Shehu Sani Ya Magantu bayan Amurka Ta Kawo Tallafin Kayan Aiki ga Sojojin Najeriya
- Najeriya ta samu tallafin kayan aiki na sojoji a yakin da take yi da 'yan ta'adda da 'yan bindiga daga rundunar tsaron Amurka
- Kayan aikin sun iso ne yayin da Najeriya ke kara karfafa hadin gwiwar da take yi da Amurka domin tunkarar matsalar ta'addanci
- Tsoho sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya yabawa Amurka tare da mika kokon bararsa ga sauran kasashen duniya masu ikirirarin suna kaunar Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Tsohon sanatan da ya wakilci Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya yaba kan isowar muhimman kayan aikin sojoji da Amurka ta kawo Najeriya.
Tsohon 'dan gwagwarmayar, Shehu Sani ya bayyana matakin a matsayin wanda ya zo a kan lokaci kuma abin a yaba.

Source: Twitter
Shehu Sani ya bayyana hakan ne a wani rubutu da ya yi a shafinsa na X a ranar Talata, 13 ga watan Janairun 2026.
Kasar Amurka ta kawo tallafi ga Najeriya
Rundunar sojojin Amurka a Afrika (AFRICOM) ta sanar da kawo kayan aikin sojoji zuwa Najeriya domin tallafa wa ayyukan tsaro da kasar ke ci gaba da yi a yakin da ake yi da ta’addanci da ’yan fashi da makami.
Rundunar AFRICOM ta tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X, inda ta ce an mika kayan ga hukumomin Najeriya a birnin Abuja.
A cewar AFRICOM, isar kayan na nuna ci gaba da kudirin Amurka na karfafa haɗin gwiwar tsaro da take yi da Najeriya.
Me Sanata Shehu Sani ya ce kan tallafin Amurka?
Tsohon sanatan ya bayyana cewa wannan tallafi zai karfafa kokarin Najeriya wajen dakile matsalar rashin tsaro, musamman a yankin Arewa maso Yamma.
“Na karanta rahotannin da ke nuna cewa Amurka ta kawo muhimman kayan aikin sojoji ga Najeriya. Wannan ci gaba ne mai kyau kuma abin a yaba."
- Sanata Shehu Sani

Source: Twitter
Shehu Sani ya yi kira ga sauran kasashe
Tsohon ɗan majalisar ya kuma yi kira ga sauran kasashen da ke ikirarin suna kaunar Najeriya da su yi koyi da Amurka ta hanyar bayar da sahihin tallafi a yakin da ake yi da ta’addanci da ’yan bindiga masu dauke da makamai.
“Wasu kasashen da ke cewa suna sonmu ko suna kaunarmu su yi koyi da wannan mataki. Duk wani abu da za a iya yi domin kawar da Bello Turji, Adamu Aliero, Baleri da sauran ’yan ta’adda masu aikata laifuffuka a dazukan Zamfara abin maraba ne."
- Sanata Shehu Sani
Shehu Sani ya yi wa Trump martani
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Sanata Shehu Sani, ya yi wa shugaban kasar Amurka martani kan barazanar kawo hari Najeriya.
Sanata Shehu Sani wanda ba bakon tofa albarkacin baki ba ne kan abubuwan da ke gudana a kasa, ya nuna kin amincewarsa kan shigowar kowace irin rundunar ketare a Najeriya.
Hakazalika, kwamred ya ce Najeriya ba za ta taɓa zama “wulakantacciyar kasa ba" bayan shugaban na Amurka ya kira da wannan suna.
Asali: Legit.ng

