Gwamna Ya Kori Hadiminsa, an Cafke Shi yayin da Ake Ci Gaba da Bincike

Gwamna Ya Kori Hadiminsa, an Cafke Shi yayin da Ake Ci Gaba da Bincike

  • Gwamnan jihar Edo, Sanata Monday Okpebholo, ya dauki matakin sallamar daya daga cikin masu ba shi shawara ta musamman daga mukaminsa
  • Sanata Mpnday Okpebholo ya kori mai ba shi shawara ta musamman kan wayar da kan matasa, Aigbobun Collins bayan gudanar da wata zanga-zanga
  • Gwamnan ya kuma maye gurbinsa da wanda zai ci gaba da ba shi shawara kan harkokin wayar da kan jama'a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Edo - Gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo, ya sallami mai ba shi shawara na musamman kan harkokin wayar da kan matasa, Aigbogun Collins.

Gwamna Okpebholo ya kuma amince da nadin wanda zai maye gurbin Aigbogin Collins bayan korar da aka yi masa.

Gwamnan jihar Edo ya kori hadiminsa
Gwamnan jihar Edo, Sanata Monday Okpebholo Hoto: @makpakomiza
Source: Twitter

Jaridar The Nation ta ce ganin na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar Edo, Umar Musa Ikhilor, ya sanyawa hannu kuma aka rabawa manema labarai.

Kara karanta wannan

Bayan kashe mutane fiye da 40, Gwamna Bago ya fadi dalilin 'yan bindiga na farmakar Kasuwan Daji

Meyasa Gwamna Okpebholo ya kori hadiminsa?

Sallamar Aigbogun Collins na zuwa ne a daidai lokacin da ake gudanar da bincike kan zanga-zangar tashin hankali da aka yi kan garkuwa da mutane a Ekpoma, da ke Karamar hukumar Esan ya Yamma.

Zanga-zangar dai da aka gudanar a garin Ekpoma ta haifar da lalata kayayyaki da satar dukiya mai tarin yawa.

Aigbogun tsohon shugaban Karamar Hukumar Esan Yamma ne. An kama shi tare da yi masa tambayoyi dangane da zanga-zangar tashin hankalin da ta girgiza Ekpoma.

Majiyoyi sun ce an kama tsohon mai taimaka wa gwamnan ne bisa umarnin Gwamna Okpebholo na gudanar da bincike kan rikicin da ya auku.

An maye gurbinsa nan take

Gwamna Okpebholo ya kuma amince da naɗa Christopher Udobor Iyase a matsayin wanda zai maye gurbin Aigbogun Collins, rahoton da jaridar Daily Trust ta kawo ya tabbatar da hakan.

Sakataren gwamnatin jihar, Umar Musa Ikhilor, ya ce gwamnan ya amince da naɗa Christopher Udobor Iyase a matsayin sabon mai ba shi shawara na musamman kan wayar da kan matasa, inda zai karɓi muƙamin daga Collins.

Kara karanta wannan

An samu matsala a shirin ganawar gwamnan Kano da Tinubu kan batun komawa APC

Gwamna Okpebholo ya nada sabon mai ba shi shawara na musamman
Gwamna Monday Okpebholo na jawabi a wajen taro Hoto: Sen Monday Okpebholo
Source: Twitter

Ya bayyana Iyase a matsayin jajirtaccen mai wayar da kan matasa, wanda ke da matuƙar ƙwazo da burin ganin an kula da jin daɗi da walwalar matasan jihar Edo baki ɗaya.

“Iyase kwararren mai wayar da kan matasa ne, wanda yake da son walwalar matasan jihar Edo. Yana da digiri a fannin gudanar da harkokin jama’a daga jami’ar Benin."

- Umar Musa Ikhilor

Gwamna Okpebholo ya biya albashin watan 13

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Edo, Sanata Monday Okpebholo, ya faranta ran ma'aikata bayan biyan su albashin watan 13.

Babban sakataren yaɗa labarai na gwamnan, Mista Patrick Ebojele, ya ce Okpebholo ya ƙaddamar da wannan tsarin na biyan albashin wata 13 makonni kaɗan bayan rantsar da shi a matsayin gwamna a watan Nuwamba 2024.

Hadimin gwamnan, ya ce Okpebholo ya kuma ci gaba da hakan a shekarar 2025 domin rage wa ma'aikata raɗaɗin hidimomin karshen shekara da shiga.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng