Tinubu Bai Dawo ba, Jirgin Shettima Ya Shilla zuwa Kasashe 2

Tinubu Bai Dawo ba, Jirgin Shettima Ya Shilla zuwa Kasashe 2

  • Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya bar babbar birnin tarayya Abuja zuwa kasar Guinea-Conakry da ke Yammacin Afrika
  • Kashim Shettima zai wakilci Mai girma Bola Ahmed Tinubu a wajen bikin rantsar da shugaban kasar Guinea, Mamadi Doumbouya
  • Tafiyar Kashim Shettima dai na zuwa ne yayin da 'yan Najeriya ke ci gaba da dakon dawowar Shugaba Tinubu wanda ya bar kasar nan tun karshen shekarar 2025

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya tashi daga babban birnin tarayya Abuja zuwa kasar Guinea-Conakry.

Kashim Shettima ya tashi ne domin wakiltar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a bikin rantsar da shugaban kasar Guinea-Conakry, Mamadi Doumbouya.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC ta yi wa Atiku shagube bayan dansa ya ki binsa zuwa ADC

Kashim Shettima ya bar Najeriya zuwa kasashen waje
Kashim Shettima yayin da yake shiga cikin jirgin sama Hoto: @stanleynkwocha
Source: Twitter

Shettima ya bar Najeriya

Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yaɗa labarai da sadarwa, ofishin mataimakin shugaban kasa, Stanley Nkwocha, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na X ranar Juma’a, 16 ga watan Janairun 2026.

Har ila yau, ana sa ran mataimakin shugaban kasar zai halarci taron shekara-shekara karo na 56 kungiyar World Economic Forum (WEF) da za a gudanar a Davos, Switzerland, bayan kammala halartarsa a bikin rantsar da shugaban kasar ta yammacin Afirka.

Shettima zai je kasar Guinea

Nkwocha ya ce mataimakin shugaban kasar zai wakilci Shugaba Tinubu ne a bikin rantsar da Shugaba Doumbouya bayan nasararsa a zaɓe, inda aka shirya gudanar da bikin a ranar Asabar, 17 ga Janairu, a filin wasa na GLC da ke Nongo, birnin Conakry.

Kara karanta wannan

Atiku ya yi martani da dansa ya sauya sheka zuwa APC, zai goyi bayan tazarcen Tinubu

Ya kara da cewa, baya ga nuna haɗin kai na diflomasiyya, ziyarar na da nufin ƙarfafa huldar kasuwanci tsakanin kasashen biyu, musamman ganin yadda fitar da kayayyakin Najeriya zuwa Guinea, ciki har da kayan masana’antu da na noma, ya karu zuwa dala miliyan 3.29.

Jirgin Shettima zai je Switzerland

Daga Guinea, Shettima zai wuce Davos-Klosters na lasar Switzerland domin halartar taron shekara-shekara na 56 na World Economic Forum (WEF 2026), wanda za a gudanar daga ranar 19 zuwa 23 ga watan Janairu, 2026.

A yayin taron, mataimakin shugaban kasar zai gana da shugabannin duniya da masu zuba jari domin tattauna ajandar sauye-sauyen tattalin arzikin Najeriya, damar zuba jari, da rawar da Afirka ke takawa wajen gina makomar tattalin arzikin duniya mai ɗorewa da haɗin kai.

Kashim Shettima ya yi tafiya zuwa kasar waje
Kashim Shettima na gaisawa da sojojin Najeriya Hoto: @stanleynkwocha
Source: Twitter

Yaushe Shettima zai dawo?

Ana sa ran Shettima zai dawo Najeriya bayan kammala dukkan ayyukansa a birnin Davos.

Wannan ci gaba na zuwa ne a daidai lokacin da ’yan Najeriya ke jiran dawowar Shugaba Tinubu, wanda ya shafe wani lokaci a kasashen waje tun shekarar da ta wuce.

Shettima ya ja kunnen 'yan adawa

A wani labarin kuma, kun ji cewa mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya ja kunnen 'yan adawa kan tazarcen Mai girma Bola Tinubu a 2027.

Kara karanta wannan

Rasuwar Sarki mai martaba ta taba Bola Tinubu, ya mika ta'aziyya ga masarautar Badagry

Kashim Shettima ya ja gargadi 'yan adawa da kada su yi yunkurin kalubalantar Tinubu a zaɓen shugaban kasa na 2027 da ake tunkara.

Ya kuma yi gargaɗin cewa ba a cin zaɓe da hayaniyar kafafen sada zumunta, yana mai jaddada cewa nasara a zaɓe tana zuwa ne ta hanyar haɗin gwiwa mai karfi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng