haɗa kai wajen karɓar baƙuncin taron INVESTOPIA a birnin Lagos a watan Fabrairu.
Ya ce taron, wani shiri ne na jawo hankalin masu zuba jari daga sassa daban-daban na duniya domin bunƙasa zuba jari mai dorewa a Najeriya.
Shugaban Ƙasar ya kuma bayyana cewa Najeriya na da burin tara kimanin Dala biliyan 30 a duk shekara domin ayyukan kare muhalli da bunƙasa masana’antu masu amfani da makamashi mai tsafta.

Source: Twitter
A cewarsa, kuɗaɗen za su taimaka wajen sauya tsarin makamashi da kuma faɗaɗa wutar lantarki a faɗin ƙasar.
Tun da farko dai, Shugaba Tinubu ya bar Najeriya ne a ranar 28 ga Disamba, 2025, zuwa abin da hadimansa suka bayyana a matsayin hutun ƙarshen shekara, kafin daga bisani ya halarci taron na Abu Dhabi.
Shettima ya tafi kasar Guinea-Conakry
A wani labarin, kun ji cewa Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya bar babbar birnin tarayya Abuja zuwa kasar Guinea-Conakry da ke Yammacin Afrika.
Kashim Shettima ya yi wannan tafiya ne domin wakiltar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a bikin rantsar da shugaban kasar Guinea-Conakry, Mamadi Doumbouya.
Har ila yau, ana sa ran mataimakin shugaban kasar zai halarci taron shekara-shekara karo na 56 kungiyar World Economic Forum (WEF) da za a gudanar a Davos, Switzerland.
Asali: Legit.ng


