Tinubu Ya Yi Jimami da Matar Tsohon Gwamna Ta Mutu, Ya Roki Gwamnati
- Shugaba Bola Tinubu ya yi alhini kan mutuwar Uwargidan tsohon gwamna da ta bar duniya tana da shekaru 100 a yau Laraba
- Tinubu ya mika ta’aziyya ga gwamnatin Ogun da iyalan marigayiyar inda ya fadi gudunmawar da ta bayar
- Tinubu ya ce Lucia Onabanjo ta rayu tana hidima, tausayi da tasiri matuka musamman wajen tallafa wa mata da kula da walwalar yara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ogun - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya jajanta wa gwamnatin Jihar Ogun, al’ummarta bisa rasuwar matar tsohon gwamna bayan fama da jinya.
Tinubu ya ce marigayiyar Lucia Onabanjo wacce uwargida ce ga marigayi tsohon gwamnan farar hula na farko ta yi sa'ar tafiya.

Source: Twitter
Tinubu ya kadu kan rasuwar matar tsohon gwamna
Legit Hausa ta samu wannan rahoto ne daga mai ba shi shawara kan yada labarai, Bayo Onanuga wanda ya wallafa a shafin X.
Marigayiya Lucia Onabanjo, wadda ita ce matar Cif Victor Olabisi Onabanjo, ta rasu tana da shekaru 100 a duniya.
Shugaba Tinubu ya bayyana alhininsa ga iyalai, abokai da masoyan marigayiyar, yana cewa rasuwarta babban rashi ne ga Jihar Ogun da kasa baki daya.
Ya ce Lucia Onabanjo ta rayu rayuwar hidima, tausayi da nutsuwa, inda ta taba rayuwar mutane da dama a cikin al’umma da ma waje.
Abin da ya fi ba Tinubu mamaki kan rashin
Shugaban kasar ya lura cewa yawan sakonnin jaje da yabon da ake yi mata bayan rasuwarta na nuna irin kyawawan dabi’u da tasirin da ta bari.
“Goyon bayan da Lucia Onabanjo ta bai wa mijinta a lokacin mulkinsa na gwamnan Jihar Ogun daga 1979 zuwa 1983 abin yabawa ne sosai."
- In ji Tinubu.
Ya kara da cewa sha’awarta wajen kula da walwalar yara da karfafa mata ta nuna tsantsar jajircewarta ga ci gaban al’umma.

Source: Facebook
Tinubu ya tuna da sadaukarwar marigayiya
Shugaba Tinubu ya ce tarihinta na sadaukarwa, karamci da taimakon masu rauni zai ci gaba da zama abin tunawa ga al’umma har sauran al'umma masu zuwa.

Kara karanta wannan
Rasuwar Sarki mai martaba ta taba Bola Tinubu, ya mika ta'aziyya ga masarautar Badagry
Ya kara da cewa:
“Ina da yakinin cewa halayenta na tausayi da karamcin da ta bari ba zai gushe ba."
Ya bukaci gwamnatin Jihar Ogun da iyalan Onabanjo su daukaka tarihinta ta hanyar ci gaba da ayyukan tallafa wa matalauta da marasa galihu.
Shugaban kasar ya kuma yi addu’ar Allah ya jikanta, ya gafarta mata, tare da bai wa iyalanta hakurin jure wannan babban rashi.
Tinubu ya jajanta kan rasuwar Sarki a Lagos
Mun ba ku labarin cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi ta'aziyyar rasuwar Sarkin Badagry da ke jihar Lagos, Wheno Aholu Menu-Toyi I, wanda aka fi sani da Oba Babatunde Akran.
Shugaban kasar ya tuna da wasu halaye da nagartar marigayi Sarkin, inda ya bukaci mutane su yi koyi da dabi'unsa masu kyau domin inganta rayuwar mutane.
Shugaba Tinubu ya yi addu'ar Allah ya ji kan mamacin, sannan ya mika ta'aziyya ga iyalan marigayin bisa wannan rashi da suka yi.
Asali: Legit.ng
