Bayan Kashe Mutane Fiye da 40, Gwamna Bago Ya Fadi Dalilin 'Yan Bindiga na Farmakar Kasuwan Daji
- Gwamnan jihar Neja, ya yi tsokaci kan mummunan harin da 'yan bindiga suka kai a Kasuwan Daji da ke karamar hukumar Borgu
- Umaru Bago ya bayyana cewa akwai dalilin da ya sa 'yan bindigan suka kai harin, inda suka kashe mutane tare da sace wasu
- Gwamnan ya bayyana cewa tun asali dama kasuwar ta yi kaurin suna wajen sayar da shanun sata, inda daga nan ne ma ta samo sunanta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Neja - Gwamnan jihar Niger, Mohammed Umaru Bago, ya yi karin bayani kan abin da ya janyo harin 'yan bindiga a Kasuwan Daji.
Mummunan harin na 'yan bindigan dai ya jawo kashe-kashe da sace-sacen mutane a kasuwar da ke karamar hukumar Borgu a jihar Neja.

Source: Twitter
Jaridar Leadership ta ce Gwamna Bago ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa bayan ziyarar girmamawa da ya kai wa Sarkin Borgu, Alhaji Mohammed Dantoro.
Wane bayani Gwamna Umaru Bago ya yi?
Gwamna Umaru Bago ya ce kasuwar ta dade da yin kaurin suna wajen sayar da shanun sata, jaridar Premium Times ta kawo labarin.
Ya ce bisa wannan dalili ne wata kungiyar ’yan bindiga mai gaba da wata ta kai hari kan kasuwar a makon da ya gabata, inda suka kashe mutane da dama.
"Abin takaici ne wannan na sake faruwa cikin kasa da watanni biyu, inda yanzu aka kashe mutane, aka yanka su a tsakiyar kasuwa.”
“Wannan kasuwa ana kiranta Kasuwan Daji. Kasuwan Daji kasuwa ce ta barayi. A ma’anarta, ana sayar da shanun sata ne a cikin daji, don haka wannan shi ne abin da ya faru."
"Harin da aka kai hari ne daga wata kungiyar ’yan bindiga a kasuwar da ake sayar da shanun sata."
"Abu mafi muhimmanci shi ne an kashe mutane. Yanzu mun fahimci tushen matsalar, shi ya sa muka zo domin gargadin majalisar masarautar da rawar da take takawa na ba mutanen da ba a san su ba masauki."

Kara karanta wannan
Gwamnan Kaduna ya hango abu mai kyau, ya ba 'yan Najeriya mafita kan dokar haraji
"Wanda daga bisani suke zuwa dauke da mugayen makamai, akidu na tsattsauran ra’ayi, da Boko Haram domin aikata munanan laifuka.”
- Gwamna Mohammed Umaru Bago
Matakin da Gwamna Bago ya dauka
Dangane da abin da ya kamata a yi gaba, gwamnan ya ce an umarci mazauna kauyukan da ke kewaye da dajin Tafkin Kainji da su fice daga yankin cikin watanni biyu masu zuwa.

Source: Facebook
An umarci su fice ne domin bai wa hukumomin tsaro damar fatattakar ’yan ta’adda da masu aikata laifuffuka a yankin.
Ya yi gargadin cewa za a samu asarar rayuka da dukiya idan mutanen kauyukan suka ki amincewa da barin yankin tare da rungumar shirin gwamnatin jihar da na masarautar na sake tsugunar da su.
Gwamnan ya ce wannan lamari ya zama kira ga majalisar masarautar da kada ta bari kowa ya zo ya zauna a yankinta ba tare da binciken asalin mutumin da inda ya fito ba.
'Yan ta'adda sun kai hari a jihar Neja
A wani labarin kuma kun ji cewa wasu 'yan ta'adda dauke da makamai sun kai harin ta'addanci a jihar Neja.
'Yan ta'addan sun kai harin ne sun kai harin ne kan wani shingen bincike na rundunar ‘yan sandan Najeriya a jihar Neja.
Tsagerun 'yan ta'addan sun kai harin ne a kauyen New Kalli da ke karamar hukumar Borgu a jihar Neja.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

