'Yan Sanda Sun Damke Bama Bamai da Miyagun Kwayoyi a Kano

'Yan Sanda Sun Damke Bama Bamai da Miyagun Kwayoyi a Kano

  • Jami’an ‘yan sanda a jihar Kano sun kama kayan fashe wa da miyagun kwayoyi a ayyuka biyu daban-daban a cikin birnin Kano
  • An gano buhunan kayan fashe wa da miyagun kwayoyi a Tudun Bojuwa da Sani Mainagge, yayin da jami’an leken asiri suka yi aiki bisa rahoton sirri
  • An kama wani direban babur mai kaya da ake zargi da safarar kayan fashe wa daga Jihar Nasarawa zuwa wasu wurare, inda ake ci gaba da bincike sosai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Kakakin rundunar ‘yan sanda ta Kano, CSP Abdullahi Kiyawa, ya bayyana cewa jami’an ‘yan sanda sun yi nasarar kama buhunan da ake zargin sun kunshi kayan fashe wa da miyagun kwayoyi.

Kara karanta wannan

Duk da ya samu digirin PhD, Sarki Sanusi II ya koma jami'ar Kano ya yi karatu

Ya ce a ranar Litinin, jami’an da ke caji ofis na Rijiyar Lemo bisa umarnin kwamishinan ‘yan sanda sun gudanar da bincike a gidan da ke Tudun Bojuwa, a karamar hukumar Fagge.

Yan sandan Kano sun kama kayan bama-bamai
Kwamishinan yan sandan Kano Ibrahim Bakori Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa
Source: Facebook

Wannan na kunshe a cikin wata sanarwa da Kakakin rundunar 'yan sanda, Abdullahi Kiyawa ya fitar a shafin Facebook, inda ya ce an samu buhuna biyu da ake zargin sun kunshi kayan laifi.

Kano: Yan sanda sun kama kayan fashe wa

CSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya kara da cewa kwararrun jami’an rundunar masu kula da kayan fashe wa sun tantance tare da gano abubuwan fashewa a buhunan.

Daya daga cikin buhunan ya kunshi abin tayar da bam guda shida, yayin da dayan ke dauke da fakitin ganyen hodar iblis guda 20 da kuma katina 220 na kwayar Exol.

Sanarwar ta kara da cewa jami’an yaki da 'yan daba na rundunar sun samu labarin sirri, har ta kai aka kama wani direban babur mai kaya a Sani Mainagge, a karamar hukumar Gwale.

An samu buhuna uku da ake zargin sun kunshi kayan fashe wa masu nauyi, daga ciki har da abubuwan tashin bama-bamai 3,700.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta gabatar da bukatar cafke Abdullahi Ganduje, kotu ta yi hukunci

Yan sandan Kano sun kama direba

An kama direban babur mai suna Ibrahim Garba, mai laƙabi da ‘Manyan Baki’, dan shekaru 49 daga Zamfara.

Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce an kama direba da ake zargi da safarar kayan
Kakakin yan sandan Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa
Source: Facebook

Bayan kama direban, ya amsa laifin safarar kayan daga Jihar Nasarawa zuwa wasu wurare. Kiyawa ya ce rundunar ta fara bincike mai zurfi a kan lamarin.

Kwamishinan ‘yan sanda, Ibrahim Bakori, ya yaba wa jami’an da suka gudanar da ayyukan, sannan ya bukaci al’umma da su kasance masu lura.

Ya yi kira ga jama’a da su ci gaba da bayar da rahoton duk wani abu ko motsi da ake zargi zuwa ofishin ‘yan sanda mafi kusa ko ta layukan gaggawa na rundunar.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Wani abu da ake zargin bam ne ya tarwatse da mutane a Adamawa

Yan sanda sun kama miyagun mutane

A baya, kun ji cewa rundunar ‘yan sandan Jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin Kwamishinan ‘yan sanda, CP Ibrahim Adamu Bakori, ta bayyana nasarorin tsaro da ta samu a shekarar 2025, inda ta kama mutane 3,081.

Rahoton ya nuna cewa rundunar ta ƙara bazawa da ɗaukar matakan tsaro a faɗin jihar domin murƙushe ayyukan ɓata-gari da ke barazana ga zaman lafiya da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a.

CP Bakori ya bayyana cewa tun daga ranar 17 ga watan Maris, 2025, lokacin da ya karɓi ragamar jagorancin rundunar, aka ƙaddamar da bincike na musamman domin gano manyan matsalolin tsaro da ke addabar jihar

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng