Gwamna Ya Sayo Dankara Dankaran Motoci 65 na Alfarma, Ya Rabawa Sarakuna

Gwamna Ya Sayo Dankara Dankaran Motoci 65 na Alfarma, Ya Rabawa Sarakuna

  • Gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori ya raba wa sarakuna motocin alfarma domin tallafa masu wajen gudanar da ayyukansu
  • Sheriff Oborevwori ya yaba wa gudummuwar da sarakunan gargajiya ke bayarwa wajen tafiyar da harkokin mulki a Delta
  • A cewarsa, kokarin da sarakunan ke yi abin a yaba ne domin su ke shiga lungu da sako domin tabbatar da zaman lafiya da hadin kai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Delta, Nigeria - Gwamnan Jihar Delta, Sheriff Oborevwori, ya ba wa sarakunan gargajiya na jihar kyautar sababbin motoci kirar SUV guda 65.

Gwamnan ya ce ya masu wannan kyauta ne a matsayin tallafi ga ayyukansu na tabbatar da zaman lafiya da ci gaba a fadin jihar Delta.

Gwamna Oborevwori.
Gwamnan jihar Delta, Sherrif Oborevwori yana jawabi Hoto: Rt. Hon. Sherrif Oborevwori
Source: Facebook

Daily Trust ta tattaro cewa Sheriff Oborevwori ya mika motocin ga sarakunan a ranar Laraba a gidan gwamnati da ke Asaba.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Gwamnatin Tinubu ta yi wasu sauye sauye da sababbin dokokin haraji

Ya bayyana sarautar gargajiya a matsayin "hanya ta yin hidima ga al'umma" kuma ginshikin zaman lafiya.

Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa (NAN) ya ruwaito cewa motocin da aka raba sun hada da sababbin motoci kirar Prado Jeep guda 60 da kuma Land Cruiser guda biyar.

Dalilin rabawa sarakuna motoci a Delta

A cewar gwamnan, wannan karamci ya nuna muhimmancin da sarakuna ke da shi a cikin harkokin gudanarwa, kamar yadda Punch ta ruwaito.

"Sarakunan mu sun wuce a kira su da masu kare al'adu, su ne tsani da ke hada gwamnati da mutanen karkara," in ji Oborevwori.

Ya kara da cewa gudunmawar da sarakunan ke bayarwa wajen tafiyar da mulki tana da girma kwarai, kodayake sau da yawa ba a cika bayyana hakan ba.

Yadda sarakuna ke taimakon gwamnatin Delta

Gwamnan Oborevwori ya jinjina wa sarakunan kan yadda suke taimaka wa jami’an tsaro, sasanta rikice-rikice tsakanin al’umma, da kuma tallata shirye-shiryen gwamnati ba tare da jiran wani sakamako ba.

"Zan iya fada da babbar murya cewa sarakunan gargajiya sun sanya harkar mulki ta zama mai sauki da tasiri a jihar Delta.

Kara karanta wannan

Jigon ADC ya zargi Tinubu da sakaci, an tsunduma mutane miliyan 141 a bakin talauci

"Suna yawan tafiye-tafiye a kan hanya don sasanta rikice-rikice da tabbatar da zaman lafiya. Mun zabi ba su wadannan motoci masu karfi ne saboda la'akari da yankunan karkara da suke gudanar da ayyukansu."

- In ji Gwamna Sheriff Oborevwori.

Gwamnan ya kammala da cewa wannan mataki na daya daga cikin kudurorin gwamnatinsa karkashin ajendar M.O.R.E, wanda ke nufin samar da dama ga kowa.

Ya gode wa sarakunan bisa yadda suke nuna masa kauna da hadin kai a duk lokacin da ya ziyarci masarautunsu.

Motoci.
Wasu daga cikin motocin da Gwamnan Delta ya rabawa sarakuna Hoto: Delta State Government
Source: UGC

Gwamnan Delta ya ce jihohi na samun kudi

A wani labarin, kun ji cewa gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori, ya ce jihohi na samun makudan kuɗaɗe fiye da baya daga asusun rarraba kuɗin shiga na tarayya.

Gwamnan ya ce babu dalilin ɓoye gaskiya ga ’yan Najeriya, yana mai cewa gwamnatocin jihohi yanzu suna da isassun kuɗaɗe.

Oborevwori ya faɗi hakan ne a ranar Litinin, 12 ga watan Janairun 2026 yayin bikin fara aikin gina gadar sama ta Otovwodo a kan kuɗi Naira biliyan 39.3.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262