Bankuna 20 Sun Cika Sabon Sharadin CBN, za a Rufe Wasu ko Su Yi Hadaka
- Babban bankin Najeriya ya kafa sabon sharadin mallakar jari da ke tilasta wa bankuna ƙara ƙudi domin jure girgizar tattalin arziki da tallafa wa bunƙasa ƙasa
- Rahotanni sun nuna cewa zuwa yanzu bankuna 20 sun riga sun kammala cika sharudan, yayin da wasu ke ci gaba da nema wa kansu mafita kan batun
- Ana hasashen cewa bankunan da suka gaza cika sharudan da bankin CBN ta gindaya za su kulle ko kuma su yi hadakar jari da wasu bankuna su taimaki juna
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Akalla bankuna 20 a Najeriya sun riga sun cika sabon sharadin jarin da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya kafa, a wani shiri da ke nufin ƙarfafa tsarin banki da tabbatar da cewa cibiyoyin kuɗi na da ƙarfin fuskantar kalubalen tattalin arziki.
Shirin sake tara jari ya kafa sharadin mallakar Naira biliyan 500 ga bankunan kasuwanci masu lasisin ƙasa-da-ƙasa, Naira biliyan 200 ga na ƙasa, da Naira biliyan 50 ga bankuna na yankuna.

Source: Getty Images
Business Day ta rahoto cewa an ba bankuna wa’adin wata 24 da zai ƙare a ranar 31, Maris, 2026, lamarin da ya haifar da yawaitar fitar da hannayen jari, tattaunawar haɗaka, da sake tsara ma’aunin kuɗi .
Sabon tsarin CBN ga bankuna
Rahoton Business Insider Africa ya ce sabon tsarin CBN na da burin tabbatar da cewa bankuna sun samu isasshen jari domin kare kansu daga girgizar kasuwa tare da taka rawa mai ma’ana a bunƙasar tattalin arzikin Najeriya.
Wannan tsari ya yi kama da abin da aka aiwatar a 2004 a zamanin Charles Soludo, inda aka tilasta wa bankuna kara jari daga Naira biliyan 2 zuwa biliyan 25, lamarin da ya rage adadin bankuna daga 89 zuwa 25.
Bankunan da suka cika sharadi
Access Bank ya zama bankin farko da ya cika sharadin, ya tara jarin Naira biliyan 500 bayan ya tattaro sama da Naira biliyan 351 ta hanyar fitar da hannayen jari.
Zenith Bank ma ya kammala shiri, inda ya tara sama da Naira biliyan 350 ta haɗa kudin masu hannun jari, lamarin da ya kai jarinsa sama da ma’aunin da ake buƙata.
First HoldCo, GTCO da UBA suma sun sanar da cika sharudan, ta hanyar shirye-shiryen tara jari daban-daban da suka haɗa da zuba hannun jari da wasu dabaru na kasuwanci.
Wasu bankuna sun cika sharadin CBN
A matakin bankunan gida Najeriya, Citibank Nigeria, Ecobank, Globus Bank, Stanbic IBTC da PremiumTrust Bank sun riga sun haura ma’aunin Naira biliyan 200.
Providus Bank ya bi wata hanya ta daban, inda ta kammala shirin ta hanyar haɗaka da Unity Bank, wanda ya zama haɗaka ta farko da aka amince da ita a ƙarƙashin sabon shirin CBN.
Haka kuma, bankunan ‘yan kasuwa kamar FSDH Merchant Bank, Greenwich Merchant Bank, Nova Bank da Rand Merchant Bank sun cika nasu sharudan.

Source: Getty Images
Bankunan da ba su karbar kudin ruwa irin su Jaiz Bank, Lotus Bank da TAJBank ma sun ƙara jarinsu domin bin dokar CBN kafin ƙarshen wa’adin.
Hasashen CBN kan tattalin arzikin Najeriya
A wani labarin, mun kawo muku cewa bankin Najeriya na CBN ya fitar da hasashe kan yadda tattalin arzikin Najeriya zai kasance a shekarar 2026.
Rahoton da bankin ya fitar ya nuna cewa yanayin tattalin arzikin kasar ya nuna cewa farashin litar man fetur zai kasance tsakanin N950 zuwa kasa.
A bangaren sauka da hauhawar farashi kuma, bankin CBN ya bayyana cewa akwai alamun cewa 'yan Najeriya za su saye kaya da rahusa a 2026.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


