Katsina: Jigo a ADC Ya Bankado Yadda Aka Ware Kason 'Yan Bindiga a Kasafin Kudi

Katsina: Jigo a ADC Ya Bankado Yadda Aka Ware Kason 'Yan Bindiga a Kasafin Kudi

  • Tsohon sakataren gwamnatin jihar Katsina, Mustapha Muhammad Inuwa, ya soki tsarin sulhun da ake yi da 'yan bindiga a garuruwa
  • Dakta Mustapha Inuwa ya yi zargin cewa gwamnatin jihar Katsina na daukar kudin kananan hukumomi tana biyan 'yan bindiga da su
  • Tsohon sakataren gwamnatin ya nuna cewa har kudi ake warewa a kasafin kudi wadanda za a rika hidimar 'yan bindiga da su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Katsina - Tsohon sakataren gwamnatin jihar Katsina (SSG) kuma jigo a jam’iyyar ADC, Dakta Mustapha Inuwa, ya yi magana kan matsalar 'yan bindiga.

Mustapha Inuwa ya yi zargin cewa wata karamar hukuma a jihar ta ware Naira miliyan 300 a kasafin kudinta na shekara domin ci gaba da yarjejeniyoyin zaman lafiya da ’yan bindiga.

Mustapha Inuwa ya yi zarge-zarge kan 'yan bindiga
Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda da Mustapha Inuwa Hoto: Ibrahima Kaulaha Mohammed
Source: Facebook

Mustapha Inuwa ya bayyana wannan zargi ne yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a DCL Hausa.

Kara karanta wannan

An zo wajen: Kwankwaso ya kafa sharadin sauya sheka zuwa jam'iyyar APC

Jigon ADC ya soki gwamnatin Katsina

Jigon na ADC ya soki tsarin da gwamnatin jihar ke bi wajen magance matsalar rashin tsaro, yana mai gargadin cewa tattaunawa da kungiyoyin masu dauke da makamai na iya kara jefa al’ummomin karkara cikin hatsari.

A cewarsa, zargin ware kudade a kasafi ya sabawa ikirarin da gwamnatin jihar Katsina ke yi na cewa ba ta tattaunawa da ’yan bindiga.

Ana ba 'yan bindiga kudi a jihar Katsina

Jigon na ADC ya yi zargin cewa gwamnati na daukar kudin kananan hukumomi tana ba 'yan bindiga.

"Yanzu a wata wata ake ba su kudi. Gwamnati ke ba su kudi daga kudin kananan hukumomi."
"Akwai wata karamar hukumar da kasafin ta na wannan shekarar, miliyan 300 ne 'yan bindiga a nan cikin Katsina. Kasafin da ta yi na abin da za a yi hidimar 'yan bindiga miliyan 300 ne."

- Dakta Mustapha Inuwa

'Yan bindiga na kafa sharuddan zaman lafiya

Ya ce wannan lamari na nuni da cewa yanzu ’yan bindiga ne ke gindaya sharuddan zaman lafiya, maimakon gwamnati ta tilasta bin doka da oda.

Kara karanta wannan

Jigon ADC ya zargi Tinubu da sakaci, an tsunduma mutane miliyan 141 a bakin talauci

Tsohon SSG din ya bayyana damuwarsa cewa irin wadannan tsare-tsare sun bar mazauna yankunan karkara cikin barazana, musamman ganin rade-radin cewa gwamnatin jihar na duba yiwuwar sakin wasu mutane 70 da ake zargi ’yan bindiga ne da ke tsare a halin yanzu.

Ya ce al’ummar yankunan na fargabar yiwuwar daukar fansa idan aka saki wadanda ake zargin, musamman kan mutanen da suka taimaka wa hukumomin tsaro wajen gano su tare da kama su.

Mustapha Inuwa ya ce ana ba 'yan bindiga kudi a Katsina
Tsohon sakataren gwamnatin jihar Katsina, Mustapha Inuwa Hoto: Ibrahim Mukhtar
Source: Facebook

Mustapha Inuwa ya amince cewa zaman lafiya ya dawo a wasu al’ummomi, amma ya jaddada cewa har yanzu rashin tsaro na ci gaba da addabar wasu yankuna.

Ya ambaci sababbin hare-hare a karamar hukumar Malumfashi da wasu sassan jihar a matsayin hujja cewa har yanzu ba a warware matsalar ba.

'Yan bindiga sun kai hari a Katsina

A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindiga dauke da makamai sun kai hari kan tawagar masu zuwa taron biki a Katsina.

Tsagerun 'yan bindigan sun kashe akalla mutane biyu daga tawagar masu zuwa biki a harin yayin da wasu da dama, ciki har da amarya, suka jikkata.

'Yan bindigan sun yi awon gaba da baki da dama da suka halarci biki, wadanda ba a san adadinsu ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng