Daliban UNIMAID na Taimakawa Boko Haram? Jami'ar Ta Fadi Gaskiyar Lamari

Daliban UNIMAID na Taimakawa Boko Haram? Jami'ar Ta Fadi Gaskiyar Lamari

  • Jami’ar Maiduguri (UNIMAID) ta yi magana game da zargin dlaibai da alaka da Boko Haram a yau Talata 13 ga watan Janairun 2026
  • UNIMAID ta musanta bidiyon da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke zargin kama dalibai bisa alaka da Boko Haram
  • Bidiyon ya yi ikirarin cewa jami’an tsaro sun kama wasu daliban UNIMAID bisa zargin taimaka wa Boko Haram a matsayin ’yan leƙen asiri

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Maiduguri, Borno - Hukumar Jami’ar Maiduguri, UNIMAID ta yi karin haske kan zargin wasu dalibai da alaka da Boko Haram.

Jami'ar ta karyata zargin da ke cewa an kama wasu dalibanta bisa zargin alaka da kungiyar yan ta'addan Boko Haram.

UNIMAID ta karyata alakar dalibanta da Boko Haram
Babbar kofar Jami'ar Maiduguri a jihar Borno. Hoto: @uni_maid.
Source: Twitter

Sai dai a wata sanarwa da TheCable ta samu, magatakardan jami’ar, Ahmad Lawan, ya karyata ikirarin da ake yadawa a kafafen sadarwa.

Kara karanta wannan

Duk da harin Amurka, 'yan Sokoto sun fadi yadda barazanar Bello Turji ke tarwatsa su

Yadda aka alakanta daliban UNIMAID da Boko Haram

Wani bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta ya nuna wani mai amfani da kafar sadarwa yana zargin jami’an tsaro sun kama daliban jami’ar.

Mutumin ya wallafa a kafofin sadarwa, inda ya yi ikirarin cewa daliban suna taimaka wa ’yan Boko Haram a matsayin masu basu bayanai.

Ya kara da cewa daliban na daga cikin mutanen da ke cin gajiyar ayyukan kungiyar ta’addanci, lamarin da ya janyo fargaba a tsakanin jama’a.

An ƙaryata alakar daliban UNIMAID da Boko Haram
Taswirar jihar Borno da ke fama da matsalar Boko Haram. Hoto: Legit.
Source: Original

Boko Haram: UNIMAID ta magantu kan zargin dalibai

Lawan ya bayyana zargin a matsayin karya, maras tushe kuma na tada hankali wanda ka iya jawo rikici a tsakanin dalibai da kuma sauran al'umma da ke cikin gari.

Ya ce babu wani dalibi a UNIMAID da aka taba zargi ko kama shi bisa alaka da Boko Haram ko wata kungiyar makamanciya.

Ya jaddada cewa jami’ar ba ta amincewa da tsattsauran ra’ayi, yana mai cewa dalibai da ma’aikata masu biyayya ga dokoki ne.

Kara karanta wannan

Yaran Turji sun yi ta'asa a Sokoto bayan sakon dan ta'addan ya rikita jama'a

A cewarsa, jami’ar na dauke da mutane daga kabilu da addinai daban-daban, wadanda hankalinsu ya karkata ne kawai kan karatu, cewar Tribune.

Shawarar da jami'ar ta ba al'umma, dalibai

Sanarwar ta ce jami’ar ta lura da bidiyon da ke dauke da bayanai masu rudani da ke iya bata sunan cibiyar ilimi wanda ka iya jawo rigima.

UNIMAID ta bukaci jama’a da su yi watsi da irin wadannan labaran karya da ka iya haddasa fargaba da bata mutuncin jami’ar.

Jami’ar ta ce tana ci gaba da jajircewa wajen inganta ilimi, tarbiyya, zaman lafiya, tsaro da kuma hadin kan kasa baki daya.

Dalibi ya yi magana da Legit Hausa

Wani dalibi a tsangayar kimiyyar siyasa, Al-Mukhtar Usman Muhammad ya bayyana fargaba game da rade-radin da ake yadawa.

Mukhtar ya ce hankulansu sun tashi matuka game da lamarin duba da yadda ta'addanci ke kara yawa.

Ya ce:

"Karyata rahoton da Jami'ar ta yi, ya kwantar mana da hankali saboda akwai tashin hankali a ce kana tare da yan ta'adda kamar Boko Haram."

Kara karanta wannan

AFCON 2025: Abin da muka sani game da Laryea, alkalin wasan Najeriya da Morocco

UMIMAID ta karrama Shugaba Bola Tinubu

An ji cewa asibitin koyarwa na jam'iar Maiduguri ya bude cibiyar fasahar zamani na ICT ta kiwon lafiya kuma sai aka karrama Bola Tinubu.

An sanyawa cibiyar da aka bude ta musamman sunan shugaban kasa wacce ta koma 'Bola Ahmed Tinubu Medical ICT Institute'.

Hakan na zuwa ne yayin da aka yi ta magana kan sauya sunan jami'ar zuwa sunan marigayi tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.