Gwamna Bago Ya Ciri Tuta yayin da Babban Malamin Addini Ya Yi Magana kan 'Yan bindiga
- Bishof Isaac Idahosa ya bayyana goyon bayansa ga yunkurin Gwamna Mohammed Imaru Bago na dawo da zaman lafiya a jihar Neja
- Malamin addinin ya ce matakan da Gwamna Bago ke dauka sun cancanci a yaba masa, domin zai cimma nasara a yaki da matsalar tsafo
- Wannan yabo na fitaccen limamin cocin na zuwa ne a lokacin da Gwamna Bago ya dauki wasu matakai masu tsauri don tabbatar da tsaro
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Niger, Nigeria - Gwamna Mohammed Umaru Bago ya fara shan yabo daga malaman addini kan matakan da ake ganin yana dauka domin shawo kan matsalar tsaro a jihar Neja.
Wani fitaccen malamin addini a Najeriya, Bishof Isaac Idahosa, ya yaba wa Gwamna Bago bisa matakan da yake dauka, yana mai nuna cewa hakan na iya magance matsalar tsaro.

Source: Facebook
Jaridar Leadership ta ce Idahosa ya bayyana goyon bayansa ga Gwamna Umaru Bago, inda ya nuna kwarin gwiwa cewa gwamnan na da ƙwarewar da za ta ba shi damar magance matsalar rashin tsaro a Neja.
Wadanne matakai Gwamna Bago ya dauka?
Goyon bayan da malamin na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Bago ke fuskantar ƙaruwar hare-haren ta’addanci da sace-sacen mutane a Neja da yankin Arewa ta Tsakiya .
Gwamna Bago, wanda aka fi sani da “manomin gwamna,” ya ɗauki matakai masu tsauri domin shawo kan matsalolin tsaro, inda ya ayyana dokar ta-baci a wasu sassan Minna, tare da jaddada cewa ba zai yi sulhu da ’yan bindiga ba.
Haka kuma, kwanan nan gwamnan ya sanar da shirin ɗaukar mutane 10,000 aiki a rundunar tsaro ta Joint Task Force (JTF) domin ƙarfafa tsaro da dawo da zaman lafiya a jihar.
Malamin addini ya yabawa Gwamna Bago
Limamin cocin, Bishof Idahosa ya yabawa Gwamna Bago bisa abin da ya kira dabaru masu kyau da yake amfani da su wajen tunkarar kalubalen tsaro, inda ya ce:
“Daukar matakin bincike a wurin da matsala ke faruwa wata dabara ce mai matuƙar kyau. Kamar jiya ma, gwamnan ya je yankin Borgu domin ya ga abubuwa da idonsa. Gwamna ne da ke ɗaukar tsaron mutanensa da muhimmanci sosai.”

Source: Facebook
Malamin, wanda ya yi takarar mataimakin shugaban kasa a inuwar NNPP, ya nuna cikakken tabbaci cewa Gwamna Bago zai yi nasara kan ƙalubalen tsaron da ake fuskanta.
Bishof Idahosa ya kuma yabawa jajircewar gwamnan da ƙudurinsa na tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar Neja.
A cewarsa, gwamnan ya tsaya kan alkawurran da ya dauka naa kare rayuka da dukiyoyin al’umma tare da dawo da zaman lafiya a jihar duk da ƙalubalen da ake fuskanta a halin yanzu.
Bago ya gano dalilin kai hari kasuwa
A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Umaru Bago ya bayyana cewa akwai dalilin da ya sa 'yan bindigan suka kai hari Kasuwan Daji da ke karamar hukumar Borgu a jihar Neja.

Kara karanta wannan
Bayan kashe mutane fiye da 40, Gwamna Bago ya fadi dalilin 'yan bindiga na farmakar Kasuwan Daji
Gwamnan ya yi ikirarin cewa tun asali dama kasuwar ta yi kaurin suna wajen sayar da shanun sata, inda daga nan ne ma ta samo sunanta.
Ya ce bisa wannan dalili ne wata kungiyar ’yan bindiga mai gaba da wata ta kai hari kan kasuwar a makon da ya gabata, inda suka kashe mutane da dama.
Asali: Legit.ng

