Sanata Ya Mutu a Najeriya, Barau Ya Yi Jawabin Jan Hankali yayin Jana’izarsa

Sanata Ya Mutu a Najeriya, Barau Ya Yi Jawabin Jan Hankali yayin Jana’izarsa

  • Manyan 'yan siyasa a Najeriya sun halarci bikin jana'izar Sanata a Najeriya da ya riga mu gidan gaskiya a kasar India
  • Shugaban majalisar dattawa da mataimakinsa da tsofaffin gwamnoni sun halarci jana'izar da aka yi a jihar Nasarawa
  • Gwamna Abdullahi Sule ya yi kira ga shugabanni da jama’a su rungumi zaman lafiya, gafara da haɗin kai domin cigaban jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Lafia, Nasarawa - An gudanar da jana'izar marigayi Sanata Godiya Akwashiki daga jihar Nasarawa a Najeriya.

Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya ta 10, Sanata Godswill Akpabio, tare da Mataimakin Shugaban Majalisar, Sanata Barau Jibrin sun halarci jana'izar.

Sanata Barau ya yi jawabi yayin jana'izar sanata
Sanata Barau Jibrin da Godiya Akwashiki. Hoto: Barau I Jibrin.
Source: Twitter

An yi jana'izar marigayi Sanata a Nasarawa

Rahoton Punch ya ce Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule na daga cikin bakin da suka samu zuwa jana’izar marigayi Sanata Godiya Akwashiki a Lafia.

Kara karanta wannan

Rai bakon duniya: An yi jana'izar Sanata bayan ya rasu a asibitin kasar India

An gudanar da jana’izar ne a Cocin St. Williams Catholic Cathedral da ke birnin, inda manyan shugabanni daga sassa daban-daban na ƙasar suka halarta.

Cikinsu akwai tsohon gwamnan Nasarawa, Tanko Al-Makura, Gwamnan Plateau, Caleb Mutfwang, da Shugaban marasa rinjaye a Majalisar Dattawa, Abba Moro.

Da yake jawabi a madadin Majalisar Ɗinkin Tarayya, Sanata Barau Jibrin ya bayyana cewa marigayi Akwashiki ya rasu a ranar 31 ga Disamba, 2025.

Ya ce dan majalisar ya mutu a wani asibiti a India yana da shekaru 52, ya kwatanta shi a matsayin mai kishin ƙasa na gaske kuma jajirtaccen shugaba.

Barau ya ce Majalisar Dattawa ta yi babban rashi sakamakon mutuwar Akwashiki, yana mai jaddada gudunmawarsa wajen inganta dokoki da hidimar ƙasa mai inganci.

Gwamna Sule ya ja hankalin shugabanni a jana'iza
Gwamna Sule Abdullahi na jihar Nasarawa. Hoto: Abdullahi Sule Mandate.
Source: Facebook

Jan hankali da Gwamna Sule ya yi

A nasa jawabin, Gwamna Abdullahi Sule ya yi kira ga shugabannin siyasa, addini da al’umma da su rungumi juna duk da bambance-bambancen ra’ayi, domin haɗin kai da cigaban Jihar Nasarawa da Najeriya baki ɗaya.

Gwamnan ya bukaci jama’a su fifita zaman lafiya da jituwa, tare da kira ga ’yan siyasa da su yafe wa juna kura-kurensu, yana mai cewa mutuwa ba ta barin kowa a baya.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya turo sako daga kasar waje kan rasuwar malamin Musulunci a Najeriya

A cikin hudubar jana’izar, Bishop Matthew Ishaya Audu na cocin Jos ya bayyana marigayi Akwashiki a matsayin Kirista na gaskiya, ɗan siyasa na ƙasa da jama’a, tare da tunatar da jama’a cewa rayuwa mai mutunci ita ce ginshiƙin shugabanci nagari.

Marigayi Sanata Godiya Akwashiki ya wakiltci Mazabar Nasarawa ta Arewa a Majalisar Dattawa ta 9 da ta 10, ya shugabanci kwamitoci da dama ciki har da na Rundunar Sojin Sama da Harkokin Yada Labarai.

Sanata a Najeriya ya bar duniya

Kun ji cewa Najeriya ta yi babban rashi bayan da aka sanar da mutuwar sanata mai ci wanda ya bar duniya bayan fama da jinya.

Sanata Okey Ezea daga Enugu ta Arewa ya rasu a Birtaniya lamarin da ya girgiza jam’iyyar LP da mutanen yankinsa.

Ezea shi ne ɗan majalisa guda kaɗai da ya ragewa LP daga Enugu, abin da ya sa rashin nasa ya fi ɗaga hankalin jama’a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.