Cikin Rashin Imani, 'Yan Bindiga Sun Harbe 'Matar Sarki' Mai Shekara 75

Cikin Rashin Imani, 'Yan Bindiga Sun Harbe 'Matar Sarki' Mai Shekara 75

  • ’Yan bindiga sun kai mummunan hari Kabe a karamar hukumar Borgu, inda suka bindige matar Sarkin Noma yayin da jama’a ke tserewa
  • Mazauna sun ce harin ya faru ne da dare, inda aka fasa shaguna, aka sace kayan abinci, inda kauyuka da dama suka fara watsewa
  • Hakan na zuwa ne yayin da gwamnatin jihar Neja ke cewa tana daukar matakai domin magance matsalar 'yan bindiga da sauran 'yan ta'adda

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Neja – Wata tsohuwa mai shekaru 75, Amina Abu-Shaki, matar Sarkin Noma na al’ummar Kabe, ta rasa ranta bayan ’yan bindiga sun kai hari garin Kabe da ke karamar hukumar Borgu.

Rahotanni sun ce an bindige ta ne yayin da aka hango ta a wajen da ta buya a cikin daji a lokacin da jama’a ke tserewa domin kubuta da rayukansu.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun ci gaba da ta'asa a Benue, an hallaka dan sanda da jikkata matafiya

Taswirar jihar Neja
Taswirar jihar Neja a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

Daily Trust ta wallafa cewa harin ya faru ne da misalin karfe 8:00 na dare, lokacin da ’yan bindigar suka shigo cikin al’umma suna harbe-harbe ba kakkautawa.

Yadda aka harbe matar Sarkin noma

Wani mazaunin garin Kebe, Malam Awwalu, ya shaida cewa bayan ’yan bindigar sun kammala barnar da suka yi, sun hango tsohuwar a inda ta buya, sannan suka harbe ta nan take, lamarin da ya janyo mutuwarta a wurin.

Malam Awwalu ya ce ’yan bindiga da yawa sun shiga Kabe, inda suka rika lalata shaguna tare da kwashe kayan abinci da wasu muhimman kayayyaki.

Channes TV ta rahoto ya kara da cewa an ga tsohuwar da aka kashe ne a kan hanyar da ’yan bindigar suka bi suna ficewa daga garin bayan harin.

“An hango ta a cikin daji inda take buya, sai suka bindige ta, ta mutu nan take,”

- In ji shi

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun farmaki amarya da wasu 'yan gidan biki, an rasa rayukan bayin Allah

'Yan bindiga sun kai hari Neja

A wani harin daban da ya faru a kauyen Damala, wanda shi ma ke karamar hukumar Borgu, an kashe mutane hudu a makon da ya wuce.

Majiyoyi sun ce ’yan bindigar sun shigo kauyen da misalin karfe 8:00 na dare, inda suka harbe mutane hudu, suka kuma tilasta wa sauran mazauna tserewa daga gidajensu.

An ce maharan sun kuma kwashe shanu da sauran dabbobi da dama, tare da banka wa wuraren ibada da gidaje da dama wuta.

Gwamna Umaru Bago a fadar Borgu
Gwamna Bago a lokacin da ya ziyarci fadar Sarkin Borgu. Hoto: Balogi Ibrahim
Source: Facebook

Wani jami’in a karamar hukumar Borgu, Musa Saidu, ya tabbatar da kisan mutane hudun a Damala, yana mai cewa lamarin abin takaici ne da ke bukatar daukin gaggawa.

Za a kakkabe 'yan bindiga a Neja

A wani rahoton, kun ji cewa a kokarin dakile ta’addanci, gwamna Umaru Bago, ya umarci al’ummomin da ke kusa da Kainji da su fice daga gidajensu.

Ya bayyana hakan ne yayin da ya kai ziyarar jaje ga Sarkin Borgu, Alhaji Muhammad Haliru Dantoro Kitoro IV, a fadarsa da ke New Bussa.

Gwamnan ya ce wannan mataki ya zama dole domin bai wa jami’an tsaro damar kakkabe ’yan bindigar da ke amfani da yankin a matsayin maboya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng