Newswatch: Najeriya Ta Kara Yin Rashi, Yakubu Mohammed Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

Newswatch: Najeriya Ta Kara Yin Rashi, Yakubu Mohammed Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

  • An tabbatar da rasuwar fitaccen dan jarida kuma daya daga cikin wadanda suka kafa Newswatch, Yakubu Mohammed bayan fama da jinya
  • Wata majiya mai kusanci da iyalan mamacin ta bayyana cewa ya dade yana fama da ciwon suga, wanda hakan ne ya yi ajalinsa ranar Talata
  • Gwamnan jihar Kogi Ahmed Usman Ododo ya yi alhinin rasuwar Yakubu, yana mai bayyana shi a matsayin jagora a aikin jarida

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kogi, Nigeria - Fitaccen dan jaridar nan kuma daya daga cikin wadanda suka kafa mujallar Newswatch, Yakubu Mohammed, ya rasu yana da shekara 75 a duniya.

Rasuwar Yakubu na zuwa ne kasa da watanni biyu bayan mutuwar babban abokin aikinsa kuma daya daga cikin wadanda suka kafa Newswatch, Dan Agbese, wanda ya rasu a ranar 17 ga Nuwamba, 2025.

Kara karanta wannan

Shirin tsige Gwamna Fubara a Majalisa ya gamu da tangarda, 'yan Majalisa 2 sun canza tunani

Dan jarida, Yakubu Mohammed da Gwamna Ododo.
Fitaccen dan jarida a Najeriya, Yakubu Mohammed da Gwamna Ahmed Ododo na jihar Kogi Hoto: @NTANetwork
Source: Twitter

Abin da ya zama ajalin dan jaridar

Rahoton Daily Trust ya nuna cewa Yakubu Mohammed ya rasu ne a birnin Legas ranar Talata, 13 ga watan Janairu, 2025.

Wata majiya mai kusanci da iyalan mamacin ta bayyana cewa ya dade yana fama da ciwon sukari, wanda hakan ne ya yi sanadiyyar rasuwarsa.

"Ya dade yana jinyar ciwon suga, kuma ya rasu a ranar Talata a Legas. Iyalansa za su fitar da jawabi a hukumance nan ba da jimawa ba," in ji majiyar.

Takaitaccen tarihin marigayi Yakubu Mohammed

An haifi Yakubu Mohammed ne a ranar 4 ga Afrilu, 1950, a garin Ologba da ke karamar hukumar Dekina a jihar Kogi, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Ya yi karatunsa na farko a Ayangba da Okene kafin ya wuce Jami'ar Legas (UNILAG) inda ya kammala digiri a 1975. Ya kuma kara karatu a kwalejin fasaha ta Glasgow da ke kasar Scotland.

Kara karanta wannan

Tinubu ya kashe Naira biliyan 40 a zamanantar da gadar Legas da CCTV

Yakubu Mohammed ya kafa tarihi a aikin jarida a Najeriya lokacin da suka kafa jaridar Newswatch a 1985, tare da sauran abokan aikinsa kamar su Dele Giwa, Ray Ekpu, da Dan Agbese.

Gwamna Ododo ya aika da sakon ta'aziyya

Gwamnan Jihar Kogi, Ahmed Usman Ododo, ya nuna alhininsa kan wannan babban rashi, inda ya bayyana marigayin a matsayin daya daga cikin jagororin aikin jarida na bincike a Najeriya.

Gwamna Ahmed Ododo.
Gwamna Ahmed Udman Ododo a fadar gwamnatin jihar Kogi Hoto: Ahmed Usman Ododo
Source: Twitter

A cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan kafofin yada labarai, Hon. Ismaila Isah ya fitar, Gwamna Ododo ya ce:

"Alhaji Yakubu Mohammed daya ne daga cikin 'yan jarida da suka bayyana ma'anar jarumta da kwarewa a aikin jarida. Ya kasance tamkar gada, mai jagorantar matasa kuma mutum ne mai gaskiya."

Gwamnan ya yi addu'ar Allah ya jikan mamacin da rahama, sannan ya ba iyalan mamacin da kungiyar 'yan jarida ta kasa (NUJ) hakurin jure wannan rashi.

Matar tsohon gwamnan Ogun ta rasu

A wani rahoton, kun ji cewa uwargidan tsohon gwamnan farar hula na farko a Jihar Ogun, Cif Olabisi Onabanjo ta rasu bayan fama da doguwar jinya.

Kara karanta wannan

Sababbin matasan 'yan wasa 5 da suka dauki hankula a gasar AFCON 2025

’Diyarta, Olubukunola Onabanjo, ce ta tabbatar da rasuwar mahaifiyarsu a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Talata 13 ga Janairu, 2025.

Rasuwar Lucia Onabanjo ta janyo alhini da jimami daga ’yan uwa, abokai da al’ummar Jihar Ogun, inda da dama ke yabon gudunmawar da ta bayar a rayuwarta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262