An Ware Kwanaki 4, Za a Birne Mataimakin Gwamnan da Ya Rasu a Najeriya
- Gwamnatin jihar Bayelsa da iyalan marigayi Mataimakin gwamna, Lawrence Ewhrudjakpo sun cimma matsaya kan jana'izarsa
- Gwamna Douye Diri na jihar Bayelsa ya sanar da cewa za a yi taron addu'o'i tare da birne gawar mataimakinsa a ranar 30 ga watan Janairu, 2026
- A watan Disamba, 2025 ne mataimakin gwamnan ya rasu jim kadan bayan ya fadi a cikin gidan gwamnati da ke Yenagoa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Bayelsa, Nigeria - Gwamnatin jihar Bayelsa ta kammala shirye-shiryen jana'izar mataimakin gwamna, Mr Lawrence Ewhrudjakpo, wanda ya rasu a kwanakin baya.
Idan ba ku manta ba, a ranar Alhamis, 11 ga watan Disamba, 2025, Ewhrudjakpo ya yanke jiki ya fadi a ofishinsa da ke cikin gidan gwamnatin Bayelsa, inda aka garzaya da shi asibitin tarayya (FMC) amma rai ya yi halinsa.

Source: Facebook
Tashar Channels tv ta rahoto cewa gwamnati Bayelsa ta tabbatar da rasuwar mataimakin gwamnan da yammacin ranar Juma'a, 12 ga watan Disamba, 2025.
Bayan wata daya, gwamnan Bayelsa, Douye Diri, ya sanar da cewa za a gudanar da jana'izar tsohon mataimakinsa, Marigayi Lawrence Ewhrudjakpo, a ranar 30 ga watan Janairu, 2026.
Gwamna Diri ya bayyana hakan ne a yau Laraba, 14 ga watan Janairu, 2026 yayin taron Majalisar Zartarwa ta Jiha karo na 179 da aka gudanar a gidan gwamnati da ke Yenagoa.
Yadda aka tsara jana'izar Lawrence Ewhrudjakpo
Gwamna Diri ya bayyana cewa an amince da gudanar da tarurruka na kwanaki hudu don karrama marigayin, biyo bayan shawarwarin da kwamitin jana'iza karkashin jagorancin Sakataren Gwamnatin Jiha, Farfesa Nimibofa Ayawei, ya bayar.
Ya ce za a fara da wasannin motsa jiki a ranar 27 ga watan Janairu, 2026 duk a wani bangare na jimami da karrama tsohon mataimakin gwamnan.
A rahoton Vanguard, Douye Diri ya ce:
"A ranar 27 ga Janairu, 2026 za a fara da wasannin motsa jiki, sai kuma washe gari watau ranar 28 ga watan Janairu, wadda aka ware domin bayyana yabo da jinjina ga rayuwar marigayin.
Za a birne mataimakin gwamnan Bayelsa
Gwamnan ya kara da cewa a ranar 29 ga Janairun 2026 za a gudanar da taron bankwana na musamman a Babbar Kotun Jiha da kuma dakin taron Majalisar Zartarwa.
Ya ce a ranar 30 ga Janairu, 2026, za a yi addu’o’i na musamman a cocin St Paul’s Catholic Church da ke Ofoni, kafin daga bisani a birne gawar marigayin.

Source: Twitter
Gwamna Diri ya jaddada cewa gwamnatin jihar Bayelsa, iyalan marigayin, da kuma coci duk sun amince da wannan tsari don girmama tsohon mataimakin gwamnan.
Gwamna ya bada umarnin binciken mutuwar Ewhrudjakpo
A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Diri ya bayar da umarnin a gudanar da binciken gawa, domin gano musabbabin mutuwar mataimakin gwamnan jihar, Lawrence Ewhrudjakpo.
Gwamna Diri ya fadi haka ne yayin da ya karɓi bakuncin tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan a gidan gwamnatin jihar Bayelsa da ke Yenagoa.
Douye Diri ya kuma yi Allah-wadai da abin da ya kira shirme da ake yadawa a kafafen sada zumunta game da mutuwar Ewhrudjakpo.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


