ICPC Ta Gurfanar da Mutumin El Rufai, Ana Zargin Ya Karkatar da Biliyoyin Naira
- Hukumar ICPC ta gurfanar da Amadu Sule a kotun Kaduna kan zargin safarar haramtattun kudade naira biliyan dari uku da goma sha daya
- Ana zargin Sule da kamfanin TMDK da boye kudaden haraji da suka fito daga haramtattun ayyuka tare da boye asalin kudaden a bankuna
- Wannan shari'a ta ja hankali duba da alakar Sule da tsohon gwamna El-Rufai da kuma yadda aka taba gurfanar da sauran mataimakansa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kaduna - Hukumar yaƙi da cin hanci ta ICPC ta gurfanar da Amadu Sule, babban daraktan kamfanin TMDK Terminal Limited, a gaban babbar kotun tarayya da ke Kaduna.
Ana tuhumar Sule, wanda aka sani a matsayin mutumin tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, da laifuffuka biyar da suka shafi safarar kuɗaɗe da suka kai kimanin Naira biliyan 311.

Kara karanta wannan
Mutum 2 da za su gabatar da shaida a shari'ar Ganduje sun fara fuskantar hadari a Kano

Source: Instagram
An gurfanar da aminin El Rufai a kotu
Bayanin hakan na kunshe a cikin takardar tuhuma da shugaban sashen shari’a na ICPC, Osuobeni Akponimisingha ya sanya wa hannu, in ji rahoton The Cable.
A cikin takardar, hukumar ICPC ta bayyana cewa Amadu Sule ya mallaki waɗannan maƙudan kuɗaɗe a asusun bankunan Fidelity, Stanbic IBTC, da kuma Providus.
Hukumar ta bayyana cewa an turo waɗannan kuɗaɗe ne daga kamfanonin sadarwa irin su IHS Nigeria Limited da Boaz Commodities Limited, da sunan biyan kuɗin samar da man fetur.
Alaƙar kamfanin TMDK da iyalan El-Rufai
Wannan shari'a ta ja hankalin jama'a da masu sharhi kan al'amuran yau da kullum duba da yadda kamfanin TMDK Terminal Limited ke da 'kyakkyawar alakar' kasuwanci da siyasa da iyalan tsohon gwamna El-Rufai.
Rahoton jaridar Punch ya nuna cewa ana zargin har ma babban yayan tsohon gwamnan, Bashir El-Rufai, yana da hannu a wasu harkokin kamfanin.
ICPC ta bayyana cewa, ya kamata a ce Amadu Sule ya san cewa an samu waɗannan kuɗaɗen ta haramtattun ayyuka, kuma ya haɗa baki da kamfanin TMDK wajen riƙe harajin da ya kamata a biya wa gwamnati daga waɗannan ma’amaloli na zamba.

Source: Original
ICPC ta taso aminan El Rufai a gaba
Wannan ba shi ne karon farko da hukumar ICPC ke damƙe na kusa da tsohon gwamnan na Kaduna ba a cewar rahoton Business Day.
A cikin watan Janairun 2025, hukumar ta gurfanar da Jimi Lawal, tsohon babban mataimakin El-Rufai, kan makamancin wannan zargi na zamba da safarar haramtattun kuɗaɗe.
Kotun ta saurari bayanan farko sannan ta ɗage sauraron shari’ar Amadu Sule zuwa gobe Alhamis, 15 ga watan Janairu, 2026, domin yanke shawara kan buƙatar neman belinsa da lauyoyinsa suka shigar.
Idan har aka same shi da laifi, dokar hana safarar haramtattun kuɗaɗe ta shekarar 2022 ta tanadi tsauraran hukunci ga mutane da kamfanonin da suka aikata hakan.
ICPC ta cakumo aminin El-Rufai, Jimi Lawal
Tun da fari, mun ruwaito cewa, Hukumar yaki da cin hanci ta ICPC ta sake tuhumar wani tsohon ma’aikacin gwamnatin jihar Kaduna, Jimi Lawal kan zargin rashawa.
ICPC ta gabatar da tuhume-tuhume guda biyar a kan Jimi Lawal, tsohon hadimin tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa’i, bisa zargin rashawa da kuma halasta kudin haram.
Jimi Lawal ya na babban mai ba da shawara ga tsohon gwamna El Rufa'i, kuma ya zama daga cikin 'yan kwamitin bunkasa tattalin arzikin Kaduna daga 2019 zuwa 2023.
Asali: Legit.ng

