Rai Bakon Duniya: An Yi Jana'izar Sanata bayan Ya Rasu a Asibitin Kasar India
- An yi jana'iza tare da birne marigayi sanatan Nasarawa ta Arewa, Godiya Akwashiki a gidansa da ke birnin Lafiya yau Asabar
- Sanata Godiya Akwashiki ya rasu ne bayan fama da jinya a wani asibiti a kasar Indiya, yana da shekaru 52 da haihuwa
- Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, wanda ya halarci jana'izar, ya ce rasuwar Sanatan babban rashi ne ga Najeriya baki daya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Nasarawa, Nigeria - An yi jana'izar Sanata Godiya Akwashiki (SDP, Nasarawa ta Arewa) a gidansa da ke birnin Lafia, inda iyalai, abokan aiki da manyan ’yan siyasa suka yi masa bankwana.
Sanata Akwashiki ya rasu ne a ranar 31 ga Disamba, 2025, yana da shekaru 52, bayan fama da doguwar jinya a wani asibiti a ƙasar Indiya.

Source: Twitter
An birne Sanatan Nasarawa a gidansa
Daily Trust ta rahoto cewa an yi jana’izarsa da misalin karfe 1:50 na rana yau Asabar, bayan gudanar da taron addu'o'i a Cocin St. William Cathedral da ke Lafia, kafin a birne shi a harabar gidansu.
Marigayin, wanda aka haife shi a Angba Iggah da ke ƙaramar hukumar Nasarawa Eggon ta Jihar Nasarawa, ya fara zama Sanata a shekarar 2019, sannan aka sake zaɓarsa a 2023.
Kafin haka, ya taba zama ɗan Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa, inda ya riƙe muƙamin shugaban masu rinjaye, sannan daga bisani ya zama Mataimakin Kakakin Majalisar.
Gwamna Sule ya yi alhinin Akwashiki
Da yake jawabi a wajen jana’izar, Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya bayyana marigayin a matsayin jagora mai sadaukarwa, wanda ya ba da rayuwarsa wajen bautar Allah da yi wa al’umma hidima.
“Mun hallara a nan ne domin yi wa Sanata Godiya Akwashiki bankwana na ƙarshe, mutuwa tana tunatar da mu, mu kasance masu tawali’u da ƙaunar juna,” in ji Gwamna Sule.
Ya yi addu’ar Allah ya ba iyalansa, al’ummar Eggon da kuma ƙasar baki ɗaya haƙurin jure wannan babban rashi, tare da kira ga ’yan Najeriya da su rungumi yafiya domin ci gaban ƙasa.

Source: Twitter
Sanata Barau ya wakilci Akpabio
A nasa jawabin, Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, wanda Mataimakin Shugaban Majalisar, Sanata Barau Jibrin, ya wakilta, ya ce Najeriya ta yi babban rashi.
“Mun rasa ɗan’uwa, aboki kuma abokin aiki wanda ya bayar da gagarumar gudummawa ga ci gaban jama'a a mazabarsa da ƙasa baki ɗaya,” in ji Barau.
Sanata Barau ya yi addu’ar Allah ya ba iyalansa, Nasarawa ta Arewa da Najeriya juriyar wannan rashi da ba za a iya maye gurbinsa ba, kamar yadda Vanguard ta rahoto.
Za a yi janazar mataimakin gwamnan Bayelsa
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin jihar Bayelsa ta kammala shirye-shiryen jana'izar mataimakin gwamna, Mr Lawrence Ewhrudjakpo.
A ranar Alhamis, 11 ga watan Disamba, 2025, Ewhrudjakpo ya yanke jiki ya fadi a ofishinsa da ke cikin gidan gwamnatin Bayelsa , inda aka garzaya da shi asibitin tarayya (FMC) amma rai ya yi halinsa.
Gwamna Douye Diri, ya sanar da cewa za a gudanar da jana'izar tsohon mataimakinsa, Marigayi Lawrence Ewhrudjakpo, a ranar 30 ga watan Janairu, 2026.
Asali: Legit.ng

