An Dakatar da Likitoci kan Barin Almakashi a Cikin Matar Aure yayin Tiyata a Kano

An Dakatar da Likitoci kan Barin Almakashi a Cikin Matar Aure yayin Tiyata a Kano

  • Hukumar kula da asibitocin Kano ta tabbatar da cewa barin almakashi a ciki ya kai ga mutuwar Aishatu Umar bayan tiyata a asibitin Abubakar Imam Urology
  • Rahotanni sun nuna cewa an dakatar da ma’aikata uku da ake zargi da hannu a lamarin, tare da mika batun ga kwamitin ladabtar da likitoci na jihar Kano
  • Baya ga dakatar da jami'an, hukumar ta yi alkawarin daukar tsauraran matakai domin hana sake faruwar irin wannan kuskure a asibitocin gwamnati a nan gaba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano – Hukumar kula da asibitocin jihar Kano ta tabbatar da cewa batun barin almakashi a cikin maras lafiya, Aishatu Umar ya faru a asibitin Abubakar Imam Urology.

Hukumar ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da ta fitar a yammacin Talata, inda ta ce binciken farko da aka gudanar ya tabbatar da sahihancin faruwar lamarin a wannan cibiya ta lafiya.

Kara karanta wannan

Majalisa za ta haramta zina da ƙaƙaba hukunci mai tsanani? Gaskiya ta fito

Aisha Umar da aka bar almakashi a cikinta
Maras lafiyar da aka bar almakashi a cikinta bayan tiyata a Kano. Hoto: Sophie Shureem Danja|Getty Images
Source: Facebook

Sanarwar da hadimin gwamnan Kano, Ibrahim Adam ya wallafa a Facebook ta jaddada cewa an dauki matakin ne bisa umarnin babban sakataren hukumar, Dr. Mansur Mudi Nagoda.

An bar almakashi a ciki bayan tiyata

A cewar sanarwar, binciken da aka yi cikin gaskiya ya tabbatar da cewa marigayiya Aishatu Umar ta fuskanci matsala bayan wata tiyata da aka yi mata a asibitin Abubakar Imam Urology Centre.

Jaridar Leadership ta wallafa cewa bincike ya zo ne bayan zargin da iyalanta suka yi cewa an yi sakacin barin almakashi a cikinta a lokacin tiyatar da aka mata.

Hukumar ta ce ta dakatar da ma’aikata uku da aka gano suna da alaka kai tsaye da lamarin daga duk wani aikin jinya da asibiti, nan take.

Matakin dakatarwar, a cewar hukumar, na wucin gadi ne har sai an kammala cikakken bincike, kuma an dauke shi a matsayin mataki na farko wajen kare martabar sana’ar likitanci da lafiyar marasa lafiya.

Kara karanta wannan

Matar aure ta mutu bayan barin almakashi a cikinta yayin tiyata a Kano

An mika lamarin ga kwamitin ladabtarwa

Hukumar ta kuma bayyana cewa ta mika lamarin ga Kwamitin Ladabtar da Likitoci na Jihar Kano domin ci gaba da bincike da daukar matakan hukunci idan an tabbatar da laifi.

Ana sa ran cewa wannan mataki zai tabbatar da cewa duk wani hukunci da za a dauka ya yi daidai da dokoki, ka’idojin sana’a, da kuma dabi’un aikin likitanci.

Taswirar jihar Kano
Taswirar jihar Kano a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

Sakon ta’aziyya da alkawarin gyara

Hukumar ta mika sakon ta’aziyyarta ga iyalan marigayiya Aishatu Umar, tana mai bayyana alhininta kan irin wannan rashi mai radadi.

Har ila yau, hukumar ta tabbatar wa al’ummar Kano cewa za ta kara karfafa tsarin sa ido a cikin asibitocin gwamnati tare da tabbatar da bin ka’idojin sana’a yadda ya kamata.

Bayanin mijin matar da aka yi wa tiyata

A wani labarin, mun kawo muku cewa mijin Aishatu Abubakar da ta rasu bayan mata tiyata saboda barin almakashi a cikinta ya fito ya yi magana.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta fara binciken yadda likitoci suka bar almakashi a cikin wata mata

Mijin matar ya kara da cewa sun shafe watanni suna zuwa asibiti domin duba abin da ke damun matar ta shi amma ba a gano damuwarta ba.

Bayan shafe lokaci ne ya bayyana cewa sun ziyarci wasu asibitoci domin a duba lafiyar matar, a can ne kuma ya ce aka gano an bar almakashi a cikinta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng