Gwamna Ya Fito Ya Fadi Gaskiya kan Kudaden da Ke Shigowa Hannun Gwamnoni
- Gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori, ya yi tsokaci kan kudaden da ake ba gwamnoni daga asusun tarayya
- Sheriff Oborevwori ya bayyana cewa abin da gwamnoni ke karba duk karshen wata ya karu sosai fiye da wanda suke samu a baya
- Gwamnan ya bayyana cewa masu cewa babu kudi a kasar nan, ba gaskiya suke gayawa 'yan Najeriya ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Delta - Gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori, ya ce jihohi a halin yanzu suna karɓar kuɗaɗe fiye da baya daga asusun rarraba kuɗi na tarayya.
Gwamna Oborevwori wanda ya koma jam'iyyar APC mai mulki ya jaddada cewa ya kamata wasu mutane su daina cewa babu kuɗi a ƙasar nan.

Source: Facebook
Jaridar TheCable ta ce Oborevwori ya faɗi hakan ne a ranar Litinin, 12 ga watan Janairun 2026 yayin bikin fara aikin gina gadar sama ta Otovwodo a kan kuɗi Naira biliyan 39.3 a karamar hukumar Ughelli ta Arewa.
Gwamnan Delta ya ce jihohi na samun kudade
Gwamnan ya ce babu dalilin ɓoye gaskiya ga ’yan Najeriya, yana mai cewa gwamnatocin jihohi yanzu suna da isassun kuɗaɗe.
“Ina so na faɗa muku wani abu da wasu mutane ba su sani ba. Kuɗi sun karu wajen jihohi. Ni ba gwamna ba ne da zan ɓoye hakan. Don me zan ɓoye hakan?”
“Kuɗin suna fitowa ne daga wani wuri. Wasu mutane suna son su ɓoye gaskiya su ce babu kuɗi; amma akwai kuɗi. Ku yi amfani da kuɗin kamar yadda muke amfani da su a jiharmu. Ku yi amfani da su a jiharku domin jama’a su yi farin ciki.”
- Gwamna Sheriff Oborevwori
Gwamna Oborevwori ya fadi amfanin gadar da zai gina
Oborevwori ya bayyana a shafinsa na Facebook cewa aikin gadar sama ta Otovwodo wata muhimmiyar nasara ce a kokarin gwamnatinsa na inganta ababen more rayuwa a faɗin jihar.
“A yau mun sake cimma wani muhimmin mataki a wannan gwamnati yayin da na jagoranci bikin fara aikin gina gadar sama a mahadar Otovwodo da ke Ughelli ta Arewa."
- Sheriff Oborevwori
Ya ce mahadar Otovwodo muhimmiyar hanya ce da ke haɗa Warri, Asaba da Patani a kan titin East–West, wanda hakan ya sa ta zama ɗaya daga cikin hanyoyin da suka fi cunkoso a yankin.

Source: Facebook
Ya kara da cewa idan aka kammala aikin, wanda kamfanin Julius Berger ke aiwatarwa kan kuɗin Naira biliyan 39.34, zai rage cunkoson ababen hawa tare da ƙarfafa harkokin kasuwanci da ciniki, kuma ana sa ran za a kammala shi cikin watanni 12.
“A yayin bikin, na jaddada cewa wannan gwamnati tana sake fayyace yarjejeniyar zamantakewa da jama’arta ta hanyar tausayi, jajircewa da kuma nuna al’adar gaskiya wajen aiwatar da ayyukan more rayuwa."
- Gwamna Sheriff Oborevwori
Gwamnan na Delta ya kuma roki direbobi da masu amfani da hanyar da su yi hakuri, yana mai kira gare su da su bi umarnin jami’an zirga-zirga a lokacin aikin domin kauce wa cunkoso a kan hanya.
Su yi abin da ya dace

Kara karanta wannan
A karon farko, El Rufai ya yabi gwamnati bayan zazzafar adawa da kamun ludayin Tinubu
Wani mazaunin Katsina, ibrahim Kabir, ya shaidawa Legit Hausa cewa ya kamata gwamnoni su ji tsoron Allah, su yi abin da ya dace.
"Tabbas gwamnoni sun samu kari sosai bangaren kudaden da suka samu, amma tambayar shi ne shin talaka ya gani a kasa?"
"Ya kamata su ji tsoron Allah su yi wa talakawa abin da ya dace. Mutane na bukatar su gani a kasa cewa kudade sun karu a hannun gwamnoni."
- Ibrahim Kabir
Gwamna jihar Delta ya yi ta'aziyya
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori, ya nuna alhininsa kan rasuwar tsohon sanata, Peter Nwaoboshi.
Gwamna Oborevwori ya ce marigayin wanda ya wakilci Delta ta Arewa a majalisar dattawa, jajirtaccen ɗan Delta ne kuma gagarumin mai kare muradun Anioma.
A cewarsa, marigayin ya sadaukar da rayuwarsa wajen yi wa al’umma, jam’iyya da ƙasa hidima, ya bar tarihi na jarumta da biyayya.
Asali: Legit.ng

