Shugaba Tinubu Ya Turo Sako daga Kasar Waje kan Rasuwar Malamin Musulunci a Najeriya
- Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya aiko da sakon ta'aziyya daga kasar waje bisa rasuwar malamin addinin musulunci, Imam Abubakar
- Malamin ya shahara ne bayan taimakon da ya yi wa wasu kiristoci fiye da 260 a lokacin fadan addinin da ya faru a jihar Filato a shekarun baya
- Bola Tinubu ya bukaci malaman addini da sauran 'yan Najeriya su yi koyi da marigayin, wanda ya rungumi zaman lafiya fiye da kabilanci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana alhini da jimami kan rasuwar Malam Abdullahi Abubakar, Babban Limamin ƙauyen Nghar da ke ƙaramar hukumar Barkin Ladi a Jihar Filato.
Marigayi Imam Abubakar, malamin addinin Musulunci kuma limamin masallacin Juma'a na kauyen Nghar, ya rasu yana da shekaru 92 a duniya.

Kara karanta wannan
Rai bakon duniya: Malamin Musulunci da ya ceci Kiristoci 260 a rikicin Plateau ya rasu

Source: Twitter
Duk da yana kasar waje, Shugaba Tinubu ya aiko da sakon ta'aziyyar rasuwar malamin a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga ya wallafa a shafin X.
Imam Abubakar ya shahara a ciki wajen Najeriya bayan da ya ɓoye tare da kare Kiristoci sama da 200 a shekarar 2018, a lokacin rikicin kabilanci da addini da ya girgiza Jihar Filato.
Shaidar da Tinubu ya yi wa Malam Abubakar
A cikin sanarwar da Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Juma’a, Shugaba Tinubu ya miƙa ta’aziyyarsa, inda ya bayyana marigayi limamin a matsayin malami na musamman.
Tinubu ya ce rayuwar marigayin ta kasance shaida ta gaskiya, jarumtaka da girmama rayuwar kowane ɗan Adam ba tare da duba addininsa ba.
“A lokacin da rikice-rikicen kabila da addini suka kusan rinjayar hankali da tunani, Imam Abubakar ya tsaya tsayin daka a kan hanyar zaman lafiya.
"Ko da yake rayuwarsa na cikin babbar barazana, wannan limami ya zaɓi kare rayuwar ɗan Adam fiye da nuna banbanci da ƙauna maimakon ƙiyayya.

Kara karanta wannan
Atiku ya yi martani da dansa ya sauya sheka zuwa APC, zai goyi bayan tazarcen Tinubu
"Wannan jarumtar tasa ta nuna ma’anar gaskiyar addini fiye da wa’azi, tare da aika saƙo mai ƙarfi ga duniya baki ɗaya. Imam Abubakar mutumkn kirki ne kuma abin koyi da ya kamata kowa ya yi ƙoƙarin zama kamarsa.”
- In ji Bola Ahmed Tinubu.

Source: Twitter
Tinubu ya nemi a yi koyi da Imam Abubakar
Shugaba Tinubu ya yi kira ga shugabannin addini da na al’umma da su yi koyi da rayuwar Imam Abubakar ta hanyar wa’azi da rayuwa bisa haƙuri, girmama juna da zaman lafiya.
“Allah Madaukakin Sarki Ya gafarta masa, Ya masa rahama, kuma Ya saka masa da alheri bisa kyawawan ayyukansa da jarumtakar da ya nuna,” in ji shugaban ƙasar.
Shugaban kasa ya yi alhinin mutuwar Lucia Onabanjo
A wani labarin, kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya yi alhini kan mutuwar uwargidan tsohon gwamnan jihar Ogun, Lucia Onabanjo, wacce ta rasu tana da shekaru 100 a duniya.
Shugaba Tinubu ya tura sakon ta'aziyya ga iyalai, abokai da masoyan marigayiyar, yana cewa rasuwarta babban rashi ne ga Jihar Ogun da kasa baki daya.
Ya bukaci gwamnatin Jihar Ogun da iyalan Onabanjo su daukaka tarihinta ta hanyar ci gaba da ayyukan tallafa wa matalauta da marasa galihu.
Asali: Legit.ng