Gwamna Bago Ya Hau Mimbari a Katafaren Masallacin da aka Yi a Neja
- Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ya yaba wa Alhaji Mustapha Sani Bello bisa gina Masallacin Juma’a a birnin Minna
- Rahoto ya ce gwamnan ya ce aikin gina masallacin sadaka ce mai dorewa da za ta ci gaba da jawo albarka ga wanda ya assasa shi
- An bayyana cewaba sallah za a rika yi kawai a masallacin ba, mai kula da shi ya ce zai zamo cibiyar ilmantarwa da yada Musulunci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Neja – Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ya yabawa Alhaji Mustapha Sani Bello, wanda aka fi sani da Sani Basket, bisa kokarinsa na gina Masallacin Juma’a mai suna Masjidiul Huzaifa bn Yaman a yankin Shango da ke birnin Minna.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da ya kai ziyara domin duba aikin masallacin, inda ya nuna jin dadinsa da yadda aka gina masallacin cikin tsari da nagarta.

Source: Facebook
Legit Hausa ta tattaro bayanai game da sabon masallacin a cikin sakon da hadimin gwamnan jihar Neja, Balogi Ibrahim ya wallafa a Facebook.
Bago ya yaba da gina masallaci a Neja
A yayin ziyarar, Gwamna Umaru Bago ya bayyana cewa ya yi matukar farin ciki da inganci da kuma matakin da aka kai wajen gina Masjidiul Huzaifa bn Yaman.
Rahotanni sun ce gwamnan ya ce gina masallaci wata sadaka ce mai gudana wadda lada da albarkarta ba za su yankewa mai ita ba.
Tare da rakiyar jami'an tsaro, gwamna Umaru Bago ya zagaya sashe-sashe na masallacin har da hawa kan mimbarin da liman ke hububar sallar Juma'a.
Kira ga masu kula da masallacin
Umaru Bago ya yi kira ga shugabanni da masu kula da Masjidiul Huzaifa bn Yaman da su tabbatar da kula da masallacin yadda ya dace.
Ya ce kula da tsafta, tsari da kiyaye kayayyakin masallacin na da matukar muhimmanci domin ci gaba da amfanin da za a rika samu daga gare shi.
Manufofin masallacin ga al’umma
Da yake gabatar da bayani ga gwamnan, Sakataren Masjidiul Huzaifa bn Yaman, Ibrahim Adamu, ya bayyana cewa masallacin zai kasance wajen gudanar da sallar yau da kullum da kuma sallar Juma’a.
An bayyana cewa malam Ibrahim Adamu ya ce baya ga ibada, an shirya masallacin ya zama cibiyar al’umma inda za a bude wurin taro da koyarwa
A cewarsa, malamai masu ilimin addini za su rika taruwa a nan domin koyar da ilimin Musulunci da kuma taimakawa wajen yada fahimtar addini cikin hikima da natsuwa.
An bude sabon masallaci a jihar Bauchi
A wani labarin, kun ji cewa Sanata Shehu Buba ya bude katafaren masallacin juma'a a jihar Bauchi, inda malamai da dama suka hallara.
Rahotanni sun nuna cewa masallacin ya kunshi wajen ibada ga maza da mata da wajen karatu domin yada addinin Musulunci a jihar.
Malamai da sauran al'umma da suka halarci taron bude masallacin sun yaba wa Sanatan suna rokon Allah ya ba shi ladan aikin da ya yi.
Asali: Legit.ng

