Kwana Ya Kare: Sarki Mai Martaba a Najeriya Ya Rasu bayan Kusan Shekaru 50 Yana Mulki
- An shiga jimami a jihar Legas bayan bullar labarin rasuwar Mai Martaba Sarkin Badagry, De Wheno Aholu Menu-Toyi I
- Fadar Sarkin ta tabbatar da rasuwar mai martaba wanda ya shafe kusan shekaru 50 a kan karagar mulki a jihar Legas
- Mazauna yankin masarautar Badagry sun shiga alhini tare da jimami, inda suka ce sun rasa uba mai ba au shawarwari na hikima
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Lagos, Nigeria - An kara rasa daya daga cikin manyan sarakun gargajiya da suka dade a kan karagar mulki a Najeriya.
Rahotanni sun tabbatar da cewa Sarkin Badagry da ke jihar Lagos, Mai Martaba De Wheno Aholu Menu-Toyi I, Akran na Badagry, ya rasu yana da shekaru 90.

Source: Facebook
Sarkin Badagary ya rasu a Legas
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa rasuwar basaraken ta jefa garin Badagry da al'ummar da ke rayuwa a yankin cikin yanayin jimami da alhini.

Kara karanta wannan
Rikicin Rivers: Matakin da Tinubu ya dauka bayan alaka ta sake tsami tsakanin Wike da Fubara
Rasuwar Sarkin ta kawo karshen tsawon shekarun da ya shafe yana jagorantar al'ummarsa a jihar Legas da ke Kudu maso Yammacin Najeriya.
Tsawon shekaru da dama, ya kasance mai kula da harkokin al’adun masarautar Badagry, kuma an ce mulkinsa ya kawo haɗin kai tsakanin mazauna yankin.
Bugu da kari, Marigayi Sarkin ya kasance ɗaya daga cikin manyan masu magana da yawun Majalisar Sarakuna da Manyan Masu Rike da Sarauta ta Jihar Lagos.
Lokacin da Sarkin Badagary ya shafe a mulki
An bayyana marigayin a matsayin Sarki mai ilimi, rikon al’adu, da daraja ta musamman, wanda tasirinsa ya wuce fadar masarautar Badagary kadai, har da Legas da Najeriya baki daya.
Jaridar Vanguard ta tattaro cewa Sarkin ya shafe kusan shekaru 50 yana sarauta a masarautar Badagry, kafin Allah ya karbi rayuwarsa a yau Litinin, 12 ga watan Janairu, 2026.
Mutuwar Sarkin ta kawo ƙarshen mulkin shekaru 48 da ya shafe a kan karagar mulki, wanda hakan ya sanya shi ɗaya daga cikin sarakunan gargajiya mafi daɗewa a Jihar Legas.
Al'ummar garin Badagary sun shiga jimami

Kara karanta wannan
Sarkin Musulmi ya nemi Tinubu ya ziyarci garin da aka yi wa jama'a yankan rago a Neja
A cewar fadar Sarkin, ƙwararrun likitoci ne suka tabbatar da mutuwar Akran, kuma tuni aka fara shirye-shiryen da al'adun jana'izarsa.
Mazauna Badagry, waɗanda a halin yanzu ke cikin alhinin rasuwar Sarkinsu mai daraja, sun bayyana mutuwarsa a matsayin babban abin bakin ciki da damuwa.

Source: Original
A cewarsu, ba wai Sarki kadai garin Badagry ya rasa ba, har ma da uba wanda hikimarsa, shawarar da yake bayarwa da rayuwarsa suka kawo kwanciyar hankali a yankin.
Tarihi ya nuna cewa an haife shi a shekarar 1936, inda ya fara aikin jarida kafin ya hau gadon sarautar kakanninsa a ranar 23 ga Afrilu, 1977.
Sarkin Kagarko ya rasu a jihar Kaduna
A wani rahoton, kun ji cewa Sarkin Kagarko a jihar Kaduna, Alhaji Sa’ad Abubakar, ya riga mu gidan gaskiya bayan fama da jinya.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa an riga da an yi sallar jana'izar marigayin a ranar Jama'a, 9 ga Janairun 2026, a masallacin Masarautar Kagarko bayan idar da sallar Juma'a.
Shugaban Karamar Hukumar Kagarko, Muhuyideen Abdullahi Umar, ya bayyana matuƙar baƙin ciki kan rasuwar Sarkin tare da mika sakon ta'aziyya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng