Shirin Tsige Gwamna Fubara a Rivers Ya Sake Gamuwa da Cikas a Majalisa
- 'Yan majalisar dokokin jihar Rivers na ci gaba da yunkurin ganin sun tsige Gwamna Siminalayi Fubara da mataimakiyarsa, Ngozi Odu
- Sai dai, shirin tsige gwamnan ya fuskanci tangarda bayan da wasu 'yan majalisa suka janye goyon bayan da suke yi
- Sun bayyana dalilin da ya sanya suka sake tunani duk da cewa sun amince cewa ta iya yiwuwa gwamnan ya yi laifi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Rivers - Yunkurin tsige gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, da mataimakiyarsa, Farfesa Ngozi Odu, ya sake fuskantar tangarda.
Shirin tsige Gwamna Simi Fubara ya sake samun tangarda ne bayan wasu ’yan majalisar dokokin jihar biyu sun janye goyon bayansu ga wannan tsari.

Source: Facebook
Tashar Channels tv ta kawo rahoto cewa 'yan majalisar sun yi kira da a warware rikicin siyasar jihar ta hanyar zaman lafiya.

Kara karanta wannan
Shirin tsige Gwamna Fubara a Majalisa ya gamu da tangarda, 'yan Majalisa 2 sun canza tunani
'Yan majalisa sun janye daga shirin tsige Fubara
Barile Nwakoh, mai wakiltar mazabar Khana I, da Emilia Amadi ta mazabar Obio/Akpor II, sun bayyana matsayinsu ne kasa da awanni 48 bayan da wasu ’yan majalisa biyu sun sanar da janye goyon bayansu ga shirin.
Duk da janyewar, 'yan majalisar sun jaddada cewa gwamnan da mataimakiyarsa na iya karya wasu tanade-tanaden kundin tsarin mulki.
Meyasa wasu 'yan majalisar dokokin suka janye?
Sun ce sauyin ra’ayinsu ya biyo bayan shiga tsakani da rokon da manyan shugabanni da masu ruwa da tsaki da suka yi, inda suka bukaci a yi hakuri domin samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar, rahoton TVC News ya tabbatar da hakan.
Da wannan sabon ci gaba, yanzu ’yan majalisa hudu daga cikin 26 da tun da fari suka amince da sanarwar zargin aikata manyan laifuffuka sun janye daga yunkurin tsige gwamnan.
Janyewar tasu na kara nuna karuwar kiraye-kirayen yin sulhu da tattaunawa a cikin majalisar maimakon fafatawa da bangaren gwamnati.
Ana sa ran majalisar dokokin jihar Rivers za ta koma zama a ranar 15 ga Janairu, 2026, yayin da hankula ke karkata kan yadda shugabancin majalisar zai tafiyar da rarrabuwar kai da ke kara tsananta a cikinta.

Source: Original
Yunkurin tsige Fubara ya gamu da tangarda
A baya, shugaban marasa rinjaye a majalisar, Sylvanus Nwankwo, mai wakiltar mazabar Omuma, da Peter Abbey na mazabar Degema, sun sanar da janyewarsu daga tsarin tsige gwamnan yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a Port Harcourt.
’Yan majalisar sun bukaci takwarorinsu da su duba wasu hanyoyi daban-daban na warware rikicin siyasar, suna gargadin cewa ci gaba da zaman dar-dar na iya kara dagula tafiyar da harkokin mulki a jihar.
Fayose: Tinubu zai zabi Wike kan Fubara
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya yi tsokaci kan rikicin siyasar Rivers da wanda Shugaba Bola Tinubu zai goyawa baya.
Ayodele Fayose ya ce Tinubu ba zai taba sadaukar da Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike ba domin Gwamnan Rivers, Siminalayi Fubara.
A cewar tsohon gwamnan, Nyesom Wike ya fi Fubara muhimmanci a fagen siyasa ga Shugaba Tinubu, don haka babu dalilin da zai sa shugaban ya yi watsi da shi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
