Gwamnatin Najeriya za Ta ba Manoma Tallafi bayan Karyewar Farashin Abinci

Gwamnatin Najeriya za Ta ba Manoma Tallafi bayan Karyewar Farashin Abinci

  • Gwamnatin tarayya ta ce za ta ɗauki matakan gaggawa domin tallafa wa manoma bayan da farashin wasu kayan abinci ya faɗi warwas a kasuwa
  • Ministan kuɗi, Wale Edun ya ce saukar farashin abinci ya kawo sauƙi ga masu saye, amma na iya hana manoma ci gaba da noma a fadin kasar nan
  • Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa 2026 za ta mayar da hankali kan tsaron abinci, samar da wutar lantarki, hanyoyi da kariya ga masu karamin karfi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Lagos – Gwamnatin tarayya ta bayyana aniyarta ta tallafa wa manoman ƙasar nan bayan da aka lura cewa farashin wasu kayan abinci ya faɗi.

Ministan kuɗi, Wale Edun, ne ya bayyana haka yayin gabatar da jawabin bude taron ƙaddamar da rahoton hasashen tattalin arzikin 2026 na kungiyar NESG a Lagos.

Kara karanta wannan

Rasha ta shiga rikicin Amurka da Iran, Trump na barazanar kai hari Tehran

Ministan kudin Najeriya da wata gona a gefen dama
Ministan kudi Wale Edun a gefen hagu, wata gona gefen dama. Hoto: Wale Edun|Getty Images
Source: Facebook

Premium Times ta rahoto ministan ya ce matakan tallafin za su kasance cikin gaggawa domin ƙarfafa manoma su ci gaba da zuba jari a noma, tare da kare nasarorin da aka samu na saukar farashin abinci a ƙasar.

Dalilin tallafawa manoman Najeriya

A cewar Wale Edun, wasu farashin kayan abinci sun sauka ƙasa da kuɗin da manoma ke kashewa wajen samar da su, lamarin da zai iya hana su ci gaba da noma idan ba a ɗauki mataki ba.

Ya ce:

“Akwai bukatar taimaka wa manoma a wannan lokaci, domin a wasu lokuta farashin ya faɗi ƙasa da kuɗin samarwa, kuma za a magance hakan cikin gaggawa domin ƙarfafa ci gaba da zuba jari a samar da abinci.”

Ministan ya jaddada cewa manufar gwamnati ita ce daidaita buƙatun masu saye da kuma ƙarfafa masu samarwa, musamman kananan manoma da ke da muhimmiyar rawa a wadatar abinci.

Farashin abinci ya sauka a Najeriya

Kara karanta wannan

Juyin mulki: Shugaba Bola Tinubu ya yi kira ga sojoji kan dimokuradiyya

Rahotanni sun nuna cewa farashin abinci da sauran kayayyaki sun ci gaba da raguwa watanni bayan tsauraran matakan kuɗi da gyare-gyaren tattalin arziki da Bola Tinubu ya ce ya yi.

Ya zuwa watan Disamba, 2025, hauhawar farashin abinci ya yi kasa da kashi 10.84 daga kashi 39.84 a Disamba, 2024, abin da ya nuna babban sauyi a tattalin arzikin ƙasa.

An ce saukar farashin ya samo asali ne daga wadatar abinci, sauƙin matsin lamba a bangaren canjin kuɗi da kuma rage kuɗin shigo da kaya daga waje.

Wasu manoma na aiki a gona
Yadda wasu manoma ke aiki a gona. Hoto: Getty Images
Source: UGC

The Guardian ta rahoto ministan ya ce kasafin kuɗin 2026 zai mayar da hankali kan sauya tattalin arziki zuwa samar da ingantaciyar rayuwa ga al’ummar Najeriya.

Ya ce muhimman fannoni da za a mayar da hankali a kansu sun haɗa da tsaron abinci, inganta wutar lantarki, faɗaɗa damar samun rancen gidaje, gina hanyoyi da kuma kare masu rauni a cikin al’umma.

Korafin manoma kan saukar farashi

A wani labarin, kun ji cewa wasu manoma a Najeriya sun yi korafi game da yadda farashin kayan abinci ya sauka kasa sosai a bana.

Kara karanta wannan

Sanata Barau zai fara raba kudi duk wata a Kano da kayan tallafi daban daban

Sun koka da cewa saukar farashin ya jefa su a matsaloli da dama saboda yadda kudin da suka kashe ya gagara dawowa bayan sayar da abin da suka noma.

Sun bukaci gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ta shiga lamarinsu domin karfafa jama'ar Najeriya su cigaba da noma domin samar da abinci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng