Da Gaske Harkokin Gwamnati Sun Tsaya Cak a Kano Abba na Shirin Shiga APC?

Da Gaske Harkokin Gwamnati Sun Tsaya Cak a Kano Abba na Shirin Shiga APC?

  • Gwamnatin Jihar Kano ta ce ikirarin da ke yawo na cewa wani umarni daga gwamna ya hana tafiyar da harkokin mulki ba shi da tushe
  • Ta bayyana cewa umarnin dakatar da mika sababbin fayal ya shafi wani yanayi na sauyin kasafin kudi ne kawai ba tsayar da harkoki ba
  • Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta ta jaddada cewa muhimman ayyuka sun ci gaba da gudana ba tare da tangarda ba a dukkan sassan Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Gwamnatin Jihar Kano ta mayar da martani kan rahotannin da ke cewa wani sabon umarni daga Gwamna Abba Kabir Yusuf ya durkusar da harkokin mulki a jihar.

A wata sanarwa da ta fitar a ranar Asabar 17 ga Janairun 2026, ta bayyana ikirarin a matsayin kuskure domin kawo ruɗani a jihar.

Kara karanta wannan

Gwamna ya sayo dankara dankaran motoci 65 na alfarma, ya rabawa sarakuna

Abba Kabir Yusuf
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf. Hoto: Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Hadimin Abba Kabir Yusuf, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya wallafa a Facebook cewa an bayar da umarnin ne a karshen watan Disamban 2025 a daidai lokacin da kasafin kudin shekarar ya ke dab da karewa.

Umarnin da Abba Kabir ya bayar a Kano

A cikin sanarwar, gwamnatin ta bayyana cewa umarnin da gwamnan ya bayar ya bukaci ma’aikatun gwamnati, hukumomi da sassa na gwamnati su dakatar da mika sababbin fayal zuwa ofishinsa na wani dan lokaci.

Daily Trust ta rahoto ta ce wannan mataki ba sabon abu ba ne a harkokin kudi na gwamnati, musamman idan babu cikakken kasafi kudi da ya ke aiki.

Gwamnatin ta ce manufar umarnin ita ce kare jihar daga fitar da kudi ba bisa ka’ida ba, inda ta jaddada cewa a ka’idar tafiyar da kudin gwamnati ba a amincewa da kashe kudi idan babu kasafin da ya ke aiki.

Harkokin gwamnati sun tsaya cak a Kano?

Kara karanta wannan

Mutanen kauyuka za su kaura domin luguden wuta kan 'yan bindiga a dazuka

Sanarwar ta bayyana cewa sabanin ikirarin da ake yadawa, harkokin gwamnati sun ci gaba da tafiya ba tare da katsewa ba a Kano.

Kano ta ce ayyuka masu muhimmanci kamar tsaro, lafiya, ilimi, da sauran bangarori sun ci gaba da tafiya bisa tanade-tanaden doka.

An ce umarnin bai shafi ayyukan yau da kullum ba, illa kawai ya dakatar da kai sababbin batutuwan da ke bukatar amincewar gwamna, har sai an fitar da umarnin da ya dace da sabon tsarin kasafin kudi.

Gwamnatin Kano ta ce matakin ya kara karfafa tsarin shugabanci na hukumomi, ta hanyar barin kowace hukuma ta yi aiki cikin iyakar ikon da doka ta ba ta.

Ta bayyana rashin jin dadinta kan yadda aka fassara wannan mataki a matsayin durkusar da mulki, tana mai cewa a maimakon haka, matakin na nuna hangen nesa, ladabi da mutunta doka.

Gwamna Abba Kabir Yusuf
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf a wani taro. Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

'Yan APC sun gargadi Abba Kabir

A wani rahoton, kun ji cewa wasu 'yan jam'iyyar APC da NNPP sun yi magana game da dambarwar siyasar da ake yi a jihar Kano.

Kara karanta wannan

An dakatar da likitoci kan barin almakashi a cikin matar aure yayin tiyata a Kano

Wasu 'yan APC kamar Abdulmajid Dan Bilki Kwamanda sun gargadi gwamna Abba Kabir Yusuf da ya tsaya wajen mai gidansa, Rabiu Kwankwaso.

Dan Bilki Kwamanda ya bayyana cewa ko da gwamnan ya koma APC ba za su yarda su ba shi takara kai tsaye ba a 2027 sai an yi zaben fitar da gwani.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng