Sakon da Bello Turji Ya Aiko Ya Hargitsa Mutane, An Fara Guduwa a Jihar Sakkwato

Sakon da Bello Turji Ya Aiko Ya Hargitsa Mutane, An Fara Guduwa a Jihar Sakkwato

  • Kasurgumin dan bindigar nan, Bello Turji ya turo sako mai daga hankali ga mazauna Tidibale a karamar hukumar Isa ta jihar Sakkwato
  • Rahotanni sun nuna cewa mutanen kauyen, wadanda galibinsu manoma ne sun fara guduwa daga gidajensu domin neman tsira
  • Ana zargin Turji ya dauki wannan mataki ne domin nuna cewa har yanzu yana da karfin iko bayan tsawon lokaci da daina jin duriyarsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Sokoto, Nigeria - Fargaba da zaman dar-dar sun sake dawowa a kauyen Tidibale, wani ƙaramin ƙauyen manoma da ke gabashin Karamar Hukumar Isa a Jihar Sakkwato.

Mutanen garin sun fara fargabar abin da zai iya zuwa ya dawo bayan fitaccen jagoran ’yan bindiga, Bello Turji ya fitar da wata barazana mai tsanani ga al’ummar yankin.

Jihar Sakkwato.
Taswirar jihar Sakkwato da ke Arewa maso Yammacin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Barazanar Bello Turji ta hargitsa mutane

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun mamayi jami'an tsaro, sun kashe tsohon 'dan takarar majalisa da mutum 4

A rahoton da Vanguard ta wallafa yau Talata, ta ce mazauna yankin sun ce barazanar, wadda ta zo bayan dogon lokaci da daina jin duriyar Turji, ta jefa jama’a cikin tsoro mai tsanani.

An ce a karshen makon nan, iyalai da dama sun fara barin gidajensu da gonakinsu, suna tafiya zuwa wuraren da suka fi tsaro domin tsira da rayukansu.

Wasu mazauna kauyen sun gudu zuwa garin Isa, Gidan Hamisu, yayin da wasu suka tsallaka zuwa Shinkafi a Jihar Zamfara domin neman mafaka.

Rahotanni daga yankin na nuni da cewa Bello Turji na ƙoƙarin sake nuna ƙarfinsa da tasirinsa bayan dauke kafar da ya yi a kwanakin baya.

Wani sako Bello Turji ya turo a Sakkwato?

An ce kasurgumin dan bindigar ya turo sakon barazana cewa duk al’ummomin da suka ki masa biyayya ko jituwa da shi za su fuskanci mummunan sakamako.

Mata, yara da tsofaffi na daga cikin waɗanda suka bar matsugunansu, yayin da manoma da ya kamata su fara shirin noman badi suka koma kwana a gidajen ’yan uwa ko tantuna na wucin-gadi, ba tare da tabbacin lokacin da za su koma gida ba.

Kara karanta wannan

Tinubu ya kashe Naira biliyan 40 a zamanantar da gadar Legas da CCTV

Wani mutumi da ya baro gidansa, ya ce:

“Mun bar komai namu a gida, rayuwa ta fi amfanin gona muhimmanci.”

Turji ya kulla yarjejeniya da wasu garuruwa

A gefe guda kuma, rahotanni sun nuna cewa wasu mazauna garuruwa daban-daban a Karamar Hukumar Shinkafi ta Jihar Zamfara, kamar Shinkafi, Katuru, Jangeru da Kanwa, sun cimma wata yarjejeniya da Bello Turji.

A cewar mazauna yankin, sun amince ba za su ƙalubalanci ayyukansa ko kai rahoto a kansa ba, wani mataki da suka ce sun ɗauka ne domin tsira, ba don goyon baya ba.

Gwamna Ahmad Aliyu na Sakkwato.
Gwamnan jihar Sakkwato, Ahmed Aliyu a gidan gwamnati Hoto: Ahmed Aliyu
Source: Facebook

Masana sun yi gargaɗin cewa duk da cewa irin waɗannan yarjejeniyoyi na iya kawo sauƙi na ɗan lokaci ga wasu ƙauyuka, suna iya ƙara yada rashin tsaro zuwa wasu yankuna.

Da gaske Bello Turji ya gudu ya buya?

Ku na da labarin wani masanin tsaro a Najeriya, Yahuza Getso ya bayyana cewa babu inda Bello Turji ya gudu ya 'buya kamar yadda ake yada jita-jita.

Kara karanta wannan

Halin da aka shiga bayan farmakar Hausawa a jihar Edo

Masanin tsaron ya bayyana haka ne kwanaki kadan bayan Turji ya fito da bayanai, yana musanta cewa akwai wata alaka tsakaninsa da karamin Ministan Tsaro, Bello Matawalle.

Dr. Yahuza Getso ya bayyana cewa sau da yawa an bai wa gwamnati bayanai kan inda Turji yake, amma duk da haka ba a dauki matakin kama shi ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262