Bayan Morocco Ta Doke Najeriya, BUA Ya Yi Magana kan Alkawarin Dalolin Kudi da Ya Yi
- Attajirin dan kasuwar Afrika, Abdulsamad Rabiu BUA ya yi magana kan alkawarin da ya dauka na ba Super Eagles kyautar $500,000
- BUA ya dawo da batun kyautar kudin ne bayan Najeriya ta sha kashi a hannun Morocco a wasan kusa da na karshe na gasar AFCON 2025
- Manyan yan siyasa kamar Sanata Rabiu Kwankwaso da Peter Obi sun bukaci 'yan Super Eagles su dage don zuwa na uku a gasar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Shugaban kamfanin BUA Group, Abdulsamad Rabiu, ya sanar da cewa zai cika alkawarin da ya yi wa tawagar Super Eagles na ba su kyautar $500,000.
A ranar Laraba, 14 ga Janairu, 2025, attajirin dan kasuwar ya ce zai cika wannan alkawar duk da rashin samun nasarar kaiwa ga wasan ƙarshe na lashe kofin AFCON 2025.

Source: Twitter
Morocco ta doke Najeriya a AFCON 2025
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na X a makon jiya, BUA ya ɗauki wannan alkawarin ba Super Eagles $500,000 bayan doke Ajeriya, da alkawarin $1,000,000 idan sun ci kofin AFCON 2025.
To sai dai kuma, Legit Hausa ta rahoto cewa tawagar Super Eagles ta yi rashin nasara a wasan kusa da na karshe da ta kara da Morocco mai masaukin baki.
Wasan ya tashi 0:0 a mintuna 90 na farko, sannan an tashi canjaras a wasan karin lokaci na mintuna 30, inda a karshe aka doke Najeriya da ci 4-2 a bugun fanareti.
A sakon da ya wallafa a shafinsa na X jim kadan bayan kammala wasan, BUA ya yaba wa 'yan wasan bisa jajircewa da kwarin gwiwar da suka nuna a duk tsawon gasar.
BUA zai cika alkawari ga Super Eagles

Kara karanta wannan
AFCON 2025: Gwamnatin tarayya ta aika sako ga Super Eagles yayin da take shirin fafatawa da Morocco
Duk da cewa ba a samu nasarar da ake buƙata ba, Abdulsamad Rabiu ya nuna cewa ruhin haɗin kai da kishin ƙasa da 'yan wasan suka nuna shi ne babban abin duba da ya fi kofin mahimmanci.
Ya bayyana cewa:
“Kun yi wasa da zuciya ɗaya, kun bayar da dukkan ƙarfinku, kuma kun nuna gaskiyar jarumta a fili. Ko da yake rabon bai zo ba a wannan karon, kun sanya kowane ɗan Najeriya alfahari da kasarsa.”
Ya ƙara da cewa zai cika alkawarin ba da kyautar $500,000 ga 'yan wasan don karrama ƙwazon su da sadaukarwar da suka yi, da kuma irin farin cikin da suka sanya wa miliyoyin 'yan Najeriya a lokacin gasar.
BUA ya jaddada cewa ko da ƙoƙarin mutum bai kawo sakamakon da ake fata ba, nuna ƙwazo da kishin ƙasa abin murna ne da ya cancanci tukuici.

Source: Twitter
AFCON: Martanin manyan 'yan siyasa
Manyan 'yan siyasar Najeriya ma sun taya 'yan wasan jimami tare da ba su kwarin gwiwa:
Rabiu Musa Kwankwaso, a shafinsa na X, ya buƙaci Super Eagles da su dage su nemi lambar yabo ta tagulla a wasa na gaba.
Sanata Shehu Sani, a dandalin na X, ya bayyana cewa bugun fanareti ba ma'aunin ƙwarewa ba ne, face sa'a, sannan ya ce wasannin Super Eagles sun jawo haɗin kan ƙasar da ba a taɓa gani ba.
A shafinsa na X, Peter Obi kuwa ya yabawa 'yan wasan bisa ƙoƙarinsu na tsawon mintuna 120 ba tare da sun karaya ba, inda ya ce "Mikiya ba ta daina tashi ba," yana mai kira gare su da su kiyaye martabarsu su nemo lambar tagulla.
Mourinho ya hango nasarar Morocco
A wani labarin, mun ruwaito cewa, tun kafin a fara wasan Najeriya da Morocco, kocin Benfica, Jose Mourinho ya ce kungiyar Atlas Lions ne za su daga kofin AFCON 2025.
Mourinho ya ce duk da cewa Najeriya na da shahararrun 'yan wasa, amma Morocco ta riga ta nuna wa duniya cewa yanzu ta daina zama 'yar kallo a fagen tamaula.
Tsohon kocin kungiyar Manchester United da Chelsea, yakuma bayyana Morocco a matsayin ƙasa mafi ƙarfi da kowa ya kamata ya ji tsoronta a nahiyar Afirka.
Asali: Legit.ng

