An Faɗi Lokacin Fara Cire Harajin VAT a Asusun Bankuna, Masu POS Sun Shiga Ciki

An Faɗi Lokacin Fara Cire Harajin VAT a Asusun Bankuna, Masu POS Sun Shiga Ciki

  • 'Yan Najeriya da suke amfani da bankuna za su fara biyan harajin VAT ga gwamnatin tarayya domin inganta tattali
  • An tabbatar da cewa a wannan watan Janairu 2026, bankuna za su fara cire harajin VAT kashi 7.5
  • Bankin Moniepoint ya ce sabon tsarin gwamnati ne, inda za a rika tura kudin VAT da aka cire kai tsaye zuwa Hukumar NRS

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Bankuna a Najeriya za su fara cire harajin VAT kashi 7.5 kan wasu hidimomin banki domin inganta tattalin arziki.

An tabbatar da cewa za a fara cire harajin ne daga ranar Litinin, 19 ga Janairu 2026 da muke ciki domin inganta hanyoyin samun kudin shiga ga gwamnatin tarayya.

Za a fara cire harajin VAT daga asusun bankunan yan Najeriya
Wani matashi yana cire kudi a na'urar ATM ta banki. Hoto: Contributor.
Source: Getty Images

Za a fara cire harajin VAT a Janairun 2026

A wata sanarwa da ta aikewa kwastomominta ta imel, bankin Moniepoint ya ce sabon tsarin ya samu amincewar gwamnati, cewar TheCable.

Kara karanta wannan

Cikin rashin imani, 'yan bindiga sun harbe 'matar sarki' mai shekara 75

Wannan ya shafi kudin canja wuri ta wayar hannu, cajin POS, USSD, da wasu kudaden hidimar banki da kwastomomi ke biya.

Bankin ya bayyana cewa VAT din ana cire shi ne daga kudin hidima da harajin hatimi N50, ba daga kudin da ake turawa ba.

Moniepoint ya ce kudaden VAT da aka tara za a mika su kai tsaye ga Hukumar Haraji ta Kasa, wato Nigerian Revenue Service (NRS).

Sanarwar ta ce:

“Daga 19 ga Janairu 2026, dukkan bankuna dole su fara tattara da tura VAT zuwa NRS.”

Bankin ya jero hidimomin da VAT zai shafa, ciki har da cajin POS, canja wuri ta waya, USSD, katin ATM da sauransu.

Harajin zai kuma shafi kudaden sarrafa rance, takardun bashi, da wasu kudaden hidimar banki da ake karba daga kwastomomi.

Banki ya fadi yadda za a cire harajin VAT
Tambarin bankin Moniepoint da matashiya rike da waya. Hoto: Moniepoint.
Source: UGC

VAT: Bankin Moniepoint ya yi karin haske

Moniepoint ya jaddada cewa ribar rance da kudin ajiya ba sa cikin hidimomin da harajin VAT ke shafa.

Bankin ya kara da cewa wannan ba neman kara farashi ba ne, illa bin umarnin gwamnati na tara haraji.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya ta kawo sabon tsari, masu amfani da banki za su fara biyan VAT

An bayyana cewa NRS ta sanya wa bankuna wa’adin 19 ga Janairu don fara aiwatar da tsarin VAT gaba daya.

Moniepoint ta ce za a rika nuna VAT a fili a cikin bayanan ma’amala da rahoton kudin banki na kwastomomi domin tabbatar da adalci.

Sababbin dokokin haraji a Najeriya sun bar kason VAT a kan kashi 7.5, ba tare da sauyi ba, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Hajjin 2026: Maniyyata za su biya haraji

Kun ji cewa rahoto ya nuna gwamnatin tarayya na shirin samun biliyoyin Naira daga alhazan Najeriya na Hajjin 2026 ta hanyar kudin hidima na 2%.

Kungiyar Independent Hajj Reporters (IHR) ta ce kowane maniyyaci zai biya kimanin N136,417, wanda za a tura kai tsaye zuwa Babban Bankin Najeriya.

Ta bukaci gwamnati da CBN su bayyana yadda ake amfani da kudin, tare da rokon Majalisar Tarayya ta yi bincike da ba da bayani kan yadda lamarin zai kasance.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.