Shehu Sani Ya Yi Karatun Ta Natsu, Ya Gano Hanyar Magance Matsalar 'Yan Bindiga
- Tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya yi maganganu kan matsalar rashin tsaro da ake fama da ita a Najeriya
- Sanata Shehu Sani ya bayyana cewa dole ne 'yan Najeriya su tashi tsaye domin kwato kansu daga hannun 'yan bindiga
- 'Dan siyasa kuma 'dan gwagwarmayar ya koka kan yadda 'yan bindiga ke cin karensu babu babbaka a wasu jihohin Arewacin Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Tsohon sanatan da ya wakilci Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya yi tsokaci kan matsalar 'yan bindiga da 'yan ta'adda da ake fama da ita a Najeriya.
Shehu Sani ya ce dole ne ’yan Najeriya su tashi tsaye su yi turjiya ga ’yan ta’adda, ’yan bindiga da sauran masu aikata laifufffuka da ke addabar kasar nan.

Source: Twitter
Jaridar TheCable ta ce Shehu Sani ya bayyana hakan ne yayin da yake magana a Abuja ranar Alhamis, 15 ga watan Janairun 2026 yayin bikin ƙaddamar da littattafansa guda biyu, The Councillor da The Perilous Path to Europe.

Kara karanta wannan
'Yan sanda sun samo mafita ga 'yan Najeriya idan suka hadu da masu neman rayuwarsu
Me Shehu Sani ya ce kan 'yan bindiga?
Tsohon sanatan ya jaddada cewa babu wata kasa daga waje da za ta zo ta ceto 'yan Najeriya da su daga wannan kalubale.
"Idan mutane suka haɗu suka samu wayewa, tare da samun goyon bayan hukumomin gwamnati, za su iya kayar da waɗanda ke ganin sun mallaki kasa kuma za su iya amfani da karfin makami su danne kowa.”
“Bai kamata mu yi tunanin cewa wata kasa ta waje za ta zo nan ta kuɓutar da mu daga waɗannan ’yan bindiga ba. Mu ne za mu yi wa kanmu yakin."
- Shehu Sani
Yayin da yake nuna cewa Najeriya na da tarihin dawo da zaman lafiya a wasu ƙasashe, Shehu Sani ya ce "Amurka ba za ta iya warware mana matsalolinmu ba."
Shehu Sani ya koka kan rashin tsaro
A wajen kaddamar da littattafan, an gabatar da wasan kwaikwayo mai taken The Village and Vigilante, wanda tsohon sanatan ya ce shi ne ya rubuta domin karfafa gwiwar ’yan Najeriya su tashi tsaye su kare kansu daga ’yan bindiga da ’yan ta’adda.

Kara karanta wannan
Jigon ADC ya zargi Tinubu da sakaci, an tsunduma mutane miliyan 141 a bakin talauci
Ya ce The Village and the Vigilante wasan kwaikwayo ne da ke bayani kan rawar da masu ruwa da tsaki ke takawa a al’umma irin ta karkara a Arewacin Najeriya, rahoton Daily Post ya tabbatar da hakan.
“Muna da sarakunan gargajiya, muna da jama’a, muna da ’yan sa-kai, sannan muna da jami’an tsaro, kowanne yana taka rawa daban-daban."
“The Village and the Vigilante, muna fatan, zai isar da sako karara ga al’ummar kasarmu cewa halin da muke ciki a yau wani mataki ne kawai a rayuwar kasarmu."
“Ba zai dawwama a tare da mu ba. Mu kasa ce mai yawan jama’a miliyan 230, kuma idan aka haɗa adadin duk waɗannan ’yan bindiga da ’yan ta’adda, ba su wuce 5,000 ba."
“Ya kamata a karfafa jama’a, a wayar musu da kai, a kuma tara su domin su tsaya tsayin daka wajen kare ’yancinsu, da mutuncinsu da darajarsu su a matsayin ’yan Adam."
“Daga Zamfara zuwa Katsina zuwa Kebbi, da wasu sassan jihar Kaduna da jihar Niger, mun ga yadda ’yan bindiga suke azabtar da al’ummarmu."
“Suna kashe mutane, suna garkuwa da mutane domin kuɗin fansa, suna kona kauyuka, suna raba miliyoyin jama’a da muhallansu."

Kara karanta wannan
Shehu Sani ya magantu bayan Amurka ta kawo tallafin kayan aiki ga sojojin Najeriya
- Shehu Sani

Source: Facebook
Shehu Sani ya yi martani kan tallafin Amurka
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya yi martani kan tallafin kayan aikin sojoji da Amurka ga Najeriya.
Tsohon sanatan ya yaba kan kawo muhimman kayan aikin sojoji da Amurka ta ba Najeriya a matsayin tallafi.
Shehu Sani ya bayyana cewa wannan tallafi zai karfafa kokarin Najeriya wajen dakile matsalar rashin tsaro, musamman a yankin Arewa maso Yamma.
Asali: Legit.ng