'Yan Bindiga Sun Kori Mutanen Kauyuka a Sokoto? Gwamnati Ta Yi Bayani

'Yan Bindiga Sun Kori Mutanen Kauyuka a Sokoto? Gwamnati Ta Yi Bayani

  • An yada wani bidiyo mai ikirarin cewa 'yan bindiga sun tilastawa mutanen kauyen Tidibale da ke jihar Sokoto ficewa daga gidajensu
  • Gwamnatin jihar Sokoto ta ba da tabbacin cewa, tabbas mutanen da aka gani.a cikin bidiyon sun fito ne daga kauyen Tidibale na karamar hukumar Isa
  • Sai dai, ta bayyana cewa ba gaskiya ba ne abin da ake yayatawa cewa 'yan bindiga ne suka koro mutanen daga matsugunansu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Sokoto - Gwamnatin jihar Sokoto ta yi karin haske kan wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke nuna cewa 'yan bindiga sun kori mutane.

Bidiyon dai an yi ikirarin cewa mutanen da aka gani a cikinsa mazauna kauyen Tidibale ne da ’yan bindiga suka kora.

Gwamnatin Sokoto ta yi bayani kan barazanar 'yan bindiga
Gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu na jawabi a wajen taro Hoto: Ahmad Aliyu Sokoto
Source: Facebook

Jaridar The Guardian ta ce shugaban yada labarai da hulda da jama’a na fadar gwamnatin jihar Sokoto, Abubakar Bawa, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa.

Kara karanta wannan

Bayan kashe mutane fiye da 40, Gwamna Bago ya fadi dalilin 'yan bindiga na farmakar Kasuwan Daji

Wane bayani gwamnati ta yi?

Gwamnatin ta bayyana cewa mutanen da ke cikin bidiyon hakika mazauna kauyen Tidibale ne da ke karamar hukumar Isa.

Sai dai, ta bayyana cewa ba ’yan bindiga ne suka kore su daga gidajensu ba kamar yadda ake yayatawa, jaridar Vanguard ta kawo labarin.

Abubakar Bawa ya ce an kai mazauna kauyen zuwa hedkwatar karamar hukumar Isa na dan lokaci ne sakamakon rade-radin cewa ’yan bindiga na shirin kai hari a yankin.

An samu labarin harin 'yan bindiga

A cewarsa, bayan samun wannan bayani wanda ya jefa al’umma cikin fargaba da tashin hankali, kansilan da ke wakiltar mazabar, Dayyabu Sani, ya gaggauta kai rahoto ga shugaban karamar hukumar Isa, Alhaji Sherifu Kamarawa.

Daga nan ne shugaban karamar hukumar ya bayar da umarnin a kwashe mutanen kauyen zuwa hedkwatar karamar hukumar a matsayin matakin kariya.

Sanarwar ta ce daga bisani mutanen da abin ya shafa sun koma gidajensu na asali a kauyen Tidibale, yayin da hukumomin tsaro suka kara kaimi wajen sintiri a yankin domin hana duk wani yunkurin tayar da fitina daga masu aikata laifuffuka.

Kara karanta wannan

Katsina: Jigo a ADC ya bankado yadda aka ware kason 'yan bindiga a kasafin kudi

Wane mataki gwamnati ta dauka?

Domin kara tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi a kauyen Tidibale da al’ummomin da ke makwabtaka da shi, gwamnatin jihar Sokoto ta amince da kafa sansanin sojoji na Forward Operations Base (FOB), a yankin.

'Yan bindiga sun firgita mutane a jihar Sokoto
Taswirar jihar Sokoto, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Gwamnatin ta kuma bai wa al’ummar jihar, musamman mazauna yankunan da ke fama da matsalolin tsaro, tabbacin cewa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a a kowane lokaci.

“Gwamnati za ta ci gaba da yin aiki kafada da kafada da hukumomin tsaro na kasa, rundunar tsaron Sokoto da kuma kungiyoyin sa-kai domin kare al’ummomin karkara a fadin jihar."

- Abubakar Bawa

Yaran Bello Turji sun yi ta'asa a Sokoto

A wani labarin kuma, kun ji cewa yaran hatsabibin dan bindiva, Bello Turji, sun kai harin ta'addanci a jihar Sokoto.

Harin na 'yan bindiga da aka kai a kauyen Gajit da ke ƙaramar hukumar Sabon Birni, a gundumar Lajinge ta jihar Sokoto, ya yi sanadiyyar raunata mutum biyu.

Lamarin dai ya auku ne bayan wasu al'ummar jihar sun fara tserewa daga garuruwansu bayan samun sakon Bello Turji na kai musu hari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng