"Za Ku Fuskanci Hukunci": Gwamna Ya Gargadi Sarakuna kan Fulani Makiyaya
- Gwamnan jihar Bayelsa, Sanata Douye Diri, ya aika da sakon gargadi ga sarakunan gargajiya kan Fulani makiyaya
- Sanata Douye Diri ya bayyana cewa har yanzu dokar hana yawo da dabbobi domin kiwo na ci gaba da aiki a jihar Bayelsa
- Gwamnan ya kuma ja kunnen sarakunan gargajiya kan ba Fulani makiyaya filaye a cikin dazuzzukan da ke jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Bayelsa - Gwamnan Bayelsa, Sanata Douye Diri, ya gargadi sarakunan gargajiya a jihar da kada su rika bai wa makiyaya filaye a cikin dazuzzuka.
Gwamna Douye Diri ya bayyana cewa duk wanda aka kama yana aikata hakan za a hukunta shi.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust tace Gwamna Diri ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a wajen kaddamar da kakar noman rani ta shekarar 2025/2026 a gonar shinkafa mallakin gwamnatin jihar da ke al’ummar Otuasega a karamar hukumar Ogbia.

Kara karanta wannan
Bayan kashe mutane fiye da 40, Gwamna Bago ya fadi dalilin 'yan bindiga na farmakar Kasuwan Daji
Wane gargadi Gwamna Diri ya yi ga sarakuna?
Gwamna Diri ya ce wannan gargadi ya yi daidai da dokar hana yawo da dabbobi domin kiwo da ke aiki a jihar Bayelsa.
Kakakin gwamnan, Daniel Alabrah, ya ce Diri ya bayyana cewa makiyaya kan rika zagayawa da dabbobinsu suna lalata gonaki da amfanin gona, lamarin da ke hana karuwar samar da abinci a jihar.
“Dangane da batun makiyaya, ba sa zama a gonakinmu. Abin da ke faruwa shi ne suna zagayawa suna lalata amfanin gona."
“Bari na sake jaddadawa cewa dokar hana yawo da dabbobi domin kiwo a jihar nan na nan daram. Idan makiyaya sun lalata gonaki, ku tuntubi hukumomin tsaro, maimakon zuwa kafafen sada zumunta."
“Ina gargadin sarakunan gargajiya da ke bai wa makiyaya filaye a cikin dazuzzukanmu cewa duk wanda aka kama zai fuskanci hukunci. Dole ne Bayelsa ta kasance cikin aminci, kuma dole ne mu hada kai wajen tabbatar da tsaronta.”
- Gwamna Douye Diri

Kara karanta wannan
Gwamnan Kaduna ya hango abu mai kyau, ya ba 'yan Najeriya mafita kan dokar haraji
Za a ba manoma tallafi a jihar Bayelsa
Gwamna Diri ya kuma umurci kwamishinan noma da albarkatun kasa da ya tabbatar da karuwar samar da shinkafar da aka noma a Bayelsa kafin karshen shekarar 2026.
Hakazalika, ya sanar da ware Naira miliyan 200 a kowane wata domin tallafa wa manoma a jihar Bayelsa, rahoton jaridar The Sun ya tabbatar da hakan.
“Ga manomanmu, koyaushe za mu ci gaba da ba ku goyon baya. Ya mai girma kwamishina, ku gano manoma na gaskiya a jihar, kuma irin tallafin da nake bayarwa ga kananan ’yan kasuwa shi ma za a fara bai wa manoma."
"Don haka, daga yanzu za a rika ware Naira miliyan 200 a kowane wata domin tallafa wa manomanmu."
- Gwamna Douye Diri

Source: Facebook
Ya kuma bukaci ma’aikatan gwamnati da dukkan al’ummar Bayelsa da su rungumi harkar noma domin bunkasa tattalin arzikin jihar.
Gwamna ya umarci a binciki mutuwar mataimakinsa
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Bayelsa, Sanata Douye Diri, ya nuna alhininsa kan mutuwar mataimakinsa, Lawrence Ewhrudjakpo.
Gwamna Diri ya bayar da umarnin a gudanar da binciken gawa, domin gano musabbabin mutuwar mataimakin gwamnan na jihar Bayelsa.
Diri ya kuma yi Allah wadai da maganganun da ake yadawa a kan mutuwar mataimakin nasa, inda ya bayyana cewa bai kamata a siyasantar da lamarin ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
