Alhaji Aliko Dangote Ya Yi Kyautar Sama da Naira Biliyan 10

Alhaji Aliko Dangote Ya Yi Kyautar Sama da Naira Biliyan 10

  • Kamfanin simintin Dangote ya karrama manyan dillalansa da kyaututtuka na kusan Naira biliyan 15 domin yaba musu bisa jajircewar da suke yi
  • Aliko Dangote ya bayyana cewa dillalai ne ginshikin nasarar kamfanin wajen kai kayayyaki zuwa sassa daban-daban na Najeriya
  • Rahotannin sun nuna cewa kamfanin ya sanar da shirin fadada samar da siminti a Najeriya zuwa kusan tan miliyan 90 nan da shekarar 2030

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar LagosKamfanin simintin Dangote ya gudanar da bikin karrama manyan dillalansa da kwastomomi inda ya raba kyaututtuka da darajarsu ta kai kusan Naira biliyan 15.

An gudanar da bikin ne a Lagos, inda aka jaddada muhimmancin hadin gwiwa tsakanin kamfanin da dillalansa wajen cimma burin ci gaba a shekarar 2026 da ma gaba.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya ta kawo sabon tsari, masu amfani da banki za su fara biyan VAT

Wadanda Aliko Dangote ya ba kyautar biliyoyi
Aliko Dangote da wasu daga cikin wadanda suka samu kyautar da ya yi. Hoto: Dangote Industries
Source: Facebook

Legit Hausa ta tattaro bayanai game da yadda aka yi taron ne a wani sako da kamfanin Aliko Dangote ya wallafa a shafinsa na X.

Dangote ya raba kyautar biliyoyin Naira

Bikin karrama dillalan ya mayar da hankali kan wadanda suka fi nuna kwazo da bajinta a harkar rarraba simintin Dangote a fadin kasar.

Wadanda aka karrama sun samu kyaututtuka daban-daban da suka hada da kudi, kwantena na siminti, manyan motoci masu tsada irin su SUV, da kuma manyan motoci masu amfani da iskar gas ta CNG.

Dangote ya ce wadannan kyaututtuka wani bangare ne na nuna godiya ga jajircewa da hakurin da dillalan ke nunawa duk da kalubalen tattalin arziki..

Jawabin Aliko Dangote ga abokan hulda

A cikin jawabin da ya gabatar, Aliko Dangote ya yabawa dillalan a matsayin ginshikin kamfanin, yana mai cewa su ne ke tabbatar da cewa kayayyakin Dangote suna isa ga al’umma a kauyuka da birane.

Kara karanta wannan

ICPC ta gurfanar da mutumin El Rufai, ana zargin ya karkatar da biliyoyin Naira

Vanguard ta rahoto ya ce jajircewarsu a fagen aiki da kyakkyawar mu’amala da kwastomomi ne ke kara karfafa kamfanin a Najeriya.

wani da ya samu kyautar Aliko Dangote
'Yar Dangote na mika kyauta ga wani dilan siminti. Hoto: Dangote Industries
Source: Facebook

Shirin Dangote a shekarar 2030

Dangote ya yi amfani da damar wajen sake jaddada shirin sa na nan da 2030, wanda ke da burin mayar da kamfanin simintinsa mai darajar Dala biliyan 100 nan da shekarar 2030.

Ya bayyana cewa shirin ya ta’allaka ne kan fadada masana’antu, zuba jari a kasashen waje, da kuma gina wadataccen tsarin dogaro da kai a Afirka a fannoni kamar makamashi, kere-kere da abubuwan more rayuwa.

Dangote ya bayyana cewa yana shirin fadada karfin samar da siminti zuwa kusan tan miliyan 90 nan da shekarar 2030. Ya ce wannan adadi ya zarce rabin dukkanin simintin da kasar Saudiyya ke samarwa a halin yanzu.

Simintin Dangote ya fi araha a ketare

A wani labarin, mun kawo muku cewa attajirin Afrika, Alhaji Aliko Dangote ya yi bayani game da bambancin farashi da ake samu game da simintinsa a gida da waje.

Kara karanta wannan

Akwai matsala: Masana sun hango babban kalubale da Tinubu zai iya fuskanta a 2026

Rahotanni sun nuna cewa simintin da ake samarwa a Najeriya ya fi araha a kasashen waje duk da cewa sai an kashe kudin mota kafin a fita da shi.

A bayanin da dan kasuwar ya yi, Dangote ya ce akwai haraji kala-kala da ake daura wa kamfanoni a Najeriya, kuma hakan ne ya ke sanya kudin ya fi yawa a kasar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng