EFCC ta Bude wa Tsohon Gwamna Yahaya Bello Aiki, Ta Kawo Hujjoji a Kansa a Kotu
- Hukumar EFCC ta sake gabatar da wasu muhimman bayanan banki a gaban kotun tarayya kan shari’ar tsohon gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello
- Shari’ar na ɗauke da tuhume-tuhume 16 da suka shafi cin amana da karkatar da kudi da ake zargin Yahaya Bello da suka kai Naira biliyan 110.4
- Shaidar banki ta bayyana wasu manyan kuɗi da aka biya ta wani asusu, amma ba a nuna takamaiman manufar wasu mu’amaloli da ka yi da su ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Ƙasa (EFCC) ta gabatar da ƙarin bayanan banki a shari’ar da take yi wa tsohon gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja.
Ana tuhumar Yahaya Bello tare da Umar Shuaibu Oricha da Abdulsalami Hudu da laifuffuka 16 da suka shafi karkatar da dukiyar jama’a da ake zargin sun kai kimanin Naira biliyan 110.4.

Source: Twitter
EFCC ta wallafa a Facebook cewa shari’ar ta ci gaba ne a gaban Mai Shari’a Maryanne Anineh, inda masu gabatar da ƙara suka sake kawo sabon shaida daga banki domin ƙarfafa tuhumar da ake yi wa waɗanda ake zargi.
Shaidar EFCC a kotu kan Yahaya Bello
A zaman shari’ar da aka ci gaba da ita, lauyan gwamnati kuma jagoran masu gabatar da ƙara, Kemi Pinheiro (SAN), ya gabatar da shaida ta shida (PW6), Mashelia Arhyel Bata, wanda jami'in Zenith Bank ne.
The Cable ta rahoto cewa an sake yi wa shaidar tambayoyi ne domin ƙarin bayani kan wasu takardun bayanan asusun banki da EFCC ta gabatar a zaman baya.
Lauyan mai kare Yahaya Bello da Umar Shuaibu Oricha, Joseph Daudu, ya mayar da hankali kan wata takarda da aka sanya wa suna ES1, wato bayanin asusun banki.
Bayanan da aka karanta a kotu
Shaidan ya bayyana wa kotu cewa bayanin asusun na ɗauke da ginshiƙai takwas, inda wani bangare na shi ke nuna bayanin abin da ya shafi kowace mu’amala.
Ya ja hankalin kotu kan wata mu’amala da aka yi a ranar 20, Janairu, 2016, wadda ta nuna biyan Naira miliyan 10 ta cak ga Abdulsalami Hudu.

Source: Twitter
Haka kuma, an ambaci wata mu’amala da ta nuna biyan N2,454,400 ga Halims Hotels and Tours da ke Lokoja. Sai dai shaidar ya ce ba zai iya faɗin manufar amfani da kudin ba, domin bayanin asusun bai nuna hakan ba.
Bayan kammala zaman, Mai Shari’a Maryanne Anineh ta ɗage shari’ar zuwa 16, Janairu, 2026, domin ci gaba da sauraron shaidu da muhawarar ɓangarorin da ke shari’ar.
Yahaya Bello zai yi takara a 2027
A wani rahoton, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya sanar da cewa zai nemi takarar Sanata a zaben shekarar 2027.
Yahaya Bello ya bayyana haka ne yayin ganawa da jama'a a wata masarauta da ya ziyarta tare da gwamnan Kogi, Usman Ododo.
Ana ganin cewa za a fafata a kan kujerar ganin cewa Sanata Natasha Akpoti da ke rike da kujerar za ta iya neman tazarce a zabe mai zuwa.
Asali: Legit.ng

